Skip to content
Part 29 of 73 in the Series Sakacin Waye? by Sumayyah Abdulkadir Takori

Grandma (Veronica) 

Ya kira Kaka a na i gobe alkawarin sa da Nasara zai cika. Ya san cewa he failed her woefully idan ta ji abinda ya yankewa rayuwar sa. And she will never forgive him. 

“Mawonmase, kana lafiya? Duk na shiga damuwa kwana biyu da ban ji ka ba.”

“Ina lafiya cikin alheri Kaka. Ina kuma yi miki shirin tahowa karbar suruka U.S nan ba da jimawa ba.”

Kaka ta yi shiru, kafin tace “Tina Gyang, zan taho kawowa United States?”

Shima yayi shiru cikin tsoro da fargaba. Kafin ya ce “a’ah kaka laifi zan miki gagarumi, na dade ina fada miki bazan auri ‘yar Birom ba. Don haka ki bar maganar Tina.  Wata kabilar daban na samo miki wadda  nake fatan ki cire banbancin addini da al’ada ki karbe ta da hannu bibbiyu. Kisa a ranki cewa itace matar da kika dade kina roka mini, ina tabbatar miki zaki so SIYAM Kaka…”

Kaka ta katseshi cikin karaji da cewa “over my dead body. A bayan rai na kadai zaka hada Jiki da dan wani addinin da ba Christianity ba.” Sai kuma ta fashe da kuka mai gigitarwa. Tan fadin “Mawonmase kai kadai nake da, na ci buri mai yawa a kan matar da zaka aura, ta taramin jikoki tunda ni ban haihu da yawa ba. Baban ka kadai na haifa. Shima ya tafi ya bar ni. Amma sakayyar da zaka yi min kenan? Butulcin da zaka yi wa Jesus kenan akan albarkar da yayi maka a cikin tsararrakin ka?” 

Kuka take masa sosai na fitar hankali tana yi tana fyatar hanci, gaba daya ta gigita shi ta rikita shi. A lokacin Kaka ta tuna mafarkin da tayi jiya-jiya ashe abinda zata ji yau dinnan kenan? Kenan ba sai ta sake komawa wajen Pastor David ba, don jin sakamakon mafarkin ta. 

Mawonmase ta gani yana karantawa yaran sa maza da mata Al’qur ‘ani a cikin barcin ta, littafin da Allah ya saukarwa Annabi Muhammad SAW, ya dauki Bible ya kekketa ya kona ya kuma zuba gawayin a shara.

Bayan tashin ta daga barci a firgice kuma a gigice ta tafi wajen Pastor din ta, ta gaya masa mafarkin da tayi yau a kan tilon jikan ta dake U.S, Mawonmase. Shi kuma ya ce ta bashi kwana biyu ta dawo zai yi duba akan mafarkin ta. 

A kuma yau kafin gobe tayi ta koma wajen Pastor David sai ga shi ya kira ta yana gaya mata wannan zance da bata taba jin mai munin sa ba. Kodayake ya kamata ace ta dade da sawa ranta wata rana irin wannan na zuwa, in tayi la’akari da Personality din sa na alaqa da musulmai fiye da kiristoci. Abin kamar a jinin sa yake. Amma ganin tun yana yaro bai yi tunanin musulunta ba tun a kan Hamzah Almustpaha ta saki jikin ta tayi tsammanin a girman sa ma ba abinda zai faru da addinin sa, haduwar jini ce kawai.

Hamzah ya rasa yadda zai yi da Kakar sa ta yi shiru daga ihun data ke kurma masa a waya sai kawai ya kashe wayar sa, kada ta illata masa dodon kunne. Hannaye bibbiyu ya aje ya zuba tagumi akai, kansa na sarawa. Ya dauki wayar ya sake rubuta ma Siyama sakon da ke nuni da halin damuwar da yake ciki. Ba don yana tsammanin samun amsa daga gare ta ba sai don hakan zai sa ya dan ji dadi. 

“Siyam, please stay with me till the very end. The battle has just began. Na fahimci ba abu ne mai sauki na daukowa kaina ba ta kowanne bangare. Na yi alkawarin jure komai da tsayawa akan ISLAM in dai zan tsira da ke! I so much love you Siyam, I LOVE YOU.”

                                                 -Hamzah.

Lokaci na farko dana karanta sakon na fahimci yana cikin matsala da iyayen sa. A dalilin hukuncin da yake so ya yanke. A take na tuno nawa Abban da tawa Ummatin, ranar da aka gaya musu mijin mafarki na tuba yake son yi ba’a haife shi cikin musulunci ba. 

Kowacce irin matsala kake ciki da iyayen ka Hamzah bata kai wadda ka janyo tsakani na da Abba na  da dan uwa na ba. Sai in maka fatan alkhairi. 

Soyayyar dana ke maka tana maka kwadayin shiriya koda bazan aure ka ba. Ina maka kwadayin haske da gardin dake cikin addinin musulunci. Ina maka kwadayin tsira daga azabar wutar Sa’irah da Jahannama.

Na fada a fili, amma ban maida masa martanin sakon sa ba.

Kwanaki uku da Hamzah ya debawa Nasara sun cika. Kuma a kwanaki ukun nan bai je wajen aikin sa ko sau daya ba. Ya kulle kan sa a gidan sa yana nemawa kansa mafita wadda yake ganin bazata zo tayi haunting dinsa daga baya ba. Damuwar sa daya Kaka ce da kuma iyayen Siyama ko zasu karbe shi su bashi ‘yar su idan yace ya amince ya musulunta?

Karfe goma na safe, a kofar gidan Nasara Alkali tayi masa. Ranar ta kasance Lahadi don haka daga Antin har maigidanta Adamu suna gida. A daren jiya ta kwana warwarewa Adamu komai. Adamu cikakken Elite sai cewa yayi.

“Idan har zai musulunta da zuciya daya kamar yadda yake niyya, kuma da gaske yake son Siyama, kuma Siyama na masa wannan son da kike bani labari, kuma shine mutumin da take duk wannan suffering din a kan sa, sannnan yayi alkawarin rike min ita da amana da soyayya, ni kuwa Adamu zan tsaya musu akan komai… har sai sun cimma burin wannan soyayya mai matukar ban mamaki daga Indallah. I’m ready to do this Jihad for bringing a new soul to ISLAM.”

Nasara bata zaci jin haka ba duk da ta san Adamu bature ne amma bata taba zaton zai amince ‘yar sa ta auri tubabbe haka farat daya ba. Tubabben ma mai budadde ido a Amurka irin Hamzah Almustapha wanda take ganin ta kowanne bangare yafi karfin tarbiyyar Siyama.

Yayi parking motar sa ‘Rolls Royce’ a kofar gidan su Siyama, a jikin kofar gidan akwai dan karfe mai ruwan gold makale da sunan maigidan “Adam Dalhatu Gembu”. Tun daga nesa ya hango Ahyan yana wasan bal a kofar gidan su. Koda yayi parking ya fito sanye cikin yadin Filtex mai ruwan madara garai-garai da shi da hular da ta dace da tsadadden yadin na jikin sa. Kamshin Sauvage na tashi a hankali daga jikin sa. 

Yafito Ahyan yayi, wanda ya dakata daga wasan yana masa kallon bakunta. Ahyan ya ki zuwa ya noke kafada. Daga ciki ya jiyo Nasara na kwala masa kira sai ya saki bal din sa da gudu yayi cikin gida yana gaya mata “Mummy that tall black Uncle is here”. Da sauri Nasara ta daga labule, nan ta hango Hamzah, tsaye jikin motar sa yana duba agogon Rolex dake daure a damtsen hannun sa.

Ta juya tana gayawa Adamu ya iso, Young Abba da yau har babbar riga ya saka don karbar suruki da kansa ya fita ya shigo da Hamzah, yana fadin “Yau VOA bakidaya a gida na! What a blissful Sunday”. Hamzah dai murmushi yake yi, murmushin sa mai kyau da aji cikin jin kunya na nuna alamun surukuta. Shi da Young Abba zasu yi sa’anni don ba yaro bane karami, da ace yayi aure da wuri da yanzu yana da yara biyu ko uku.  Young Abba ya bashi wajen zama kafin Nasara ta baibaye shi da abin sha da na taba ka lashe. Ahyan kuma ya tafi da gudu dakin mu yana gayamin Daddy yayi bako baki. 

Bakon da ko kusa ban taba tunanin Hamzah Mawonmase bane.

Bayan gaisuwar girmama juna data biyo baya da tambayar yanayin ayyukan junan su. Young Abba ya kasa boye jin dadin sa na ganin Hamzah Almustapha yau a gidan sa. Ya rasa ina yaka-saka-ina yaka-aje da shi. Ya gaya masa cewa yana jin dadin dukkan shirye-shiryen sa, kuma tun daga BBC yake bibiyar sa har kawo yau.  

Hamzah yayi godiya mai tarin yawa ya kuma kara samun kwarin gwuiwa daga karbar da Young Abba ya yi masa wadda bai zace ta ba. Young Abba yana ta jan shi da hira, amma ya kasa sakewa. Daga bisani sai ya zamo daga cikin kujerar da yake zaune ya durkusa a gaban Young Abba kan sa a sunkuye. 

Da dukkan respect a murya da fuskar sa har ma da zuciyar sa ya ce “na zo in karbi MUSLUNCI a hannun ka Abban mu, idan har shikadai zai bani damar auren SIYAM!”

A take Young Abba ya ci gyaran sa da cewa “ba’a musulunta don wani kebabben dalili, ana musuluta don Allah ne kawai. Don haka ka koma ka yi nazari idan musuluntar ka don Allah ce, to ka dawo in kai ka wajen Shaihunnan da zasu musuluntar da kai a makarantar su Siyama dake New York.”

A take Hamzah ya ce “na gyara magana ta Abban mu, zan Musulunta don Allah, da kuma son da nake yi wa Musulmi da addinin Musulunci tun kafin ma na san Siyama.”

Young Abba ya mika masa hannu sannan ya mikar da shi daga durkuson da yayi a gaban sa, ya ja shi jikin sa ya rungume shi yana cewa.

“Welcome to the happiness of life, ISLAM. 

Amma Hamzah wani hanzari ba gudu ba. Addinin musulunci addini ne na ibada, ita kuma ibada wahala gare ta sai ga muminai kadai. Zaka iya jure ibadodin dake cikin musulunci da ikhlasi babu tasgaro?” Anan ma Hamzah ya amsa “Abban mu duk abinda ka koyar da ni zan iya, but it has to be gradual, i will endure and practice everything to the best of my ability. (Duk abinda ka koyar da ni zan iya, amma a hankali, zan jure komai kuma zan gwada aikata komai da dukkan iyawa ta).”

Young Abba yace “bazaka koma addinin ka ba har abada, ko da ka rasa Siyama, hukuncin wanda yayi riddah a addinin musulunci babba ne”. Duk wasu sharuddan da Young Abba ke kwararowa Hamzah ya dukar da kai yace ya ji ya gani, zai jure saboda Allah”.

Nasara dake tsaye a bakin kofa tana kallon su, sai taji hawayen farin ciki da na tausayi na zubo mata duk a lokaci guda”.

A take Young Abba ya ce ya tashi su tafi New York ta jirgin kasa wajen shugaban makarantar su Siyama wato DAAR AL-ULOOM AL-MADANIA mai suna Shaykh Isma’il Maimon. Domin ya karbi Shahada a hannun sa.

Welcome To Islam, Hamzah Mawonmase

Shaikh Isma’il Memoon ya yi musu kyakkyawar tarba, a babban ofishin sa dake cikin makarantar Daar Al Uloom, a garin Buffalo, New York.

Ba yau ya fara musuluntar da mutane ba don haka da ya gama jin bayanin da ke bakin Young Abba na cewa ya kawo abokin sa zai Musulunta Shaykh yayi farin cikin karuwar da muslunci zai samu, ya kuma zayyano ma Hamzah shika-shikan musulunci da shika-shikan imani wadanda Young Abba ya sanar da shi wasu a ciki tun kafin ya kawo shi, duk Hamzah ya amsa zai iya. Kuma zai kwatanta. Sai ya umarci Young Abba da su shiga bandakin ofishin sa tare ya nuna masa wankan shiga musulunci.

Kafin ya yi wankan tsarki sai da Young Abba yasa shi yin wankan sabulu mai kamshi sosai, sannan ya tsaya ya nuna masa komai yayi akan idon sa. Amma dai ya dan juya baya lokacin da Hamzah yake tubewar, yayi wankan sa (as instructed) cikin tsanaki, yana jin wani irin nutsuwa da satisfaction na hasken musulunci na fara shigar sa. Sai da Shaykh ya tara daliban sa bakidaya sannan ya lanqayawa Hmzah Kalimatul -Shahadah. 

Hamzah ya maimaita tiryan – tiryan (Ashhadu An La’ilaha illallah, wahdahu laa sharika lah, wa Ashhadu anna Muhammadun Abdahu wa rasuluhu. Na shaida babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, shikadai ne bai da abokin tarayya, na shaida Annabi Muhammad SAW bawan Sa ne kuma Manzon Sa ne). Musulman dake wajen duka suka yi kabbara sannan suka mike suka shiga rungumar sa daya bayan daya suna sumbatar sa.

Young Abba shine na karshe, da yazo sai ya bashi ‘warm hug’ yana bubbuga bayan sa. Kawai sai Hamzah yaji kukan farin ciki ya rikice masa.

Wani a cikin daliban Shaykh, ya mike ya cire hular tashi ka faya nacin sa ya saka masa, wani ya bude fadin jallabiyyar sa yace “Yaa ayyuhal Muslimeen, ku nunawa dan uwa kara da karamci irin na muslunci.”

Ai kuwa kowa abinda ke aljiuhun sa ya rika zazzagewa a cikin rigar mutumin, manyan Dalolin Amurka, ga daliban ‘Daar Uloom’ masu yawan gaske don haka ba kananan kudi aka tarawa Hamzah ba.

Don haka hawaye sun ki tsayawa a idanun Hamzah wadanda bana komai bane na zallar farin ciki ne da yabawa da karamcin da aka yi masa. Da ya san haka hasken musulunci yake, tuntuni mai zai zaunar da shi a cikin bata?

Sai da suka kwana uku tare da Shaykh Ismail Memon yana koyar da Hamzah abubuwan da suka hau kansa a yanzu; sallah, tsarki, ibadah, zakkah, sadaqa da imani da Allah da Manzon sa. Sannan koyarwar Shaykh gradually yadda starter zai yi saurin dauka. Ya soma koyar da shi kananan surorin Alqur’ani da zai rika karantawa cikin sallah. A cikin kwana biyar Hamzah ya iya rabin Hizfi daya wato daga Nasi zuwa sama (kanan surori).

Sun baro New York a washegari zuwa Washington. Young Abba ya bashi shawarar cewa ya fidda komai na gidan sa ya saka sabo, sabida ya tsarkake muhallin sa. Ya san baza’a rasa GIYA a gidan ba. Sai yace ai gidan ma kan sa canzawa zai yi. Ba zai iya kara zama a cikin sa ba.

Young Abba ya sake maimaita masa “idan kana shan “Barasa” daga yau ku yi sallama, haramun ne shan ta a cikin addinin musulunci domin tana bugar da bawa ya shagalta da sallah da sauran ibadodin da suka hau kan sa.”

Hamzah yayi alkawarin barin komai da addini ya haramta, ya kuma roki Young Abba a bashi dama ya cigaba da neman auren Siyama.

Young Abba yace “nan da watanni uku dama zan dauki annual leave zamu je hutu gida Mambilla, sai mu tafi tare in gabatar da kai ga mahaifiyar mu da Abban ita Siyama wanda ya haife ta.”

Fadar irin farin cikin da ya samu kan sa a ranar, wani abu ne da biro ba zai iya rubutawa ba. Tun a ranar ya saka gidan sa a kasuwa. Ji yake hatta sittirun sa ba zai iya maimaita su ba, sakamakon haka, ya hada su duka ya saka a motar dake diban kayan charity. Kudin da aka hada masa a ‘Daar Al Uloom’ dasu yayi amfani ya sake sayen sittiru kala -kala ya kuma dinka shaddoji (his favourite attire). Satin bai fita ba hatta motocin sa ‘GMC Terrain’ da ‘Rolls Royce’ sai da ya sayar dasu ya hada ya sayi wata sabuwar mota guda daya ‘Kia EV6’, gidan sa aka saya da daraja ya koma wani American – Condo sabo dal. This is really a new Hamzah… sunan sa ne kawai bai sake ba. 

Ko da Shaykh Isma’il ya tambaye shi sunan da yake so cewa ya yi a bar masa HAMZAH tunda suna ne mai asali da tushe abun alfahari na Sayyidina Hamzah (A.S) Baffan Manzon Allah SAW.

Duk wadannan abubuwan da ke faruwa Young Abba na labarta mana. Amma bamu kara haduwa ba ni da Hamzan, he’s very busy da canje-canjen da yake yi ni kuma na maida hankali ga Internship dina.

In na ce da ku ina cikin farin ciki a wannan lokacin kema kin san yayi kadan ya bayyana zahirin halin dana ke ciki. Hamzah dai ko a waya bai kira ni ba amma sun dinke sosai shi da Young Abba sun zama wasu irin aminai. Young Abba na kara dora shi a kan hanyar duk abinda ya shige masa duhu da ya shafi tsarki da sallah, ya sayo masa kasusuwan wa’azi dana koyon karatun Al’qur ani iri daban daban.

Nutsuwar dana ke ciki a halin yanzu bana jin na taba tsintar kaina a kwatankwacin ta a kafatanin rayuwa ta. Ko yau na fadi na mutu ba tare da na auri Hamzah Mawonmase ba, burina da mafarkai na sun cika. 

Na tseratar da abinda zuciyata ke so da kauna daga azabar Allah saura neman cikawa da imani.

Yau da dare ya kira Young Abba “Abban mu (sunan da yake kiran Young Abba da shi) zani gida Jos in fara hada lefe. Muhyidden ya gaya min Fulani da Hausawa lefe ake fara hada musu”. 

Young Abba ya ce “to ka fara yakin neman soyayya kafin lefe first, don ni har yau ban ji ta bakin Siyama a kan ka ba, ina jin komai ne daga Antin ta, kuma alkawari ne bazan yi wa ‘ya ta auren dole ba.”

Dariya Hamzah yayi yace “Abban mu ni da ake so tun ba’a ganni ba, in ka yi min uzuri a gidan aure na zan yi yakin neman soyayyah ta ba a gidan ka ba. A lokacin da nake da license, amma yanzu bani da ‘yancin komai a kan Siyam. 

Zan je dai zance sau uku, in nuna mata kafa da hannaye na ta tabbatar bani da kuturta, haka Muhyiddeen yace min ana neman aure a muslunci.

Abban mu bana son kebewa da Siyam yanzu, alhalin babu aure tsakanin mu, Siyam ko hannun ta ka yi kuskuren kamawa (mistakenly) cewa zata yi “addini na ya hana.” Ni kuma I’m very touchy (mai yawan tabawa ne). So I must seek for my freedom first, saboda kebewar mu wai da sunan neman soyayya bazata zame mana alkhairi ba.”

Young Abba ya yarda da shi duk da ya ji kunya, sai ya hau fadan fanshe kunyar da Hamzah ya bashi, yace “kai wai ni abokin ka ne koko surukin ka Hamzah? Ni kake gayawa kana rike hannun ‘ya ta mistakenly? Ni kake gayawa you are touchy don baka data ido?” 

“Na tuba Abban mu, na bi Allah na bi ka tuntuben harshe ne.” Haka suka yi sallama suna ta barkwanci, da cewa yau, da gobe da jibi sune kawai Hamzah zai zo don gabatar da kan sa ga Siyama a matsayin mijin da ke neman auren ta.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Sakacin Waye? 28Sakacin Waye? 30 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×