Ita kuma Jaru sai wata jarabta ta same ta; nan duniya babu namjin da yake burge ta irin Mamman sabida gayun sa, bokon sa da tsaftar sa, ya fita daban da mutanen garin Mambila domin a lokacin yana aikin koyarwa a jami’ar Jos matsayin Lecturer, a lokaci guda kuma yana hada digirin sa na ukku a can jami’ar Jos din.
Lokaci - lokaci ya ke zuwa Gembu kuma in ya zo din baya jimawa bai fi yayi sati ko kwana uku ba ya koma, kasancewar dukkansu a gidan gadon su suke zaune har zuwa lokacin illa kowa da sassan. . .
Jinjina agareki babbar marubuciyarmu abar alfaharinmu
Allah ya saka da Alkhairi