Skip to content
Part 3 of 73 in the Series Sakacin Waye? by Sumayyah Abdulkadir Takori

Ita kuma Jaru sai wata jarabta ta same ta; nan duniya babu namjin da yake burge ta irin Mamman sabida gayun sa, bokon sa da tsaftar sa, ya fita daban da mutanen garin Mambila domin a lokacin yana aikin koyarwa a jami’ar Jos matsayin Lecturer, a lokaci guda kuma yana hada digirin sa na ukku a can jami’ar Jos din.

Lokaci – lokaci ya ke zuwa Gembu kuma in ya zo din baya jimawa bai fi yayi sati ko kwana uku ba ya koma, kasancewar dukkansu a gidan gadon su suke zaune har zuwa lokacin illa kowa da sassan sa, sassan Ummati da jikokin ta daban wanda yake daga can karshen gidan, nasu ita da Gidado daban a tsakiya sai na Mamman din a farkon shiga gidan wanda kullum yake a rufe sai idan ya zo garin Omar yake budewa ya share masa ya shigar da kayan sa.

A babban zauren gidan kuma dakin Baffan mu Adamu ne wanda a wannan shekarar Abba (Mamman) sunan da na mayar masa kenan tunda na soma baki, shi kuma Baffa Gidado in ce masa Malam, Abba ya samar ma Baffa Adamu tagomashin tallafin karatu daga (federal scholarship board) zuwa kasar Algers inda zai yi karatun degree akan Diplomasiyya.

A wancan lokacin su Abban mu sune manyan ‘yan bokon da kasar Najeriya yankin arewa maso gabas ke ji da su da kuma alfahari da su, yana daga cikin pioneers (sahun farko) na malaman tsangayar tsimi da tanadi ko kuwa tattalin arzikin kasa (department of economics) lokacin da aka fara darasin a jami’ar Jos, suna da damarmaki masu yawa a kan scholarships, ya baiwa samarin Mambila da dama tallafin karatu da scholarship zuwa Algers kasancewar a zamanin ba duka ne suka yarda suka karbi ilmin bokon ba a sanda ya kutso Taraba ya isko Manbila sai daidaiku irin su Abba, don haka su suka fi kowa cin gajiyar shi a zamanin da ake ciki yanzu sanda kai ya fara wayewa samarin Mambila na ta rububin shiga karatun.

A kan Mamman Jaru ta raina Gidado take kuma ganin ta yi rashin dace da auren sa, da ta san da kanin da bazata auri wan ba, har fata take ya mutu don ta samu damar auren kanin sa. Ita kam dama ba ‘yar asalin Mambila bane bakin haure ne daga yankin kasar Kamaru, tsautsayi ya kai shi ga auren ta kasancewar tsohon mijin ta mai rasuwa Malam Jibo aminin sa ne kuma bata taba haihuwa ba, a tunanin sa rashin haihuwa da bata samu ba da Jibo, tsahon shekaru goma sha biyar da suka yi tare da shi zai sanya ta so tilon dan sa Faruku, ta taya Ummati kula da su shi da kanwar sa.

Ba da jimawa ba ya fahimci ba wanda ta tsana a duniya irin Omar din. Abinda ke ran ta a kan kanin sa Mamman ne bai taba sani ba kuma tunanin sa bai taba bashi ba. To ta ina ma zai taba tunanin matar sa kanin sa take so?

Har zuwa wannan lokacin da ya amsa sunan Dr. na ilmi, Mamman Gembu, bai yarda yayi aure ba, fada da nasiha da tsoratarwa babu irin wanda Ummati bata yi masa ba amma ya ki. A karshe Jaru ta ga babu mafita gareta ta samun damar auren Mamman in har Gidado na raye, sai ta soma tunanin hanyar da zata bi ta kawar da Gidado.

Duk abinda ta yi tunanin yi, sai ta ga cewa za’a iya gane ta, a karshe ta nemi guba mai tsinka hanji ta saka mishi a cikin fura. Ta zauna jiran dawowar sa.

Tun tana gadin dawowar sa, ta saka furar da abincin a gaba tana ta kiyasin gobe I yanzu tana cikin Takaba, wata uku masu zuwa sai ta maye gurbin wan da kanin, ko da tsiya ko da arziki (ko da ta asiri ne), tana nan zaune tana wannan saka da warwarar har wani mugun kashi ya zo ya matse ta.

Da fari ta yi kokarin danne shi musamman da yake lokacin dawowar Gidado ya yi amma bayan gidan nan ya ki yarda da hakan, neman fitowa kawai yake yi ko ta halin kaka. Sai ta ga cewa zata iya zuwa tayi kashin ta dawo ba tare da ya dawo ba ko wani ya shigo.

Ta ajiye masa a inda ta saba ajiye abincin sa ta koma sashen ta ta shiga bayan gida kenan Gidado ya shigo tare da wani saurayi.

A nan falon sa suka zauna suna hira ya dauki furar ya baiwa bakon yana fadin.

“Jira ta ta fito Bashari, na san ta zaga ne, ga nan fura ka sha, bari in dibo Asshe cikin gida na ji kukan ta yayi yawa, yanzu haka Faruqu ke cin zalin ta”.

Ya saka takalmin sa ya nufi cikin gida da sauri babbar rigar sa na neman tadiye, shi don in da abinda yafi tsana a duniya to kukan Asshe ne.

Bakon da ya kira da Bashari kuma ya kafa fura a kai yana kwankwada don a yunwace yake ainun a matsayin sa na matafiyi, ko ludayin kan faifai din bai saka ba kada ya bata masa lokaci a yunwar da ya kwaso tun daga kasar Kamaru.

Yana sauke kwaryar daga fuskar sa suna hada ido da Yayar sa Jaru. Jaru ta kwalla kara tana fadin “na shiga uku na lalace Bashari furar Gidado ka sha??? Furar da na sakawa guba ce fa!”

Yayi daidai da dawowar Gidado tsakar gidan tare da Ummati, ya na dauke da Asshe a kafadun sa. Omar na biye da su.

Suna jin abinda Jaru ke fadi cikin yanayi na rashin hayyaci cewa ya ci gubar data sawa Gidado don ya mutu ta auri Mamman, abin nata kamar kaikayi ne ya koma mata, kasancewar Gidado Malami ne ya dade yana yi wa kan sa da ‘ya’yan sa tsari iri iri da ba dai mutum ba sai dai Allah.

Ko kafin su farga Basharin ya fara shure shure kumfa na fita daga bakin sa, sai kuma jikin ya saki bakidaya alamar babu sauran rai a jikin sa.

Wannan bakin al’amari da ya faru a gidan Malam Gidado babu wanda bai ji labarin sa a garin Gembu ba, aka saka Jaru a waka, hukuma tayi mata hukuncin da ya dace, Baba Gidado yayi alkawarin ba zai saki mace ba amma Ummati ta saka shi a gaba ta ce sai ya saki Jaru a take in yaso ya yi kaffara, wannan ba matar zama bace.

Wannan shi ya kawo karshen auren Jaru (Hadiza) da Gidado Dalhatu Gembu.

*****

Mallam Gidado Dalhatu Gembu

Hakika ya firgita da al’amarin mata wanda ya kai shi ga cewa babu shi babu kara aure har abada, wai a kan kanin sa ta yi niyyar kashe shi, wannan wane irin rikitaccen zamani ne na son zuciya da rashin tsoron Allah Allah ya kawo mu? Da yake Shi fa’aalun lima yuridu ne sai Ya juya abin a kan dan uwan ta.

Shi kan sa Dr. Mamman Gembu da ya zo gari ya samu labarin ya firgita iya firgita, Allah ya tuba ko mata sun kare a duniya ai ba zai auri matar yaya Gidado ba koda mutuwar yayi ta Allah da Annabi. Shi kam! A lokacin ya kara jin tsoron duniya dana kaidin mata. Ya kama Omar – Faruq da Asshe dake zaune bisa cinyoyin sa ya rungume a jikin sa yana nema musu tsarin Ubangiji daga mugun ji da mugun gani da sharrin mutum da aljan. Ya roki Allah ya raya musu su har su aurar da su da hannun su shi da Yayan sa, ya yi alkawari tun a lokaci in har yana raye to Asshe bata da miji sai dan uwanta Omar, Omar baya da mata sai kanwar sa Aisha. Kada su je bare su cutar da su da sunan aure.

Wannan abinda ya faru din ya kara nesanta shi daga kan turbar son sake aure shima, dan sauran hope din da ya fara samu na yin aure bayan kammala digirin sa na uku ya bi ruwa. A lokacin ya cika shekaru talatin da biyar a duniya, sabida kyawun surar sa na ‘yan Gembu da kamewar sa Allah kadai ya san iyakar matan da ke haukar ya aure su a can jami’ar Jos, inda yake aikin koyarwa.

Lamarin Jaru ya taba Malam Gidado sosai ya kasa barin ran sa, tun daga lokacin kuma sai ya fara shiga ittikafi, yana nemawa ‘ya’yan sa tsari daga sharrin mutane.

Ya fara fama da ciwon suga kadan kadan da hawan jini wanda a karshe ya kwantar da shi. Mamman ya dauke shi ya tafi da shi Jos don ya ga kwararrun likitoci, sun sha jelen asibiti kafin a samu saukin abin.

Ina da shekaru uku Yaya Omar yana da shekaru goma Allah ya yi wa Baffa na malam Gidado Gembu rasuwa a cikin sujjadar sallahr asubahi.

*****

Rasuwar dan uwan sa Gidado ta kassara shi har fiye da rasuwar matar sa uwar ‘yar sa, Asshe. Na ci sunan mahaifiya ta ne wato Aishatu, Babanmu ke kira na SIYAMA kasancewar an haife ni ne a cikin watan azumin Ramadhana, Ummati kuwa Azumi take kira na. Yayin da a bakin Yaya na Omar nake ‘Boddo’. (Boddo na nufin kyakkyawa da harshen mu na Mambilla).

Kowa kenan da sunan da yake kirana da shi a gidan mu. Wani ba ya taba aron na wani.

Dr. Mamman Gembu a lokacin ya bar jami’ar Jos ya koma aiki da ‘Economic Communiy of West African States (ECOWAS), sai suka maida shi aiki a babbar hedquatar ECOWAS ta kasar Najeriya da ke Birnin Tarayyah. Still Abba ya na nan a gwauron shi. A ruwayar Ummati ta ce wai “aljana ce ta aure shi shiyasa ya ki aure, kuma da zaman sa a haka ai gara mata da ya auri jinsin jinnun”.

A Duk ranar da tasa Abba a gaba tana gaya masa hakan mun yi ta sheka dariya kenan ni da Ya Omar, har sai Abba ya yi kwafa ya fita ya bar mata gidan zai huta da sharrin Ummati.

Shi kuwa Uncle Adam (Young Abba) sunan da na ke kiran sa da shi kenan tun ina karama sabida dasawar mu, ya dade da gama karatun da yake yi a Algers, tun kafin ya dawo ya samu aiki duk ta sanadin Abba da U.S Diplomatic Mission.

Ya auri wata abokiyar karatun sa mai suna Nasara Alkali ‘yar asalin garin Katsina, tushen unguwar Alkali, wadda suka yi karatu tare amma ba’a fanni guda ba, ita Nasara aikin jarida ta nazarta.

Da yake sarkin raha ne autan na Ummati idan Ummati ta saka shi a gaba tana masa ciwon bakin ya rasa inda zai yi aure duk kyawun matan Manbila amma ya tsallake su ya je ya auro bakar bahaushiya sai ya yi maza ya daga mata hannu ya ce.

“Allah sittiri bukui Ummati ba zan auri ‘yan Mambila ba tunda matan duniya basu kare ba, kada su mutu su bar ni da goyon ‘ya’ya in kasa sake aure, ko in sake aure su saka min guba a abinci.

A duk sanda Ummati ta yi masa korafin ya ki auren gida abinda yake gaya mata kenan ya kashe bakin ta, ita kuma sai ta ce “a’ah Adamu, kayi maza ka tuba tam, to dai ba’a yi wa Allah wayo kuma mutum ba ya tsallake kaddarar sa!”

Sai kuma ta tuno Gidado, sai ka ga ta sa habar zani ta rufe fuska ta yi ta shara kuka a gaban mu tana fadin.

“Ya Ubangiji na binne mahaifin su, na binne babban su da hannuna, (tana yi tana daga tafin hannun ta), na bizne matayen su bakidaya, ina rokon ka Ya Allah, sauran biyun nan ka bar min su su binne ni da hannayen su ya Allah in samu masu yi min addu’a (Allah wadu ta mi meta irugo ‘bikkoi’am seni be irami). Wato (Allah ka sa kada in kara binne ‘ya’ya na sai dai su su binne ni.)”

A yanzu haka shi Young Abba ( Baffa Adamu) da matar sa Anti Nasara a jihar Lagos suke zaune inda Diplomatic office na kasar Amurka ke tafiyar da ayyukan su tare da shi.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 1.5 / 5. Rating: 2

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Sakacin Waye? 2Sakacin Waye? 4 >>

2 thoughts on “Sakacin Waye? 3”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×