Skip to content
Part 2 of 73 in the Series Sakacin Waye? by Sumayyah Abdulkadir Takori

To ita kam Ummati ba ma wannan ta duba ba wajen aurawa Gidado da Mamman Aisha da ake kira (Asshe) da Hafsatu da ake kira (Hassu) illa duk fadin garin Gashaka su ne yaran da aka tabbatar sun sauke Al’qur ani sun kuma haddace shi kafin su cika shekaru goma-goma. Hassu da Asshe ‘yan biyu ne masu kamanni daya basu taba yin karatun boko ba sai na addini. Wanda ya sanya suka zama ‘yammata masu nutsuwa da tarbiyyah ababen rububi a wajen samarin Mambilla, kowanne uba da kowacce uwa fatan su a auro musu zuriyar Muhammadu Jauro, ga kuma kyawun sura da Allah ya basu.

Gidado da Mamman ra’ayi ya banbanta a kan abinda suke so a rayuwa, yayin da ilmin boko ya kunno kai a Manbila wasu sun karbe shi da hannu bibbiyu musamman kiristocin cikin su, wasu kuwa musaman musulmi suna tababa a kan amsar shi, wasu da yawa sun yi hannun riga da shi ne da cewa sakon missionaries ne.

Mamman dai ya karba da hannu bibbiyu ya shiga makaranta yayi firamare da sakandire yana kuma hadawa da kiwon shanun su na gado da noma duka bai bar Gidado da wahala shi kadai ba, Gidado ya yi wa kansa Allah ya kiyaye da boko ya maida hankali wajen kula da mahaifiyar su, daga noman da kiwon babu wanda ya dame shi ya fi gane ya tara yara a a zaure yana koya musu karatun Al’qur’ani, a kowanne karshen sati iyayen su su bashi sadakar kudin Laraba. Da haka ya zama malami sosai har manya yake karantarwa littafan addini a Alhamis da Juma’ah.

Dan autan Ummati kuwa wato Baffa Adamu har ya fi Mamman son boko, Ummati kuma ta basu dama kan kowanne ya yi abinda yafi so in dai ba sabon Allah bane.

Ta sadaukar da shanun gadon su masu yawa kafin a bawa Gidado da Mamman auren Asshe da Hassu. Gidado ya auri Hassu, Mamman ya auri Asshe. Gidado shi ya fara samun rabo shekara na zagayowa Hassu ta haifa masa Umarul-Faruq. Yaro tamkar khaki (photocopy) na mahaifin sa Gidado.

Asshe kuwa shiru, tun ana saka rai har an hakura, da abin ya dame ta duk inda ta ji mai bada maganin haihuwa sai ta je a boye ta karbo sassake don idan ta bari Gidado ya sani zai sata a gaba ne yana mata wa’azin Allah kadai ke bada haihuwa, ta yarda Allah ke bada haihuwa amma shi ya ce tashi in taimake ka.

Lura da damuwar Asshe da Ummati ta yi a kan haihuwa. Da Faruq ya isa yaye sai Ummati ta dauke shi ta baiwa Asshe. Don farin ciki Asshe saida tayi kuka a lokacin ita Hassu goyon ciki na biyu take yi.

Asshe ta dauki Umar ta rike da dukkan kaunar duniya da kulawar data fi wadda yake samu a gun mahaifiyar sa. A wajen haihuwar na biyun ne sai ya zo da karar kwana Hassu ta rasu tare da abinda ke cikin ta.

A wancan lokacin zautuwa ne kawai Malam Gidado bai yi ba sabida mutuwar matar sa uwar dan sa abokiyar rufin asiri, Hassu. To kuma ina ga ‘yar uwar ta da suka fito daga mahaifa guda suka yi yarinta da kuruciya da aure tare?

Da kyar da kuma rokon Allah har da rubutun dangana Ummati ta samo kan sa, ya koma karantarwar sa kmar yadda ya saba. Malam Muhammadu Jauro wato mahaifin su Hassu ya ce “inama ina da wata diyar! Da na baiwa Gidado, domin ban taba yin surukin da ya san darajar mace kamar sa ba, amma duka na aurar da su.”

Tun daga lokacin Baba Gidado ya dauki soyayyar duniya ya dora a kan Ya Umar, Inna Ashe kuma ta goya Umar – Faruq goyo na amana bata da lokacin kan ta sai na Faruq, bata da hidimar kowa sama da tasa ko mijin bata bashi lokacin da ta ke baiwa Faruq, koda yake ai dama Dan ta ne tunda kuwa shaqiqiyar ta ce ta haife shi. Wadda har ta rasu tana gaya mata a kullum “ke na haifawa Umaru dan ki ne halak malak.”

Auren Asshe da Mamman ba jimawa gurbin karatun sa da ya nema a jami’ar Jos ya fito, ya tattara ya tafi Jos ya bar Asshe tana goyon Omar-Faruq a gaban mahaifiyar sa Ummati. Sai da Omar ya shekara bakwai cikin ikon Allah buwaya gagara misali rana daya (bayan ta riga ta fidda rai), sai gashi Allah ya dubi hakurin ta da zumuncin ta a kan maraya ya bata nata rabon, wato ta haife ni.

Lokacin da na fara tasawa sai mutane ke cewa ai babu wanda nake kama da shi duk cikin iyayen mu, Ummati da ma dangin mu na wajen uwa dake Gashaka sai da Omar kadai. Dukkan mu kuma da iyayen mu mata muke kama don haka jama’a da yawa da basu san tarihin mu ba sun dauka uwa daya uba daya muke, musamman yadda Omar yake taya Asshe raino na tun ina mitsitsiya ta ya ke goya ni, yaje makaranta da ni goye a bayan sa.

Tun ana korar sa kan ya mayar da ni gida ya dawo, sai malamin ya ga ya tsaya a bakin tagar ajin su ya ki tafiya yana leke yana sauraron karatun daga bakin taga, dole malamin su yake jin tausayin sa ya kyale shi yake zuwa karatu da ni. Don ya lura kaunar da Ya Omar yake min tana da yawa.

Wannan ya faru ne a sanda na fara wayo. Wani abun jimami da ya biyo bayan murnar haihuwa ta shine tun bayan haihuwar Asshe ke fama da matsalar zubar jini, an yi yawon neman magani iri-iri har babban asibitin jihar Taraba inda likitoci suka tabbatar da cewa magunguna masu karfi data yi ta sha na gargajiya don neman haihuwa su suka lalata mahaifar ta, Allah ne ya rubuta zan shaki iskar duniya shiyasa har ta iya ta haife ni.

Aka saka ranar da za’a yi mata aikin cire mahaifa don a samu zubar jinin ya tsaya ta huta ta samu lafiya gabadaya amma babu batun sake haihuwa.

Da ranar ta zo aka yi komai lafiya aka gama lafiya, ana ta murna wahala ta kare, ashe kuwa da gaske babbar wahala ta kare domin kuwa Inna Asshe, bata farfado daga allurar anaesthesia ba.

*****

Mamman

“Kina nufin Hassu da Asshe duka sun shigo rayuwar mu ne ni da Yaya Gidado halan don kawai su haifa mana marayun ‘ya’ya su bar mu da kananan marayu su koma?

Me kike nufi da cewa ta zarce a cikin allura?

Kina nufin, nima ni kadai zan raini ‘dan nan/’yar nan kamar yadda Yaya Gidado yake rainon Omar Faruk shi kadai?

To shin da wanne nonon kike nufin zan raine shi/raine ta?

Ai gara Umar ya sha nonon uwa har na tsayin shekaru biyu ko ba komai ya san dumin jikin uwar sa, ki ji tausayin halittar Allah baiwar Allah ki fada min gaskiya cewa wasa ki ke….. kice min mata ta Asshe barci take yi a cikin allurar yanzunnan allurar za ta sake ta ta tashi mu tafi gida ta shayar da dan ta.” Sai hawaye wasu na korar wasu suka biyo bayan maganganun da zaka tabbatar cikin fita hayyacin sa yake yin su.

Abinda Baba na ya fadawa Nos din da ta gaya masa rasuwar mahaifiyata kenan kafin hawaye su cigaba da tsinke masa, ya kuma kasa karbar jaririn da take ta faman bashi kamar ya ce mata “ki musanya min shi da mata ta Asshe. Zata iya kara haifa min wani, amma ita bazan kara samun kamar ta ba!”

Nos dai bata gane sambatun wannan mijin mai tsananin son matar sa me yake nufi ba, ta dai san zafin mutuwar matar sa ne ke bugun sa ya kuma fidda shi a hayyacin sa, sai hakuri take bashi. Tana tuna masa ayar Ubangiji da ta ce “Kullu Nafsin Za’ikatul Maut.”

Ta kuma miko masa ni nannade cikin zanin atamfar mahaifiya ta tana fadin,

“Yi hakuri ka karbi kyakkyawar kyautar ‘yar da Allah yayi maka ka ji! ‘Ya mace ce ba namiji ba. Idan ka yi mata kyakkyawan raino watarana zata ji kan ka kamar mahaifiyar ta.”

Haka Abba ya karbe ni cikin yanayi na dimauta da yankewar buri gaba daya ya fito waje neman Ummati, can ya gano ta inda ya bar ta tana tahiyar sallame sallahr walha a inda ya bar ta tun safe kenan tana rokawa Ashe sauki a cikin tahiyar ta, ya karasa gabanta ya ajiye mata jaririyar a saman cinyar ta sannan ya koma gefe ya saka kai cikin kafafuwan sa ya saka kuka.

Kukan da tun kafin ta san dalilin sa Ummati ta tabbatar itama Asshe maraya ta bar mata, marayun sun zame mata biyu, Ya ilahi, sai ta sallame sallahr ta ce masa “ka ce Innalillahiwa’innailaihiraji’oun Muhammadu, shine kawai abinda zaka yi Allah ya yi farin ciki da kai a wannan yanayin. Ka kuma karbi ‘yar ka ka yi mata huduba da sunan mahaifiyar ta.

Ka yi fatan Allah ya baku tsahon rai ku ku raine su, ka je ka daukota mu tafi ka wanketa da hannun ka ka yi mata suttura ka kai ta makwancin ta da kan ka shine babbar soyayyar ka gare ta a yanzu, ka cigaba da nema mata aljannah”.

Daga Jalingo kai tsaye suka yi shatar mota zuwa Manbila aka yi wa mahaifiyata sutturah. Mutuwar Inna Asshe ta fi taba Ya Omar fiye da kowa a gidan don shi bai san cewa ba ita ta haife shi bama.

Omar bai san maraicin uwa ba sai da Inna Asshe ta rasu, kulawar mu ta koma hannun Ummati, duk da Ummati bata raga mana komai ba na kulawa da tarbiyyah amma Kakar mu ce kuma tsohuwa ce. Kulawar Kaka daban kulawar uwa-mahaifiya daban, idan ka hada duka biyun zaka fi kowa morewa, uwa ta kwabe ka har da bulala Kaka ta lallashe ka da tuwo da koko, tunda dai Kaka da sangarta jika aka san shi.

Mafari kenan da raino na ya koma hannun Ummati, muka shaku wata irin shakuwa da Kakata Ummatin Mambila, kakkarfar dattijiya, doguwa fara mai kyawun surah wadda bata daukar kowanne irin wargi ko raini a kan jikokin ta, zaka yi mata komai ka kwana lafiya amma kada ka taba Aisha da Omar. Da ganin Ummati zaka san an zuba zamani kuma an zuba kyau an juya miji a lokacin kurucciya.

Abu na farko da ya assasa shaquwar mu zuwa shakuwar da ta zarta ainahin wacce ke a tsakanin Kaka da jika ta zama ta mahaifiya da tilon ‘yar ta, ya sanya kuma ta dora min soyayyar duniya shine kasancewar ita bata taba haihuwar diya mace ba, na biyu ita ta shayar da ni daga madarar shanun ta, kuma na ci sunan mahaifiyata wadda tayi mata biyayya sosai.

Baba Gidado yayi aure da jimawa da Jaru, matar wani marigayin abokin sa, bayan tsayin lokacin da ya dauka babu aure, don ya tabbata ba zai sake samun mace tamkar (Ummu-Faruqu) ba kamar yadda ya ke kiran Hassu har gobe, amma ko kadan baya jin dadin ta, haka dai ake zaman da dadi ba dadi.

Ya riga ya saba da matar sa Hassu mai addini, mai hakuri da kuma godiya da duk abinda ya kawo mata, mai yakanah, wadda ko kara ya ajiye ya ce kada ta tsallaka bazata tsallaka ba, wadda in ya ce farin yadin nan baki ne zata ce da shi “bakikkirin kuwa”, amma Jaru? Akasin Hassu ce a komai.

Ya yarda hakika Allah ba ya barin wani, don wani ya ji dadi. Da bai dauke masa Hassu ya hada shi da Jaru ba, da bai raba Mamman da Aishatu ba sabida wadannan matan guda biyu tamakar Hurul ‘eenin duniya suke ga mazajen da Allah ya baiwa su;

Ga kyau ga kuma kyan hali. Ga addini da nasaba mai tsafta. A hakan dai suke zaune shi da Jaru; yau fari gobe tsumma, sabida ya yi alkawarin ba zai taba sakin mace a rayuwar sa ba, sai dai ta bizne shi ko ya bizne ta.

Babbar damuwar sa da Jaru shine ta ki jinin Omar Faruq, ba dama ya zo sassan su goye da ni zata kora mu da tsawa da bulala, daga sanda ta fahimci Omar dan sa ne na cikin sa ba na kanin sa ba tsanar da ta ke ma Omar ta karu, sabida kanin nasa (wanda ta fahimci a Jos yake zaune zuwa yake yi ya koma), kullum ya zo tsarabar sa ta Omar-Faruq ce baya ko ta kan tashi ‘yar da ya haifa a cikin sa sai Omar, Omar dai Omar dai ko’ina ka shiga sunan sa ne a bakin jama’ar gidan alamar ya gama mamaye zukatan su.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 4.5 / 5. Rating: 2

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Sakacin Waye? 1Sakacin Waye? 3 >>

6 thoughts on “Sakacin Waye? 2”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×