Berom, sune kabilu na farko mafi girma da shahara a jihar Filato, tsakiyar Najeriya. Jos ta kunshi kananan hukumomi guda hudu wadanda suka hada da Arewacin Jos (Jos North), Kudancin Jos (Jos South), Barkin Ladi (Gwol) da kuma Riyom. Mahaifiya ta ‘yar Barkin Ladi ce mahaifina kuma dan Riyom ne. Su duka kananan hukumomi ne dake makwabtaka da juna. Mahaifa na sun hadu a chochi har soyayya ta shiga tsakanin su wadda har ta kai su aure suka kuma haife ni.
Saidai ban yi rayuwa mai tsayi tare da su ba, shekaru biyu da haihuwa ta suka yi. . .