Skip to content
Part 34 of 73 in the Series Sakacin Waye? by Sumayyah Abdulkadir Takori

A cikin watanni ukun da Young Abba ya diba mana don tafiya Najeriya gabatar da Hamzah ga su Ummati, mun shaqu mun aminta mun fahimci juna fiye da zaton dan adam. Hamzah irin mazan nan ne da in suna son mace to basu da lokacin kowa da komai sai nata. Ba shi da abinda yasa a gaba yanzu daga koyon ibadah daga Young Abba da sauran abokan sa musulmai su Muhyiddeen sai aikin sa sai Siyama. Kullum yana falon Young Abba, har ta kai ta kawo kwanon abincin daren sa ya dawo gidan mu.

Sabida shi yanzu kusan kullum da dare tuwon Acca muke yi a gidan, sai muke yin miyar ganyayyaki kala daban daban da nama ko kifi iri daban daban. Idan kuma baya son mai nauyin sai ya ce in masa ‘gwate’ duk abincin Birom ne. 

Saura kwana uku tafiyar mu Najeriya duk wasu shirye shirye Young Abba ya kammala su. Ya kira Yayan sa Dr. Mamman Gembu ya gaya masa ranar Asabar zai shigo Abuja tare da iyalin sa bakidaya kuma a gidan sa zamu sauka. Tare da mijin da Siyama ta samu anan Washigton.

Budar bakin Abba sai cewa yayi.

“Kowane ne ta kawo maka ka aura mata, ba sai an zo waje na ba, sau nawa zan maimaita maka na bar maka Siyama ‘yar ka ce? Ai na dade da tahowa daga rakiyar Siyama tun lokacin da ta zabi kashe kan ta a kan ta yi min biyayya. 

Idan ka ga na yafewa Siyama Adamu, to Omar ne ya dawo gare ni, ya zabi matar data fi ta komai nayi masa aure.”

Young Abba yayi lallashi da ban bakin duniyar nan kan Abba ya karbi bakuntar mijin Siyama ko da sau daya ne Abba ya kafe ba ruwan sa da wani mijin da ba Omar ba, ba kuma a gidan sa ba, ta je ta zabi duk wanda take so rayuwar ta ce. Amma duk da haka Young Abba bai fasa tausar shi ba, ya nace masa a kan ya ya yi hakuri ya sawa Siyama albarka, ya karbi kaddarar cewa ita da Omar are not meant for each other. 

Ya kara da cewa an tabbatar masa Omar yana nan lafiya kuma yana kasar England. Ya ce “ni yanzu ba tausayin Omar nake ji ba Dr. Haushin sa nake ji matuka, yadda ya iya ya bar mu cikin zullumi har tsayin wannnan lokacin a gani na, bashi da hujjar yin hakan, sai don in dama baya ra’ayin auren Siyamar.”

Abba yayi murmushin takaici ya ce “nikuwa na san Omar na ra’ayin Siyama har gobe, na ga alama ku kuka daure mata gindi ta yi abinda take so. To ai ni ban mata baki ba sam, ban kuma taba yi mata addu’ar kada ta ga alkhairi ba Adamu. Na dai ce idan ta zabi duniya da kyale-kyalen mazan cikin ta hakika duniya zata biyar da ita ta lalama. Kowa yayi SAKACI da iyayen sa akan kyale -kyalen zuciya da muradan ta shi zai ga abinda baya so.

Kuma dama ai kaine madaurin auren ta, to na meye sai anyo tattaki kasa ya kasa an zo waje na? 

Ba sai na gan shi ba Allah ya sanya alkhairi, ku yi mata auren anan inda kuke tunda ka ce mijin ma dan can ne”.

“A’ah dan Jos ne, aiki ne ya kawo shi nan kamar yadda ya kawo mu. Broadcaster din VOA ne.”

“All the best Adamu!”.

In ji Abba, daga haka ya kashe wayar sa ba tare da ya kara komai a kai ba.

Ran Young Abba ya baci sosai. Ya rasa wane irin mutum mai baudadden ra’ayi daban dana kowa ne Yayan nasa. Shin shi auren zumuncin dole ne? Ko a ka ce lallai sai Siyama da Omar sun Yi aure ne zasu yi zumunci a tsakanin su? Bai san cewa wani auren zumuncin bata zumunci yake komawa ba? Shi ko kadan bai ga laifin yarinya Siyama ba don ta zabi mijin da zuciyar ta tafi kwantawa da shi. 

A fili yace “ai shikenan, na karbi kyautar da ka yi min Yaya Dr. Zan mata auren ni kadai da duk wani gata da Uba ke Yi wa ‘yar sa. Kuma insha Allahu Siyama bata yi zaben tumun dare ba.”

A daren ya gayawa Nasara mun fasa tafiya Najeriya sai bayan auren Siyama. Shi kadai zai yi wa Siyama aure Dr. Mamman ya ce ya bar masa Siyama ba ya bukatar a kawo masa mijin ta Abuja. Nasara cikin damuwa tace,

“You see. Yana nufin bai yi na’am ba fa kenan….. Baban Ahyan bana so mu yi abinda daga baya zai zo ya zame mana damuwa daga mu har Siyaman. Ka bi shi a hankali har sai ya amince don radin kan sa. Shi fa ya haife ta ba kai ka haife ta ba.”

Young Abba yace “bar ni kawai da tsohon dan bokon nan, ni na san halin dan uwana ciki da bai din sa, tunda kika ji yace haka har yanzu da Omar yake son hada ta aure. 

Ni Kuma wallahi ba zan taba bari yayi mata auren dole ba. Zan taimaki Siyama ta samu cikar mafarkanta koda abin zai zo ya yi haunting dina daga baya. In dai Siyama ta samu kwanciyar hankali da zaman lafiya a gidanta shikenan. Baki sanni bane kema wajen taron aradu da ka. Nima rigimammen kaina ne. Wallahi na fi shi duk wani taurin kai da zafin kai da yake ji. Ai ni addini ya baiwa alhakin daura mata aure, ni ne alwaliyin ta.”

Nasara zata yi magana Young Abba ya katse ta “kin ga in bazaki tayamu da addu’a da fatan alheri ba Nasara kema ki koma gefe kiyi kallo. Ni da shi karen bana zai yi maganin zomon bana”.

Kuma a daren bai kwanta ba sai da ya kira Hamzah yace “babu amfanin zuwan mu gida Nigeria, Baban Siyama ya bar min waliccin Siyama, so ni zan aurar da ita. Idan ka amince da cewa kana son Siyama ne saboda Allah, kuma zaka rike min ita da soyayyah da amana ka kawo sadaki muje Shaykh Isma’il Memon ya daura muku aure gobe bayan saukowa sallahr Juma’ah.”

Wannan shine albishir mafi girma a tarihin rayuwar sa. Kuma abu mafi dadin da ya wayi gari da shi a safiyar yau. Me zai yi wa Young Abba ya biya shi wannan kauna ta fisabilillah da yake masa banda ya rike masa ‘yar sa da soyayya da amana har zuwa karshen numfashin sa?”

Ko nawa ya yankawa sadakin Siyama sai ya ga cewa yayi kadan a irin kaunar data yi masa da wahalar data sha a kansa da kuma karamcin Young Abba gare shi. Da ace shi din wani mai hali ne da ya biya sadaqin Siyama da silallan gold. Amma da bashi da halin hakan, kuma yana so ya biya sadaqin ta in a unique way, sai ya yanke shawarar cewa zai biya da warawaran zinare sirara guda uku wanda Hausawa ke kira (Awarwaron gwal), wadanda yake ganin zai iya sayen su idan ya sanya motar sa guda a kasuwa. Kuma hakan ce ta kasance.

                                         ****

RANA MAI DIMBIN TARIHI/RANAR TABBATUWAR/CIKAR MAFARKAN ZUWA REALITY

Karkashin waliccin Shaykh Isma’il Memon da kanin mahaifi na Adamu Dalhatu Gembu aka daura aure na da Hamzah bayan sakkowa sallar Juma’a kafin watsewar al’ummar musulmin da suka halarci sallahr Juma’ah a masallacin DAAR AL -ULOOM AL- MADANIA a ranar 2/2. Wadda tayi daidai da ranar Takutaha a Najeriya.

Aunty Nasara ta roki Young Abba ya bata sati biyu kafin tarewa ta don ta gama shirye-shiryen ta a nitse. Amma Young Abba ya ki, ya ce shi kawai da sunnah zai yi koyi, ayi walima washegarin tarewa, anjima da dare Hamzah ya zo ya dau matar sa su wuce. Daga baya ko me zata yi sai ta yi.

Hankali na bai tashi ba sai da naji wannan hukuncin na Young Abba, domin na dauka an dai daura ne kawai babu maganar tarewa har sai mun je Najeriya ya gabatar da Hamzah ga su Ummati mun dauko albarkar Abba a cikin al’amarin. 

Tunda har Abba yaki yarda ya ga mijin aure na ko ya karbi maganar auren nake cikin tashin hankali, amma shi Young Abba ko a jikin sa, ya ce da Hamzah ya bashi mukullin gida zai zuba min kayan aure kamar yadda muke yi a namu al’adar. Shikuma Hamzah ya ce gidan sa baya bukatar komai sai SIYAM. Ya riga ya zuba komai don bai san ana hakan ba. Yana rokon Young Abba kada ya sayi komai na gida gara ya yi min wani abun daban da kudin. 

Young Abba ya yanke shawarar saya mani karamar mota tawa ta kaina a matsayin gift na aure. Amma yaki yarda da batun Hamzah na cewa haka nan zai kaini zikau, yace ko bedroom daya ne ya bashi ya saka min gado. Hakan kuwa aka yi.

“Baban Ahyan kayi hakuri ka saurareni, don Allah ka daga tarewar nan, akwai shiri irin namu na mata dana ke so na yi wa Siyama, kuma yana dan daukar lokaci, na rasa gaggawar me kake yi ta kai Siyama gidan Hamzah kamar kana neman kai da ita, ka bari in shirya ta da kyau sabida ban yarda Hamzah bai taba sanin mata ba a wadannan budaddun idanun nasa da yawan shekarun sa, ina so ‘ya ta Siyama ta kama zuciyar mijin ta sosai ta yadda zata dauke hankalin sa daga kan sauran matan banza.”

Wata harara Young Abba ya zuba mata, ya ce “yanzu na gane dalilin naki, so kike ku haukata dan mutane irin yadda kike haukata ni, to ciwon da namiji na da namiji ne ban yarda ba, ki bar ta ta je masa a halittar da Allah yayi mata wallahi ko zuma kika bata ban yafe ba. So nake ya kaunace ta saboda Allah ba don wani artificial abu ba. Ina fatan kin fahimce ni?”

Nasara jikin ta yayi sanyi, tace “Baban Ahyan ba haramun bane, ko kana da kyau aka ce ka kara da wanka, Nana Aisha R.A tana shan abinda zai sa ta kara gamsar da mijin ta kuma Annabi SAW bai hana ba.”

Young Abba ya dauki mukullin motar sa ya wuce ta a wurin yana cewa “sai kuma kiyi, na dai gaya miki ban yarda ba. Ki koya mata ladabi da biyayya kafin ya zo daukar ta anjima. Walimar ma sai washegari za’ayi ta kuma a gidan su ba’a VOA ba, bana son terere.”

Nasara ta ce “wannan ne kuma baka isa ba. Dole VOA su san da wannan aure, dole a yi walima irin wadda ba’a taba yin irinta a VOA ba, dole VOA su san HAMZAH MAWONMASE YA MUSULUNTA YA KUMA AURI MUSULMA!”.

 TAKORI

                                     ****

               TSOKACI A KAN (SAKACIN WAYE? 3)

Yanzu muka fara! Ko ince bamu fara komai ba, domin yanzu ne muka fara shiga cikin labarin SIYAM da HAMZAH. Duka wannan shimfida ce. Gundarin labarin na zuwa cikin littafi na uku. Inda acan ne zamu shiga cikin ainahin rayuwar auren su. Mu ga shin Hamzah zai cika alkawuran da ya daukarwa AISHA-SIYAMA?

Ina Omar-Faruq ya shiga ne? Shikenan ya rasa Boddon sa har abada ko kuwa burin Abba zai cika a kan su?

Yaya Ummati zata karbi auren Siyama da Hamzah? Yaya kuma tasa Kakar Grandma Veronica? Tunda dai dukkan su mun ga cewa kusoshi ne a rayuwar jikokin nasu?

LITTAFIN SAKACIN WAYE? NA UKU Na tafe da dukkan wadannan amsoshicikin gidan Siyamah da Hamzah. Bayan na ji ra’ayoyin ku a kan labarin  jaruman namu wato SIYAM da DREAM HUBAND din ta. Yau dai ga MAFARKIn Siyama ya tabbata. Sai mu biyo bayan tabbatuwar mafarkan kuma, mu duba su filla-filla a mahanga ta rayuwar yau da gobe da kuma zahirin rayuwa ta reality.

NAGODE MUKU DA JIMIRIN BIN RUBUTU NA BABU GAZAWA TAKORITES A DUK INDA KUKE. WADANDA NA SANI DA WADANDA BAN SANI BA. MASU VOLUNTEERING ALLAH YA HADA MU CIKIN ALHERIN SA, HAR ZUWA RANAR DA MUKA DAINA NUMFASHI.

               Taku har abada.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Sakacin Waye? 33Sakacin Waye? 35 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×