Skip to content
Part 35 of 73 in the Series Sakacin Waye? by Sumayyah Abdulkadir (Takori)

LITTAFI NA UKU

The Berom Man’s Bride

Young Abba bai tsaya jin surutu da karadin da matar sa Nasara ke yi ba, ya wuce ta cikin  sauri don ya san halin ta, in ta ce zata yi abu, to fa sai tayi din hankalin ta ke kwanciya, Nasara mai naci ce. Kai tsaye ya doshi kofar fita daga falon bayan ya suri mukullan motar sa da ke kan tebir, yana mai amsa kiran da Hamzah ke ta masa a waya, yana tafiya zuwa kofa yana ce da matar tasa.

“Wannan kuma matsalar ku ce, ku da ma’aikatar taku. Young Lady, carry your problem and leave me alone, ni dai ‘ya kawai na aura wa Hamzah, kuma ita zan kai masa as natural as halittar Allah, ba zan yarda  ki koya mata siddabarun ku na mata irin wanda ake min ba, a susuta dan mutane haka kawai, ana abin nan har makwabta na jiyo shi, ina dalili?

A cikin gida kuma ya zama sai yadda aka yi da shi iri na, a maida mutum ba ya da ta cewa baya da wani katabus a gidan sa, ya zama kamar waina a tanda.”

Ya fada a dake, fuska a gintse da iyakacin gaskiyar sa, amma daga ji zaka san ya fada ne cikin sigar tsokana da son tunzura Nasara. Irin abun ya dade yana damun sa dinnan, bai yi magana bane sabida bai samu dama ba sai yau da ta kama.

Hakan kuma ya faru ne kasancewar shi Adamun, da dukkan zuciyar sa yake son Hamzah, kamar kanin sa na jini ya dauke shi, yake kuma jin sa a ran sa. Don haka a cewar sa ba zai bari a mallake shi ba.

Nasara ta kama baki cikin mamaki tana duban mijin nata Adamu Gembu, ta bude bakin ta hangangan! Ta kasa rufe shi don dariya da mamaki. Sannan daga bisani dai ta rufe bakin, tana gyada kai kamar kadangaruwa, sannan ta girgiza kai cikin hadiye dariya, ta kasa cewa komai. Abin na Young Abba ya daina bata haushi yanzu, ya koma bata hamshakiyar dariya. Rigimar sa kamar ta tsohon kuturu wani lokacin. Yadda ya fitittike ya na furta maganar cikin tsohon takaici da alama maganar ta dade tana nukurkusar sa, abin nasa ya bala’in bata dariya. A karo na uku ta gyada kai cikin yardarwa ran ta, ta aikata duk abinda Adamu yake fadi da wanda ke fita daga bakin sa a halin yanzu. Sannan ta ce.

“Duk na ji Baban Ahyan, ko me zaka ce, ka dade baka fada ba in dai a kai na ne, tam. Ni Nasara da kake gani duwawu ce dole a zauna da ni, ko ana so ko ba’a so. Kuma ko babu siddabaru, dole a sarawa mu matan Katsinawa ta fannin kula da miji a gado.

Ashe-ashe dama kallon da kake min kenan Adam? Ni ce ban sani ba? Kallon mai yi maka siddabaru da mallaka sabida kawai ina gyara maka shimfida don in dauke idanun ka daga matan haramun? To na karba na kuma gode. Tunda abin arziki ya zama na tsiya.

Dama an ce wani abun mutum baya sanin ana kallon sa da shi sai dalili ya yi dalili, yau dalili ya yi na san irin kallon da kake mini, ka dade baka fada ba, walima ce dai dole ka bar mu mu yi.

Allah na tuba ai Siyama matar manya ce, abin nufi, ko ban bata komai ba na mata tsaf zata mallake mijin ta “Hamzah Al-Mustapha Mawonmase” din da kake ikirarin baza’a mallake shi ba, zai shiga hannu har fiye da irin yadda aka mallake Uban ta mai jiji da kai Adamu Gembu, balle wannan Hamzahn da ya fi ruwan sha saukin sha.

Ai wato wuyar ta ya yi sakacin zuwa gare mu a daren farko, wuyar ta ya yi ganngancin nan Adam, in ka ga ya zauna lafiya daga sannan, to ka tabbata; ni Nasara Babar Siyama na ce; bai yi gangancin kawo kan sa ga ‘ya ta ba.”

Daga bakin kofa Young Abba ya juyo ya yi mata kallon so, wani mashahurin kallon soyayyah na yaya zan yi da son ki? Yana murmushin jin karin son matar tasa sabida dimbin karamcin ta ga ‘yan uwan sa, da duk wanda ya kawo ya ce nashi ne. Karar da take yi masa a sha’anin Siyama, kamar Siyaman jinin ta ce ba nashi jinin ba, nan kusa bai taba ganin ko jin labarin matar kanin Uba irin matar sa ba, kullum ji yake ana cewa a society irin na hausawa tsakanin mata da dangin mijin su, babu kauna sai kishi, jin zafin juna da kiyayyar juna, shi kam kullum yana ganin sabanin hakan  a kan matar sa Nasara, da matar Yayan sa wato, Wasila, ko kuwa su din sun yi sa’a ne kawai? Young Abba Ya dube ta cikin kashe ido ya ce.

“Kin ci darajar sabon Baby dake like jikin nan, bana so in wujijjiga shi, da kin ga mallakau yanzun nan.

Mallakau din naku na ‘yan dakin kara kika sani, baki san real mallakau sai fulanin Mambillah ba.”

Daga haka ya fita da saurin sa. Ya bar Nasara na ‘blushing from ear to ear’.

Daga can daki na, ina iya jiyo komai na dramar da ke wakana tsakanin Young Abba da mai dakin sa Aunty Nasara, sarakan takala da tsokanar juna. A can baya in suna irin wannan dramar ta su ta fada cikin sigar shaguben soyayya ga junan su, sha’awa suke bani, kasancewar suna yi ne da sigar soyayya mai ban kaye da burgewa, sai in lalace a sauraron su ina buga murmushi ni kadai a daki na, cikin dakacen samun bayyanuwar ‘Dream Husband’ dina nima, wanda a lokacin nake cikin tsananin begen bayyanar sa, muma mu yi ta buga fadan soyayya irin nasu, mai kara shakuwa da tsayawa a zuciyar masoya.

Amma abin mamaki yau basa gaba na, daga Young Abban har maidakin nasa (Nasara). A zahiri ina jin su ne da tashin sautin muryoyin su, amma sam bana fahimtar shirmen su ko kadan. Kasacewar hankali na kafatanin sa ba ya jiki na.

I’m fighting with some sort of mixed feelings and unexpressible emotions (feelings na farin ciki da fargaba duka a lokaci guda).

Farin ciki na shine yau na mallaki abinda zuciya ta da ruhi na ke so tun daga tasowa ta har girma na, wata da watanni, shekara da shekaru zuciyata bata huta ba da neman sa ba, ina mai begen zuwan wannan ranar, yau Allah ya nuna min ita, ya kuma mallaka min mukullin mafarkaina a tafin hannu na, cikin hikimar sa, tsarkin mulkin sa da buwayar sa, mafarkai na sun gama tabbata, sun zamo absolute reality! Tunda yau na amsa sunan “The Berom Man’s Bride (Mrs. Hamzah Mustapha)”. Idan na tuna a yanzu babu shamaki, babu hijabi komai kankantar sa tsakani na da shi.

Alas! Dukkan buri na in dai na duniya ne ya gama cika yau; na zama matar sa/abokiyar rayuwar sa ta har abada, daga ranar yau dana mallaki warawaran zinare guda uku daga gare shi, matsayin ‘sadaq’ dina, (ina fatan rakiyar mu ni da shi din ta yi tsaho, ta yi karko ta yi inganci daga nan har gidan gaskiya wato, aljanah).

“HAMZAH!”

Na furta sassanyan sunan mai asali a hankali, wata ni’imar soyayyah na sauka a zuciya ta.

Wani kwayan mutum guda daya a duniya da na ke yi wa so da kauna na hakika, na bada misali a cikin labarun hikaya na soyayya, mutumin da nake yi wa so mara iyakar da ni kai na ban sani ba, wanda biro ya yi kadan ya rubuta shi, sai dai ya rubuta burbushin sa, ta hanyar kwatantawa da kintatawa, saboda babu irin sa a duniyar mu ta yanzu, a wajen wasu ma (is just a fairytale) haka cikin mutanen dana taso na girma cikin su a gidan mu, babu wanda ya gasgata namu labarin soyayyar, basu saba jin soyayya ta mafarki mai gudana a ido biyu irin tawa ba. Shi yasa suka kasa karbar ta, suka kasa fahimtar ta musamman Abba na.

Na sha wahala da gwagwarmaya ba ‘yar kadan ba a kan soyayyar Hamzah Mawonmase, na tsallake rijiya da baya iri-iri, ciki har da shan guba don tseratar da mafarkai na.  Amma sai gashi bayan samun cikar burin nawa (bayan tabbatuwar komai) bayan an yi tying ties din igiyoyin aure na musulunci uku sun tabbata tsakanina da shi, to my utmost surprise, na kasa jin farin ciki, na kasa murna na kasa ko da murmushi sai fargaba da zullumi. Zullumi na shine meye makomar auren nawa alhalin Abba Mamman Gembu, ya ce babu hannun sa?

A cewar sa Abban. Baya bukatar ganin mijin nawa, baya bukatar a wani gabatar da shi gare shi, ko wanene Young Abba ya aura min can ta matse mana, haka ba ya bukatar karbar sadaki na.

A wannan lokacin, wata sabuwar damuwa ce tsantsa mai kamanceceniya da tashin hankali suka rufto min, suka taru suka yi min rubdugu a tsakar ka, suka danne ni yadda suje so, sanadin wannan fargaba da zullumin nawa.

Fargabar kuma ba ta komai bace ta aure ce, irin ta kowacce diya mace a ranar farko da aka daura mata aure na farko a rayuwar ta.

Naturally, daga lokacin da aka daurawa diya mace aure, (anan ina maganar yarinya budurwa mai auren fari) sai ta ji wani canjin yanayi yana dira a cikin ran ta, kai har ma da gangar jikin ta. Komin yawan son da take yi wa mijin nan kuwa.

Kasancewar shi auren wani nauyi ne mai girma na Ubangiji ya hau kan ta. Nauyin mijin da Allah ya sallada komai nasa a wuyan ta, wanda zai zamo abokin ragowar rayuwar ta ta gaba. La-shakka wannan din idan akka duba za’a ga cewa ba karamin nauyi bane, abubuwan da ke faruwa dani da zuciya ta a daidai wannan lokacin kenan;

Wato karbar sabon yanayin da ke shiga cikin jiki da zuciya ta a hankali, yana cukuikuiya ruhi na da wadancan abubuwan da na ambata a sama (fargaba da zullumi), masu tabbatar min na zama karkashin ikon mijin mafarki na yanzu, ba iyaye na ba, ba kuma Ya Omar dana gujewa aure helter-skelter ba.

Suna tabbatar min ne da cewa; daga rana irin ta yau na zama matar Hamzahn VOA!!! Hamzah Al-Mustapha. Ko ko in ce Hamzah Mawonmase!!! Sabon musulmin nan da ya dabaibaye zuciya ta ni Siyama ta ko’ina, ya hana ta salama da kwanciyar hankali tun daga shekarun kuruciya, balaga har zuwa girma na. Nauyin hakkokin rayuwar sa da jin dadin rayuwar sa bakidaya da walwalar sa, duka sun rataya a wuya na yanzu.

Wannan din kadai in aka duba ba karamin responsibility bane ga diya mace. Domin shine tushen farko kuma tubalin kafa rayuwar iyalin ta. Dole ta samu sauyi a zuciyar ta a wannan ranar.

Sai na shiga tambayar kai na da gaske ne ni din amarya ce yanzu? Ni, AISHATUL – SIYAMA MAMMAM GEMBU? Na zama matar aure? Matar kuma ba ta kowa ba ta Mr. Radio dina, ko kuma in ce “The Birom Man’s Bride”.

Mijin kuma ba kowa bane face Mijin nan na Mafarki na, mijin burika na; dan mutanen Birom haihuwar addinin ‘christianity’. Wanda a sanda na gamu da shi ban taba hango yiyuwar aure tsakani na da shi ba ta kowacce hanya. Ya tabbata a fili, ni Siyama ina cikin rukunin mutane masu sa’ar samun tabbatuwar mafarkan su zuwa ‘reality’.

Amma gashi na kasa yin farin ciki da hakan ko kankani, ko mai yasa???

Ni na san babbar damuwata ita ce kin amsar aure na da Abba ya yi. Ummati bata san an yi ba, duk da na san Young Abba yayi komai kan gaban kan sa ne sabida kaunar da yake yi mun, da burin sa na kasancewa ta cikin farin ciki na har abada da wanda na zaba nake kuma so. Ya gwammace su ya bata musu, don ni ya faranta min saboda maraici na, da kuma kaunar sa ga son ya ga ya ceci burika na da mafarkai na da kullum yake jin labari.

Amma kuma sai me? Sai gashi duk da wannan assurance din dana ke da shi, ban ji farin ciki ya mamaye ni irin wanda amare ke ji a ranar auren su ba. Musamman in suka yi katarin auren wanda suke mutuwar so ne iri na.

Maimakon hakan, tarin damuwa da kunci na babu gaira babu dalili ne suka taru suka danne zuciya ta, suka lullube tsagwaron farin cikin da ke saman ta wanda shi ya fi dacewa da ni, suka mai da shi damuwa tsantsa, zuciya ta da gangar jiki na suka yi wani irin sanyi lakwas. Kai ka ce ba DREAM HUSBAND dina Young Abba yasa kwanjin sa na kanin Uba ya aura min ba.

A irin wannan ranar wato (ranar daurin aure), duk karfin soyayyar da mace ke yi wa mijin, sau tari zaka samu ta ragu, wasu ma matsananciyar tsana take komawa, musamman in ta tuna raba ta zai yi da gidan su da iyayen ta baki daya.

To kusan hakan ce ta faru da ni nima, a wannan rana mai dimbin tarihi a cikin rayuwa ta data Hamzah, ranar da Young Abba ya damkamin sadaki na na aure, wato warawaran zinare guda uku da Hamzah ya bayar, ya bani su a hannu na ne matsayin sadaki na. Ya kuma tabbatar min (bayan dukkan kalubalen da suka faru) ‘against all odds, at long last’, yau na mallaki abinda zuciya ta da ruhi na ke so (na zama matar Hamzah karkashin igiyar aure na Musulunci). Hamzah Mawonmase dai, namiji daya cikin dubu a zuciya ta, ni Aishatul-Siyama. Wanda nayi ittifakin an halicce ni ne tare da kaunar sa tun ban san shi ba.

Na girma, na kuma rayu da soyayyar fantasies din sa tare da ni, na dade ina tafiya a kan siradi na buri da begen haduwa da shi, da begen tabbatuwar mafarkai na a kan sa.

Amma gashi yau dana same shi ban ji farin ciki ba. Ban yi murnar da ya kamata in yi ba. A zahiri ban tsane shi ba, kamar yadda wasu amaren ke tsanar mazajen su ranar daurin auren su, domin na tabbata nawa issue din is extraordinary dana kowa (da soyayyar sa ni a ka halicce ni, da ita na girma, cikin ta na rayu, cikin ta na budi ido). Amma duk da haka fama nake da matsananciyar fargaba, damuwa da rashin kwanciyar hankali idan na tuna reaction din Abba na nufin rashin amincewa da auren, in aka yi la’akari da irin karbar da yayi wa maganar aure na a lokacin da Young Abba ya sanar da shi.

<< Sakacin Waye? 34Sakacin Waye? 36 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.