Mr & Mrs Mawonmase
Hamzah ya kashe motar a kofar flat din sa. A jikin kofar shiga apartment din nasa, dan karamin karfe ne mai dauke da dan rubutu da ruwan gold manne da sunan sa “Hamzah Mustapha M.” da kuma nambar gida, kamar dai yadda ya ke a like jikin kofar kowanne ‘American Condo.’
Ko da ya kashe motar bai yi saurin fitowa ba, juyowa yayi ya dube ni, na hada kai da guiwa na rufe fuska cikin katon mayafi na, kuma har zuwa lokacin rabzar kuka nake ban gaji ba, ina jin shi yana safke ajiyar. . .