Skip to content
Part 37 of 73 in the Series Sakacin Waye? by Sumayyah Abdulkadir Takori

Mr & Mrs Mawonmase

Hamzah ya kashe motar a kofar flat din sa. A jikin kofar shiga apartment din nasa, dan karamin karfe ne mai dauke da dan rubutu da ruwan gold manne da sunan sa “Hamzah Mustapha M.” da kuma nambar gida, kamar dai yadda ya ke a like jikin kofar kowanne ‘American Condo.’

Ko da ya kashe motar bai yi saurin fitowa ba, juyowa yayi ya dube ni, na hada kai da guiwa na rufe fuska cikin katon mayafi na, kuma har zuwa lokacin rabzar kuka nake ban gaji ba, ina jin shi yana safke ajiyar zuciya a hankali.

Irin ajiyar zuciyar da Hamzah ke yi a jejjere sai kayi tsammanin kamar a kasa muka tako muka taho tun daga gidan Young Abba.

Watakila kuma nauyin da ya sha ne na dauko ni a kafadunsa tun daga falon Young Abba zuwa cikin mota? Shi ya sanya shi wannan ajiyar zuciyar? Ko kuwa gajiyar tuki ne ko na godiya ga Allah oho? Hamzah Mawonmase, shi kadai ya barma kan sa sani.

Hamzah ya san a yanayin da na ke ciki yanzu bana kallon sa, amma tabbas ya san ina jin sa, duk da irin kukan fitar ran da nake yi ba zan kasa jin sa ba. Sai ya tausasa murya, ya sirantata hadi da kalmasa ta ta koma ta rarrashi, at the same time, ya kaurara ta cikin siga ta bada umarni. A hankali ya ce.

“Ba zan hana ki kuka ba Habeebty, domin kin cancanci ki yi shi yau kadai, na sabo da kewar gida, amma don Allah na roke ki alfarma, iyakacin sa cikin motar nan (kukan). Ki yi ki gama yadda ran ki ya ke so, ki yi kukan barin gida ki more, amma ki ajiye shi cikin motar nan sannan mu fita”. Ba kuma tare da ya jira cewa ta ba ya ci gaba da tausasa murya wajen cigaba da fadin;

“Welcome to your humble abode, My Damsel S. (ZINARIYA ta, Siyam), I wish you a joyous and happy married life. Taimaka min ki daina wannan kukan haka, domin yau ranar farin cikin mu ce, ni HAMZAH da mai dakina… SIYAMA, ki sa a ran ki yau muka zo duniya dukkannin mu, rayuwar mu ta baya ta wuce kamar ba’ayi ta ba. Da yardar Ubangiji yau zamu fara rayuwar aure mai cike da soyayya, kurakuran mu na baya an ce duk daga ranar yau sun rikide sun koma aikin lada. Ina rokon Allah ya yi mana gafara, ya raba mana wannan ladan ni da ke da su Young Abba.

Ina addu’ar Allah ya bani tsahon rai da dogon numfashi, wanda zai ishe ni in rikewa Abban mu amanar da ya bani. Ina rokon Ubangiji yasa kada in bashi kunya. Yasa kada in zama butulu (mai rama khairan da sharran). Ya sa in zamo mai saka khairan da mafi kyawun khairan.

Amma hakan ba zai yiwu ba sai da hadin kan ki Siyam, sai naga farin ciki ko yaya a kan kyakkyawar fuskar ki zan samu nutsuwa. Wannan kukan da kike yi sai yake birkita ni, yake yi min kama da kina nadamar aure na ne!

Na gane Siyam ba kiyi farin ciki da auren mu ba yanzu, kamar yadda ni nake yi, nake kuma kan yi, su Young Abba ma suke yi. Ko da yake ma kin fada da bakin ki a gaba na cewa kin fasa gabadaya”.
Hamzah yayi maganar cikin tarin damuwar da ta nuna kan ta a muryar sa, mai nuna yadda maganar dana yi din dazu ya taba zuciyar shi sosai. Soyayyar dake dankare a ran sa ta nuna kanta baro-baro cikin ‘almond shaped’ idanun sa wadanda ke kyalli kamar hawaye ya kwanta a cikin su.Zuciyar Hamzah na wani irin hankoro a cikin kirjin sa, tana bugawa da sauri kamar zata fito ta bakin sa, da zai iya da ya hadiye Siyam ya huta. Daga wannan azababben SO da yaji yana kara samun muhalli a zuciyar sa, yana sake rubanya kan sa a yau.

In ya tuna Siyam ce yau a gidan sa, zasu kwana su kuma tashi tare ne gida daya, zasu wayi gari ne a kan gado guda, alhalin tana matsayin matar sa ta halal kuma mallakin sa daga yanzu har zuwa wa’adin rayuwar da Allah ya debar masa, sai ya ji zuciyar ta kara karfin bugun da take yi da wani irin excitement. Babu wani farin ciki a rayuwar duniya da ya wuce masa wannan yanzu. Ban daina kuka ba, shi kuma bai bar roko na a kan in daina din ba yanzu-yanzu kafin mu bar cikin motar nan. Cikin dabara ya san yadda ya yi ya hada tafin hannun sa da nawa. Ya yi crossing yatsun hannun mu cikin na juna. Sannan yayi pressing hannun nawa da kyau cikin nasa. Sai na ji wata irin nutsuwa ta saukar min amma hakan bai sa na daina kukan ba.

Da dai ya ga har zuwa lokacin bani da niyyar dainawa kuma duk lallashin sa ya fara karewa, muryar sa kanta rawa take yi, sai yayi shiru, ya kwantar da kansa a kan sitiyari, fararen idanun sa sun kada sun yi jazir da damuwa, ba tare da ya raba yatsun mu ba, suna sarke cikin junan su. Mun fi karfi mintuna sha biyar a haka, kafin Hamzah ya gaji, yace.

“For Allah’s sake Siyam, ina kikeso in saka raina? Da wace damuwa kika fi so in ji? Da damuwar da na ke dauke da ita a rai na ta Kaka ta kike so in ji, wadda ke kwance asibiti rai a hannun Allah, cikin ciwon hawan jinin da a cewar ta ni na sanya mata shi, ko kuwa da farin cikin da nake ciki as well, mai neman fasa zuciya ta wanda kike son rikida min shi zuwa bacin rai? This is not the kind of welcome I deserve (ban cancanci wannan tarbar ba), a dai rana irin wannan mai dumbin tarihi da matukar muhimmanci a gare ni, rana ta farko da auren mu.

Ko kin san tsayin lokacin da na dauka ina jiran zuwan wannan ranar, da irin muhimmin tanadin dana yi mata?”

Sai na samu kaina da ciro fuska ta a hankali daga cikin cinyoyi na, na kuma rage sautin kuka na, amma duk da haka ban yarda na bude lullubin kai na ba. Maganganun sa da tone din da yayi amfani da shi wajen furta su, shi ya sanyaya zuciya ta, at the same time, (a lokaci guda) suka taru suka jefa min tausayin sa, maraicin sa ya fito tsantsa muraran a cikin sautin sa, da na tuna kuma bashi da kowa sai Kakar tasa…

Ganin yayi galaba na dago kai na, sai ya samu kwarin guiwar cewa, “can I unveil it? I mean wannan katon mayafin? And see your beautiful, alluring and charming face wadda a kullum nake mararin ganin ta?”

Hamzah ya tambaya da murya mafi taushin amo da ya mallaka daga can kasan makogaron sa, sounding romantic, loving, caring and concerned to his wife. Sake dukunkune fuskar tawa nayi cikin katon mayafin kunya ta lullebe ni, sai kawai ya fito daga motar ya zagayo bangaren dana ke ya bude min kofar, yana sake fadin,

“Welcome to your humble abode! My Damsel S. ZINARIYA TA! My own darling, Siyam, my wife-my life, Azumi-Boddon Young Abba da Anti Nasara kuma kanwar Ya Omar, uwargidan Hamzah Mawonmase, mother of my incoming children, the one I truly cherished and love most! Marhaban to your humble abode.”

A hankali na zuro kafafu na kasa, kai na ya yi girma da wannan kirari na Hamzah, watakila don kirarin ya fito ne daga bakin dana fi so akan na kowa ba don wai yafi kowa iya kirari ba. Na kasa tankwabe wannan girmamawa, kambamawa, martabawa, darajjawa, da kulawar tasa, kafin a hankali in fito da gangar jiki na duka daga cikin motor.

Ina jin shi yana fadin “na fi so ki taka ki shiga gidan ki da kafafun ki cikin aminci, mu roki Allah dukkan alkhairin da ke cikin sa, mu kuma nemi tsari daga sharrin shaidanu da abin kin da ke cikin sa.”

Hamzah in yana abubuwan sa ni yanzu har ya daina bani mamaki, kamar wanda aka haifa ya kuma tashi ya girma cikin Musulunci. Komai sai ya saka Allah ko da yake suma sun san akwai Allah. Sun dai yi masa kishiyoyi ne. Hannun sa ya saka cikin nawa, muka soma takawa a hankali zuwa kofar shiga apartment din anda ke cikin rukunin gidajen ‘Ceilo Apartments’ na tsakiyar birnin Washington D.C.

Gidan Hamza Mawonmase

Matukar kyau da tsaruwa na daidai misali to gidan Hamzah Mawonmase ne. Mukulli yasa ya bude falon, da bisimillah na saka kafafu na cikin gidan, a zuciya ta kuma addu’ar duk da ta zo baki na nake karantawa, shi yake yi min jagora ban san ina nake saka kafafu na ba kasancewar nabi na rufe fuska cikin katon mayafi na.

Ban san ya aka yi aka iso dakin ba naji dai ya kawo ni bakin gado ya zaunar dani kan wata lallausar water mattress. Sannan ya durkusa a gaba na ya yi unveiling lullubin dake kai na.

A lokacin ne muka hada ido, ni da Hamzah, kafin na maida idanu na kasa a hankali cikin jin matsananciyar kunya, ban iya na yi masa kallo na biyu ba, sakamakon abinda na hango cikin idanun sa masu kama da zagayayyen dan itacen almond mai girma da nauyi ne da ya shallake karfin idanu na, almond shaped eyes din sa wadanda ke walainiya kamar cikin maiko-maiko, hawaye-hawaye dauke suke da manya-manyan sakonni. Kamar ya fahimci gudun haduwar kwayan idanun mu nake yi sai yace “Siyam, dube ni cikin ido mana. Ki gaya min how you felt this day, ko kuwa kin daina so na ne kike wannan koke-koken da suka wuce kima wadanda sun soma sike ni. Ko kuwa soyayyar ta rikide zuwa tsana ta wucin gadi daga lokacin da aka daura mana aure?”

Ban yi mamakin yadda yayi saurin karantar halin da zuciya ta ke ciki a kan sa yanzu ba, in aka yi la’akari da cewa shi din kwararren dan jarida ne na jiya ba na yau ba.

A hankali na cira kai na dube shi da jikakkun idanu na, na fahimci baya son nuna cewa kuka na weakens him, amma da gaske kukan nawa ya raunata shi to an extent, ya rage masa dokin da yake ciki, idanun sa sun nuna hakan, wato sun nuna karayar sa a zahiri; kukan nawa yana neman sagar masa da gwuiwa ya rage masa kuzari da doki. Gane hakan da na yi sai na shiga share hawaye na da dukkan tafukana da sauri da sauri ina nufin na daina kukan. Tafukan hannayen sa masu taushi ya saka a cikin nawa, ya hade su cikin nasa, ya dunkule su wuri guda ya matse su sosai, yayi crossing fingers din sa cikin nawa cikin samun relief na samun shawo kaina na daina kuka.

Kafin ya mike ya kuma mikar da ni tsaye, sannan sannu a hankali cikin nutsuwa irin tasa ya shiga sauke lullubin kai na har ya sauke shi kasa baki daya, mayafin ya fadi saman kafafu na a kan ‘marbles’, bakin kwantaccen gashin da bai taba gani ba, bai kuma san inada shi ba na fulben Mambilla shi ya fara bayyana gare shi, kyallin sa ya haske idanun sa, santsin sa ya wadaci idon sa, wanda ko da wasa bai taba sanin haka yake wajen tsayi, sulbi da baki ba.

Da wata irin azama Hamzah ya cusa fuskar sa cikin gashin nawa, ya saka hannayen sa ya tallafo wuya na ya shige cikin jiki na da azama da rawar jikin da ya wuce kima, tamkar yaron da ya sha kuka har ya shide, kafin a karshe ya samu jikin mahaifiyar sa da ya dade yana nema, ilahirin jikin sa kyarma yake yi, sannan da hanzari yake sanya ni cikin jikin sa tamkar yana tsoron wani abu zai zo ya kwace masa Siyam din, ya kanainaye ni bakidaya ya shige cikin jiki na ta ko’ina, yana mai cigaba da cusa fuskar sa da sassalkan sajen sa mai taushi ta kasan wuya na, gashin kaina ya rufe fuskar sa bakidaya har baka hango fuskar Mr. Hamzah, taushi da santsin sajen gefen fuskar shi ya sauka a masangalin wuya na, wanda ke ta tashin kamshin man gyaran gashi na musamman da mazan zamani ke amfani da shi wato  (Arganavita), wanda hakan yayi sanadin tada tsigogin jiki na baki dayan su.

Duk inda hannun sa ya sauka a fatar jiki na sai naji tabin nan har cikin bargo na. Ji nake tamkar Hamzah na ja na da lantarki, kafin a yi haka na ji saukar tausasan labban Hamzah a dogon wuya na, ya soma wani irin soft kiss, a yangace (in a gentle manner) cikin madaukakiyar iyawa, inda duk ya sumbata sai na ji dirin saukar sumbar a jiki na tun daga kwakwalwata har zuwa yatsar kafata, daga baya ya koma yi a urunce, wani irin hadamammen kiss, mai nuna tsahon wahalar jiran da ya dade yana yi wa zuwan wannan ranar.

Daga sannan ya koma yin kiss mai wahala, wata irin wahalalliyar “sumba” Hamzah Mawonmase yake sauke min a wuya na wadda zaka fahimci ‘motive’ din ta na tasowa ne tun daga karkashin zuciyar sa a kan kowacce kusurwa ta fuska ta zuwa kasan masangalin dogon wuya na, wata launin sumba ce mai bada sauti Hamzah Mawonmase yake min, mai tsayi kuma mai zurfi, (hungrily, deeper and hot) mai tsayawa a zuciyar mace, musamman idan ta fito daga bakin mijin da take tsananin so ne, ta kasa manta tasirinta da sauki.

A kasan wuya na kadai Hamzah ke sha’anin sa, tamkar ba zai daina ba. Ya shiga nan da fuskar sa da bakin sa, ya fita can ya koma can. Ya rasa inda zai tsoma emotions din sa domin sun fi karfin control din sa. Dogon wuyan Siyam da ya dade yana bashi sha’awar ya sumbata ya ji irin taushi da sulbin sa kullum daga nesa-nesa in ya dube ta ta juya, shi ya samu yau, don haka yake neman cinyewa ta ko’ina, ya rasa inda zai sa kansa, ko inda zai sa Siyaman, yana yi yana tsarkake mahaliccin ta a fili da zuciyar sa, domin hakika ya kyautata halittar ta kwarai da gaske fiye da yadda ya ke gani daga nesa.

Daga wuyan nawa ya rika moving upward zuwa sama a hankali har ya dangana da baki na. A nan ne naga abin mamaki daga dan mutanen Birom. Koko in ce daga “Berom Man” din da babu kamar sa a duniya ta da ta  mafarkai na.

Wato wani launin soft mouth to mouth kiss, da Hamzah ke yi a cikin baki na, tamkar zai raba ni da halshe na bakidaya daga irin tsotson kaunar da yake yi masa passionately. Gabadaya ya gigice ya fita a hayyacin sa cikin dan lokaci kalilan, irin gigicewar da ban san maza na yi a kan matan su ba. Mazarin da jikin sa ke yi, da irin kakkarfan rikon da yayi mun kadai, sun tabbatar min yau mai kwata na a hannun Mr. Hamzah sai Allah da ya halicce shi ya kuma halatta masa Siyama……

Amma na kasa taya shi da komai. Ba don bana enjoying madaukakin romancing da yake yi mun ba (wanda na sha ganin kwatankwacin irin ta cikin mafarkai na) sai don wannan ne karo na farko da irin haka ta faru da ni a zahiri, tsakanina da da namiji, so as a first timer tsoron da ke cikin al’amarin yafi jin dadin da e cikin sa yawa.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Sakacin Waye? 36Sakacin Waye? 38 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×