Skip to content
Part 36 of 73 in the Series Sakacin Waye? by Sumayyah Abdulkadir (Takori)

A can wani dan kankanin sako, ko in ce wani dan lungu na zuciyar kuma, bidirin farin ciki ne ke gudana irin na cikar buri, ga kuma alhini da taraddadin Abba. Wato akwai wani guilty conscience din yin aure ba da yawun Abba Na ba a tattare da ni, ba da cikakkiyar yarda da sanya albarkar sa da kuma cikakken iznin sa ba. Na tabbata abinda ya hana farin cikin nawa cika kenan.

Don haka in ka ganni a wannan lokacin sai ka rasa gane a halin da na ke ciki. Na yi tagumi kawai na rasa abunda ke min dadi. Irin rafkeken tagumin da na rafka a gefen gado na na gidan Young Abba, kai in ka ganni a sannan sai nayi maka kama da mai tsohuwar takaba.

A haka Aunty Nasara ta shigo daki na ta same ni bayan sun gama fafatawar su da Young Abba a kan maganar biki, tana ta mita kamar ta ari baki, (daman dai na dade da sanin Nasara ba dai mita ba), balle a ce ta samu dalilin yin ta. Fadi take tun daga bakin kofa “ni na taba ganin mutun dan gaggawa irin Baban ki?”

Ta karasa shigowa dakin ta na cigaba da cewa.

“Sai ki tashi haka daga tagumin nan, wanda ba abinda zai sa ba abinda zai hana. Domin kuwa Baban ki Adamu Sarkin gaggawar Gembu baki daya, shugaban rigimammun birnin Washington D.C, ya ce yau zaki tare ba daga kafa, kafar ki kafar Hamzah, kuma kada in kai ki da komai, a cewar sa already Hamzah na hanya ma, ya taho daukar ki, yanzu zai zo ku tafi”.

Nasara ta dan nisa cikin damuwa, kafin ta zauna a gefe na ta kama hannaye na ta rike su cikin nata. Da sanyin murya ta cigaba da magana.

“Gashi kuma Siyama ban shirya miki komai ba, domin komai ya zo mana bagatatan ba shiri, sannan a kurace (a kurarren lokaci). Na so ya bari in shirya ki ko na sati daya ne.  Amma Baban naki wani irin sha-yanzu ne magani-yanzu, bana son halin nan nasa na gaggawa amma ya zan yi? Tunda shi ke iko da mu dukkanmu, ba mu ke iko da shi ba?!

Siyama a yau zamu kai ki gidan miji, ta kowanne fanni bani da haufi kan tarbiyyar da muka yi maki, ko in ce, Ummati da Wasila suka yi miki muka dora daga inda suka tsaya.

Amma na hore ki da hakuri, shikadai zan miki guzurin sa, idan na ce hakuri ina nufin hakuri da halin miji, shi hakurin nan da kike ji ana fada ana kara jaddadawa a cikin aure dole ne. Ki bar ganin kina son sa yana son ki kamar ku hadiye juna, kiyi tunanin shikenan baku da sauran matsala a gaban ku sai soyayya, wallahi zaman aure ya wuce tunanin ki. Dole watarana a sha Zuma…, watarana a sha Madaci.

Tunda zaman abu ne na din-din-din (abu ne da bashi da karshe, kuma ibada ne. Tunda ibada ne kuwa fata a ke a dawwama cikin sa har abada. Cikin kowacce ibada kuwa sai an saka juriya, yakanah da hakuri Siyama.

Ina cewa kiyi hakuri ne sabida watarana zaki ga abinda bakya so a auren Hamzah, ba kuma fata nake yi ba, a’ah reality ne na rayuwa yau da dadi gobe babu, ko ba dade ko bajima sai an samu sabani, ba don yana tubabbe ba a’ah, ko wadanda aka haifa cikin musulunci suna kuskurewa matan su, matan ma na kuskure musu, bar ganin yawan son da kike masa ko yake miki, ki dauka baza ku taba batawa juna rai ba; no body is perfect, shi kalubale a rayuwar aure wani abu ne inevitable (wanda ba makawar sa).

Abin bukata shine ayi wa juna uzuri da karfin soyayyar dake a tsakani.

Ki kula da girki, tunda kin ga yana son abincin gargajiyar su sosai. Musamman na tashi al’adar (Gwaten Acca, kunun Acca, tuwon Acca). To ki zage ki koya ko a yanar gizo ne. Ki dauki kan ki ‘yar kabilar Birom yanzu, addinin ku ne kawai ba daya ba.

Ki kuma cigaba da nuna masa komai na addini bi da bi, kada ki gaza, kada ki kosa, tunda ke din Alhamdulillahi Malama ce mai zaman kanta, kada ki yi kasa a gwiwa kada ki yi fushi idan ya yi wani abin haushin, kada ki sare idan bai dauka da wuri ba, kada ki yi kasa a gwiwa wajen fada masa ALLAH na kallon sa, sai a hankali zai iya mastering komai.

Yanzu Hamzah shi da jaririn da aka haifa ake raino ta fuskar addini basu da maraba, don haka sai kin mike tsaye kin jajirce wajen ganin kin yi amfani da ilmin addinin da Allah Ya baki wajen koyar da shi. Ki fara koya masa karatun Al’qur’ani tun daga Nasi har Baqarah.

Ba wata makaranta da zai shiga da zata fi taki muhimmanci da kusanci gare shi a yanzu, tunda kullum kuna tare a gida daya kuma a gado daya. Wannan nauyin yana kan ki ba wanda zai jure shi sai ke. A zaune kuke, a tsaye kuke ko a kwance yi ta koya masa karatun Alqur’ani koda aya dai-dai ne a rana.

Ta fannin tsaftar jiki bana jin ki Siyama. Na sallama miki. Allah ya baku zaman lafiya da zuri’a mai albarka ku zo ku cika mana gidannan da jikoki mu yi ta bari-bari”.

Sai naji zuciyata bakidaya ta karye, dama kuma a mace take murus, idan na tuna cewa ranar rabuwa ta da Aunty Nasara ne ya zo sai ta idasa kakkaryewa da wani irin kekkecewa, shin da gaske ne? Ko kuwa dai mafarki nake yi tunda ni din dama ma’abociyar mafarke-mafarke kala-kala ce?

Da gaske yau zan bar gidan Young Abba zuwa gidan Hamzah Mawonmase, amma gashi bana farin ciki as expected? Da gaske na bar Aunty Nasara da Baba na makwafin Uba wato Young Abba Adamu kenan, ni da su sai dai in gan su da yawo? Da gake auren na nufin. Zan je ne in zauna daga ni sai Hamzah a cikin gidan sa, babu giftawar kowa a tsakanin mu sai halayen mu ga juna, daga yau har zuwa karshen rayuwar mu?

Wannan tunanin kadai ya tsinka zuciya ta, at the same time, ya tada hankali na, na shiga kuka riris, kamar an yi min mutuwa, kaina bisa kafadar Anti na, kuka nake wiwii, babu ji babu gani, ina gayawa Auntyna na fasa auren Hamzah gabadaya. Na daina son Hamzahn kwata-kwata ma tunda haka ne, gida Najeriya zan koma wajen su Ummati.

Aunty Nasara ta rungume ni a jikin ta tana girgizani a hankali cikin lallashi, amma ita din ma she cannot control her tears. Wani irin zama ne na amana da kaunar juna hadi da fahimtar juna muka yi ni da ita, tsayin shekaru kusan shidda bamu taba samun sabanin da muka kasa fahimtar juna a kan sa ba.

(Madallah da matan Uba na kwarai irin Nasara da Wasilah, madallah da duk mata nagari masu hali irin nasu na taimakawa mazajen su da zuciya daya wajen aikin zumunci, irin wanda shi kadai zai iya kai su aljannah. Allah Ya kara amincin su a zuciyar mazajen su).

Sai jin gyaran muryar Young Abba muka yi a kan mu, ashe har ya je inda zashi ya dawo tare da Hamzah. Ya shigo dakin da sauri jin tashin sautin kukan mu kamar an mana gagarumar mutuwa, bamu ankara da shigowar shi ba sai jin fadan sa muka yi blah blah blah…. A kan mu.

“Yau nake ganin sakarci mai license!”, In ji Young Abba, yana kallon mu cikin mamaki “wannan wace irin sullutuwar Uwa ce?

Ke da zaki karfafe ta ki bata misalai na cewa mace ‘yar gidan wani ce, a’ah, sai ki kamata kuna kukan sakarci kamar wasu aringizon kananan yara? Siyamar ba mace bace? Kuma kowacce mace ba gidan aure take tafiya ba? Ke a gaban iyayen ki kike yanzu? Cewa nake aure ne ya tsallako da ke har wata kasa da ba taki ba?”

Sai kuma ya tausasa murya ganin dukkan mu mun baiwa banza ajiyar sa.

“Balle ita da muna nan kusa da juna Nasara? koyaushe kike son ganinta zaki gan ta, na yi alkawarin kai ki gidan ta duk sanda kike so ko dare ko safiya”.

Aunty ta dago ni daga jikin ta tana share min hawayen da ke zuba kamar an sunce famfo da tafukan hannayen ta, sannan ta ja hannu na zuwa toilet ba tareda ta tanka masa ba, don ba karamin haushi yake bata ba yadda yake rawar kafa a kan Hamzah kamar uwar su daya uban su daya ni din ce bare, ruwan wanka mai zafi ta hada mun, ta zuba turaren wanka na ‘OUD ISPAHAN (Christian Dior) a cikin sa, ta ajiye min komai a gefe har tawul tace in yi wankana da kyau, har da cewa “irin wanda ban taba yi ba”, in na gama in fito tana  jira na.

Kafin na fito daga wankan Anti ta ajiye min sababbin kayan data tanadar min musamman don wannan ranar. Wata doguwar riga ce dark blue data sha adon jajayen stones daga sama har kasa kirar Bahrain, ta taimaka min na saka sababbin fararen undies daga ciki, sannan ta saka min rigar, sai walwali take zubawa sabida duwarwatsun dake jikin ta, sabida yadda hawaye yayi wa fuskar kaca-kaca bata samu damar yi min kwalliya a fuska ba, sai turarukan ta na amfanin ta data debo daga dakin ta (kan mudubin ta) ta feshe ni dasu har kala uku.

Ko kafin mu gama Young Abba ya shigo ya kai sau biyu yana tambaya?

“Kun gama ko har yanzu? Shanyar taku ta bushe, ku zo ku debe ta haka. Hamzah is here already, tun dazu”.

Aunty Nasara tace “ai gara ka nuna masa ka gaji da ‘yar taka, neman kai kake yi da ita”.

Dariya ya yi, sannan ya ce “of course, na gaji da ita wallahi, in na gan ku kun kwaso tsahon kunnan, kun hada kafada dinnan kuna kus-kus, gabana faduwa yake, in rasa wacce ce mata ta, Allah ne ya so ni fara da baka ne, ke ce baki sani ba burin kowanne uba shine ya ga dan sa cikin sutturar aure ba a yawon titunan Jami’a ba”.

Aunty ta kamo hannu na bayan ta lullube ni ruf da babban mayafi dark blue, ta tufke min gashin kaina ta feshe shi da turaren gashi, muka fito falon farko, wanda daga shi sai kofar fita gidan. A nan Young Abba ya sauki Hamzah.

Hamzah na zaune a kujerar zaman mutum uku a falon Young Abba, ya saka fuskar sa cikin tafukan sa, cikin dokin jira, bai taba ganin nisan jira kamar na yau ba. Zuciyar sa tayi sanyi kamar kankara, ran sa ya yi fari kamar madara, wata irin nutsuwa ya samu kan sa a ciki wadda tun haduwar sa da Siyam bai kara samun ta ba sai yau, da yake da tabbacin ta zama mallakin sa ta hanyar da Allah ya tsara ya kuma halatta masa. Ran sa fari kal. Jin sa yake kamar yana yawo a kan gajimare a wadannan ‘yan dakikan da yake zaune yana jiran fitowar Siyama, farin cikin da yake dankare cikin ran nasa shi kan sa bai san adadin sa ba, saboda bai taba tsintar kan sa a kwatankwacin sa ba, a dai kafatanin tarihin rayuwar sa.

Ko da muka shigo falon mikewa tsaye yayi (to show respect ga Young Abba da Maidakin sa), da ‘yar sassarfa ya tako ya isko mu, wato ya tarbe mu a tsakiyar falon muka yi gaba da gaba. Ya kasa hakurin tsayuwar jiran mu shigo ciki mu zauna shiyasa ya mike ya riske mu a tsakiyar dakin. Young Abba na ganin haka sai ya yi maza ya kama hannu na ya kamo nasa ya saka ciki ya dunkule su. Yana fadin “for now, kuna iya tafiya Mr. Hamzah, Allah ya kade fitina ya bada zaman lfiya. Ku tafi yanzu, dare ya riga ya kawo jiki.

Na baka amanar Siyama Hamzah, ka rike min ita amana kamar yadda take amanar mahaifin ta a hannu na, idan ka cutar da ita Allah ba zai barka ba. Nima kuma ba zan yafe maka ba domin ita din abar so ce da kauna a gare ni.

Kada kuma ki ji na fadi haka ki dauka ke in kika cutar da shi ta kowanne fanni Allah zai bar ki Siyama, Hamzah is a nice person, a very jovial person, ni shaida ne bashi da rigima bashi da taurin kai irin naki Boddo, don haka ni na san ta fannin sa da wuya a samu sabani, dukkan ku amanar juna ne ga junan ku, ku rike juna fi-amanallah, kusa a ran ku baku da kowa sai junan ku, duk da kasancewar kuna da mu, kuna da iyaye.

Ku wuce ku tafi. Allah yayi wa rayuwar ku albarka ya baku zuri’a dayyiban salihan”.

Sabon kuka na kama har da sheshsheka ganin da gaske ne tafiya zamu yin, ina kokarin zare hannu na daga cikin na Hamzah amma ya rike sosai, ya ki bani damar hakan, cikin rishin kuka na soma fadin.

“Young Abba haka zaka bar ni in tafi gidan miji ni kadai bazaku raka ni ba sai kace wata mara gata?”

Young Abba yayi murmushi ya ce “hakan koyi da sunnah ne, miji ya zo ya dauki matar sa da kan sa zuwa gidan sa”.

“Young Abba ni dai ban shirya ba, a kara min lokaci in kintsa a hankali don Allah mana, in ba haka ba …. Ni gaskiya….  na fasa auren wallahi!”.

(A cikin ran Adamu cewa ya yi “kaji mun al- muna fun -fun, munafukar yarinya, kamar da gaske zata iya fasawar). Amma sabida Hamzah dake tsaye yayi shiru bai fada a fili ba, sai wata uwar harara da ya zabga mini irin ta “kada ki raina min hankali”. Daga Young Abba har Anti basu ankara ba sai gani suka yi Hamzah ya ja ni jikin sa da azama ya rungume ni tsam-tsam, ji yayi kamar Siyam ta diga masa wutar dalma a ran sa da kirjin sa, da ta ce wai Young Abba ya kara mata lokaci kafin tarewar ta gidan sa, ko ta fasa auren nasa, watakila ya manta a gaban iyaye na muke.

Daga haka kuma, ban gama fita daga wannan kunyar ba (ta rungumar bazatan da yayi mun) na ji ya sure ni a kan kafadun sa kamar ya dauki yaron da bashi da nauyi. A ran sa yana mamakin rashin nauyi irin na Boddo, kamar bata cin abinci mai gina jiki. Bafulatanar asali, ‘yar shafal, mai lange-langen jikin fulanin Mambillah. Hamzah ya ce.

“In kin fasa ni ban fasa ba Siyam, har abada kuma ba zan fasa ba, yanzu muka fara rayuwa tare cikin yardar Ubangiji daga nan har shekaru dari masu zuwa a gaba idan Allah ya tsawaita rayuwar mu.

Wane irin gata kike tunanin Abba zai miki, bayan wanda ya yi miki/yayi mana Siyam?

Ya yi mana komai a rayuwa tunda ya mallaka mana juna ta hanyar aure, ya taimaka min na tsira daga azabar wuta na fita daga sahun kafirtattu.

Kisa a ran ki baki da gatan da ya fi ni yanzu. Kuma alkawuran da na daukar miki kitaya ni addu’a Allah ya ban ikon cika su. Ni ne makwafin Young Abba gare ki a yanzu.

Daga yau Young Abba ya gama role din sa na Uba a gare ki, ya yi duk abinda ya dace ya yi miki kuma, tunda ya aurar da ke ga hannun da yake da tabbacin ko bayan ran sa ba zai yi nadama ba, so ba sai ya raka mu ba. In sha Allahu zan kula da ke.”

(Hamzah ya iya kalmar In sha Allahu tun ma kafin ya musulunta a bakin babban abokin sa Muhyiddeen Tokumbo, wanda cikakken musulmi ne mai yawan ratsa kalmar a cikin duk maganar da zai yi, tun a wancan lokacin ya yi adopting din ta ta zauna a bakin sa).

Aunty ta matsa a hankali da lalube ta kama mijin ta tana boye ido, ganin Hamzah ya dauki Siyama, ta rufe ido a kan kirjin Abba tana fadin “boye ni Baban Ahyan, Hamzah ya manta surakuwar sa ce ni!”

Tuni Hamzah har ya kai kofa a lokacin, ya fice da Siyama dauke a hannun sa, wadda kunya ta hana ni ko da motsin kirki na kwanta lum! A cikin kirjin sa.

<< Sakacin Waye? 35Sakacin Waye? 37 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.