Ni na san na so Hamzah Mawonmase mafificin SO, na so komai nasa, na yi burin kasancewar mu miji da mata a darare da dama da yawan su ba zai lissafu ba, kuma na sha yin mafarkai barkatai kwatankwacin irin wadannan masu kama da ido biyu, amma na yau special ne, wato (na musamman ne) yayi matukar bambanta dana cikin mafarkai na, kasancewar na yau a zahiri yake gudana, wato zallar reality ne mai sarrafa kan sa da kan sa….yake kuma tafiya (hand in hand) da karfin soyayyar da ke
zuciyar Hamzah…
Na ji ni tamkar ina shawagi a. . .