Sai ya koma babban falo, ya kwanta bisa doguwar kujerar falon, yayi filo da dogayen hannayen sa masu yawan gargasa. A hankali ya lumshe idanun sa yana tuno abubuwan da suka faru daren jiya, wadanda bazasu taba shafewa daga cikin darare mafi muhimmanci a rayuwar shi ba.
It was like ya je aljannah ta bakwai ya dandana ni’imar cikin ta, ya dawo duniya.
Wani abun da ya bashi mamaki sai ya ji ba abinda yake son sha a wannan lokacin sai BARASA, kamar yadda yake a al’adar sa ta baya, yana shan ta ne a lokutan farin ciki. . .