Skip to content
Part 39 of 73 in the Series Sakacin Waye? by Sumayyah Abdulkadir (Takori)

Sai ya koma babban falo, ya kwanta bisa doguwar kujerar falon, yayi filo da dogayen hannayen sa masu yawan gargasa. A hankali ya lumshe idanun sa yana tuno abubuwan da suka faru daren jiya, wadanda bazasu taba shafewa daga cikin darare mafi muhimmanci a rayuwar shi ba.

It was like ya je aljannah ta bakwai ya dandana ni’imar cikin ta, ya dawo duniya.

Wani abun da ya bashi mamaki sai ya ji ba abinda yake son sha a wannan lokacin sai BARASA, kamar yadda yake a al’adar sa ta baya, yana shan ta ne a lokutan farin ciki dana bacin rai, abinda ya dade bai sha ta ba, ya manta yaushe rabon sa da ita, mai yuwuwa tun fara neman sa da Siyama da Young Abba ya gargade shi a kan haramcin shan ta cikin addinin da ya karba da hannu bibbiyu. A yanzun kuma he’s overwhelmed with happiness and excitement, yana neman abinda zai rage masa excitement din sa.  Kada son Siyam da farin cikin data haddasa masa daren jiya su taru su kassara shi.  

An ce wani excitement in yayi yawa zai iya yin lahani ga zuciya da kwakwalwa. He needs something that will cool it, reduce it and if possible, giyar da ya jima bai sha ba.

Dama shi din ya kan sha barasa ne a lokuta guda biyu; lokacin bacin rai ko na tsananin farin ciki, ko kuma lokutan da kadaici ko damuwar rashin iyali suka taru suka yi masa yawa, yake neman abinda zai dauke masa damuwar su.

Amma Young Abba ya gaya masa as a devoted Moslem yanzu dole ya bar barasa, a matsayin sa na musulmi na hakika, wanda yayi alkawarin bin duk wasu ka’idoji na addinin musulunci, in har ya san yana shan ta. Kuma ya san haka tunma kafin ya san Siyama.

A lokacin da Young Abba ya fada masa giya haramun ce (in Islam) yayi masa alkawarin bari da zuciya daya. Knowing that, barin shine kadai abinda zai bashi Siyama. Kuma tun ranar da ya hana shi din ya bari. Rabon sa da shan barasa, tun ranar da ya ga Siyam gani na farko.

Amma wani abun mamaki yanzu ji yake a ran sa in bai sha ba ‘excitement’ zai kashe shi ko ya fasa masa zuciya, farin cikin da yake ciki is beyond control din sa, idan son samu ne yana son yayi moderating din sa da barasar. In ba haka ba jinin sa zai iya hawa da excitement din.

Ya dade da ajiyewa ran sa alkawarin tarawa da matar duk da ya aura a rana ta farko na auren su babu jinkirtawa saboda yadda ya kame kansa daga dattin zina. Ya yi wa ranar tanadi mai yawan gaske. Bai ma san al’amarin haka yake ba sai yau da ya kusanci matar sa da yake matukar so wadda Allah ya bashi cikin kaddarar sa wato Siyama…. yayi making love mai tsafta kuma dan asali da ita wanda ya zauna ya kasa barin ran sa, komai ya faru yadda ya dade da tsarawa da son kasancewar sa, har fiye da yadda ya tsara, burin sa a kan matar duk da ya aura don so da kauna ya cika, it’s unbearable happiness da wani shaidanin bangare na zuciyar sa ke gaya masa dole ya sha barasa don rage shi, kada ya zama matsala ga zuciyar sa.

Wata zuciyar na kwabar sa, wata na angizawa da cewa in ya sha yau, gobe ba zai kara ba ai. Ai ya gwada bari a baya kadan ya ga cewa (with time) zai iya barin, amma a hankali. Shima Young Abban, ai ya gaya masa gaskiya cewa gradually zai iya bari ba rana daya ba. In haka ne bai saba alkawari ba.

Let it be a farewell tsakanin sa da barasa. A final farewell tsakanin sa da kowanne ayyukan kafurci, tunda ya mallaki Siyaman gata kwance cikin gidan sa matsayin matar sa to zai yi komai don ya tsira da ita, amma a hankali. Sai kawai ya suri mukullin mota ya fice.

Karar tashin motar sa dana ji shi ya sani farkawa daga nannauyan barcin dana samu, koda yake na jima da farkawar mikewa daga gadon ne ya gagare ni, sabida nauyin da jiki na yayi min, na leka ta taga, sai na hango danjar motar sa ya fice daga gidan da mugun gudun gaske. Ko ina zashi haka kamar mai shirin tashi sama? Allah masani. Fata na dai koma ina ne ya dawo lafiya kuma kada ya dade.

Yanzu ne ma na san na fara son miji na wato Hamzah Mustapha (Mawonmase), so ba na wasa ba irin wanda physical relationship (gamayyar jiki) na aure ke assasawa, tunda yanzu ne na san darajar sa da kimar sa da irin baiwarwakin da Allah ya yi masa, na baya duk shimfida ne, kasancewar a can bayan duka a kan gaibu nake tafiya, yanzu ne nake tafiya dodar a kan turbar soyayyar reality wato ta rayuwar aure na zahiri ba cikin gaibu ba.

Yanzu ne nake gayawa kai na ban yi kuskure wajen dagewa da nayi na tseratar da mafarkai na ba. Hamzah ya cancanci duk wahalar dana sha a kan sa, domin gashi a dare daya shi ya fanshe min ita, ta sama da shekaru da goma. Na rantse babu inda bai shaida soyayyar da Hamzah ya nuna min jiya a gangar jiki na ba. Ko a gaban Allah kuma gabban jiki na zasu bada shaidar hakan. Cewa  sun haida da iri soyayyar Hamzah mai tsayawa a zuciyar diya mace.

Bayan na ji fitar sa daga Condo din mu, na kunna fitila dakin ya gauraye da haske, kasancewar ya saki fararen curtains (labulayen) dakin duka, ya kunna min room heater, ya kuma kashe duka kwayayen lantarkin dakin kafin ya fita. Making sure bai yi motsin da zai tada ni ba. Dana juya gefe na farar Singlet din sa na gani a gefe, ya manta bai maida ita jikin sa ba.

Daukar singlet din nayi na zauna a bakin gado na ina murmushin tuno wasu abubuwan da suka faru jiya, a hankali na rufa ta a kana fuska ta ina shakar kamshin Hamzah. Wato na turaren Guerlain Vetiver wanda nake kira (turaren Hamzah), ya kama rigar sosai, turare ne hamshaki mai sanyin kamshi na mazan da suka amsa sunan su (men’s perfume), wanda a tsayin rayuwa ta ban taba jin turare mai dadin kamshin sa da sakawa mace nutsuwa da mijin ta hadi da tada tsumin soyayyar ta gare shi kamar sa ba. Ko kuwa don kawai ina son mai shi ne da komai nasa?

Na yi kokari iyakar iyawa ta na dauke tsoron da ya same ni a lokacin, for the first time in our lives na bashi farin cikin da na san ya cancanta in bashi daren jiya, tunda shima ya gama min komai, tunda ya taimaka wajen maida mafarkai na zuwa reality. A lokacin da suka zo min a baude, har nake tunanin bazasu taba zama reality ba.

Sai ya tsaya cikin dan lokaci ya cike wannan wawakeken gap din dake tsakanin mu, wato na addini ta hanyar musulunta ba don ya shiryawa hakan ba sai don a cewar sa ya dade yana sha’awar hakan, sai soyayya ta ta zame masa jagora, ya ceci soyayyar mu, ya kuma ceci mafarkai na a kan sa.

Amma haka siddan sai wani bakon tunani ya zo min, kamar ina bukatar kara sanin waye Hamzah, bayan wannan dan sanin dana yi masa. Kamar sanin dana yi masa yayi kadan a matsayi na na matar sa yanzu, domin a dan takaitaccen lokaci ne komai ya faru (haduwar da auren) duka – duka bayyanar sa gare ni zuwa faruwar komai yaushe ne? Allah ne kawai ya yi ikon sa a kan mu (ya tabbatar da aure a tsakanin mu).

Sai na saka fuska cikin tafuka na na rufe idanu na, da rigar singlet Hamzah a kan fuska ta. Zuciyar nan mai tsananin son Hamzah da kaunar sa…. na kalubalantar sabon tunani na a kan sa, ta hanyar jefo min tambaya;

Shin Siyama akwai wani sani ne na daban da ya rage baki yi masa ba?

Kin san asalin sa da addinin sa na iyaye da kakanni kuma a hakan kika ce kin ji kin gani.

Zuciya mafi hankali da tunani mai kyau ta ce a’ah, akwai sanin da ya kamata na yi masa bayan wannan din, na halayya da dabi’a, wanda na yi masa daga bayyanar sa gare ni zuwa yanzu bai wadatar a cikin aure ba.

Zuciyar bangaren hankali da kyakkyawan tunani ta cigaba da cewa. Kwarai, ina bukatar sanin halaye da dabi’un miji na, na zahiri da badini as a life-time partner. A bangaren halaye da dabi’u, cika alkawari, amana da tsarkin addini ban gama sanin sa ba har yau.

Sai aka yi sa’a ni din kuma, wata irin mutum ce mai matukar tsantseni a kan wadannan din, da kuma kiyaye addinin ta matuka. Wato ni Siyama mai son addini ce, mai son kyawun dabi’u ce da son yin ado dasu, inada kokarin kiyaye dokokin Ubangiji tun bayan shiga ta Daar Al-Uloom. Haka kawai wani sabon bahagon tunani mara dadi kuma mara tushe ya bakunce ni a kan sa…

Hamzah ba musulmi bane for quite a long time a baya, for almost 38 years of his life ya yi su ne in Christianity, wani addini na wasu rukunin mutane kabilu daban da ba irin nawa ba, mai yuwuwa ne ya taba yin zina (ya nemi mata), mai yuwuwa ne ya sha samun biyan bukatar sa ta dan adam ta hanyar haramun iri daban daban Har ila yau, in aka yi la’akari da yawan shekarun sa kuma a yankin turai, turai din ma a kazamar kasa irin Amurka inda kowa ke yin abinda ya ga dama balle wadanda ba musulmi ba, gashi ko awon jinin nan na zamani da ake yi na kafin aure mu bamu yi ba, tsabar son cika burin zukatan mu ya rufe mana ido, shima kuma Young Abba gaggawar sa da mantuwar sa bata sa ya yi wannan tunanin ba duk bokon nasa, ko mai yasa? Sannan na bar shi ya tara da ni tun a daren mu na farko ba tare da kowacce iri kariya ba (contraception), ya kuma hada bakin sa da nawa ya sumbace ni sau ba adadi, alhalin ban san ko ya taba shan Barasa (giya) da bakin nasa ba!”.

“Innalillahi wa’inna ilaihi rajioun!” Na shiga ambata baka da zuci, ina girgiza kai na ina rokon Allah idan Shaidan ne yake son kawo min waswasi, don shiga tsakani na da mijin dana tabbatar ina yiwa wani irin sahihin SO da kauna ta hakika wanda babu irin sa a wannan zamanin, so ne tsarkakakke na samu zuciya ta ke yi wa Hamzah Mawonmase daga Indallahi wanda babu algus ko (material attachement) a cikin sa, to ina rokon sa yayi min iyaka da shi wannan tunanin mara tushe, mara amfani, mara hujja da madafa ko a addini, tunda addinin mu ya hana zargi, ya kuma hana bincike, shaidan ne kawai ke kawowa zuciyata farmaki mai son lalata zaman lafiya ta da kwanciyar hankalin dana samu, na nasarar mallakar abinda rai da zuciya ta ke so, bayan ba kowa ne yake nasarar dacewa da samun tabbatuwar mafarkan sa a zahiri kamar yadda nayi nasarar samun nawa ba.

Ni na san ina son Hamzah, kuma ina son komai nasa, amma hakika tun bayyanar sa a ba muusulmi ba na san nafi son addini na ISLAM a kan sa, da kuma tsarkin addinin musulunci cikin jiki na da rayuwa ta baki daya, fiye da ita wannan soyayyar ‘yar asali dana ke yi wa Hamzah. Ko bayan bayyanar sa dana ji cewa ba musulmi bane na yi duk kokarin da zan iya wajen ganin na yakice shi Allah bai bani iko ba, na tabbata ban zabe shi a kan addini na ba.

Wanda hakan yau ya tabbatar min (bayan na mallaki Hamzahn ta hanyar aure, zuciyar sa da gangar jikin sa gabadaya sun gauraya da nawa, kanwa ta kar tsami kwannafi ya kwanta) sai na gane cewa ashe dai ni Siyaman da sauran hankali na, ko ta ina aka je aka dawo za’a tarar ba makahon so nake yi wa Hamzah ba, irin wanda zai hana ni gano kyawun halayya da nagartar dabi’a ko akasin hakan cikin dabi’un sa.

A’ah, So ne gangariya kuma tsaftatacce daga Allah wanda ba zai hana ni ganewa idan ya yi ba daidai ba.

Na kuma fahimci cewa. Soyayyar dana ke masa a baya ta samu dan ‘tasgaro’ (cikas) daga lokacin da na same shi a ba musulmi ba! Wato ta samu dan nakasu.

Karfin SO da sabo da son ne kawai ya dorar da ita, yet ina son abina a yadda na same shi din har gobe, musamman da ya zo ya rungumi musulunci nan da nan sanadi na.

Wannan ya taimaka wajen farfado da sumammen son (karbar musuluncin da yayi), duk da cewa barin da aka yi, ba duka aka kwashe daidai ba wato hausawa suka ce ba’a bari a kwashe dai-dai, duk da hakan ina son sa har gobe da dukkan rai da zuciya ta, ina addu’a da fatan Allah ya inganta imanin sa ya cigaba a zama miji na a gaba dayan ragowar rayuwata ta gaba, amma kaso 30% cikin dari a cikin motar sa ya kwaranye. A lokacin da yake gaya min wata sadara……mai taken;

“Ni Hamzah dan addinin christianity ne!”.

Ni na san Hamzah ya riga ya musulunta a yanzu, zunuban sa na baya an shafe su, shi da wanda aka haifa cikin addinin musulunci yanzu basu da maraba. Sai ma shi da ya fi mu rangwamen zunubi. Ya koma tamkar jariri sabuwar haihuwa.

Amma duk da wannan tabbacin dana ke da shi na kasa nutsuwa a rai na, na rasa me yasa wannan bakon tunanin ke damuna yana addaba ta a yanzu; ba abinda nake so irin in tabbatar cewa Hamzah ba ya neman mata, ba kuma ya shan Barasa ko da kuwa karya zai gaya min,  ina son samun wannan tabbacin daga bakin sa ba daga kowa ba, don samun nutsuwa da kwanciyar hankali na.

Abubuwa da yawa sun taru sun hana ni kwantar da hankali na in mori wannan moment din yadda ya kamata, wanda kowacce mace sau daya take samun sa a rayuwar ta, wanda ya kamata yafi kowanne farin ciki a rayuwa ta wato (satin farko na amarci). Mai yuwuwa saboda can a kasan zuciya ta ina da damuwar Abba na a karkashin rai na, wadda yanzu ta zo ta kara lullube ni ta hana ni enjoying komai, bayan cikar mafarki da buri na na yin auren soyayya da samun irin mijin da nake mafarkin samu a kamanni da suffa, all my dreams are born alive now (duk da ban gama saninsa ta fuskar dabi’un sa ba) tukunna, amma wani hanzari ba gudu ba, duk da samun cikar mafarkan nawa ina son samun albarkar mahaifi na a cikin aure na da kuma yardar sa da amincewar sa ga mijin da Allah ya zaba min, ko in ce; ni Siyama na zaba da taimakon Young Abba, ba don komai ba sai don samun dorewar albarka cikin rayuwa ta, ba zan so nima yaran da zan haifa a gaba su yi min irin kafiyar dana yi wa Abba ba ya kasa tankwara ni, har a karshe ya zabi ya kore ni duk son da yake min.

Don haka zan roki Hamzah in ya huta, mun gama amarcin mu yadda ya kamata ya yarda muje gun Abban Abuja, koda kuwa zai tsire mu ne, ko ya jefa mu a wuta ya kona sabida ya samu ya huce fushin sa.

Hakan zai fiye min kwanciyar hankali fiye da in cigaba da rayuwa a kan fushin mahaifi na.

To amma shin ban makara ba???

Ita ce tambayar da na dade ina yi wa kai na tun bayan cikar mafarkai da burika na.

<< Sakacin Waye? 38Sakacin Waye? 40 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.