Barci nake ji sosai domin lokacin kusan karfe sha biyu na rana. Ina fatan kafin azahar in tashi don yin sallah da nema mana abinda zamu ci.
Duvet din na daga na kwanta daga can gefen sa, cikin dabara da wayo na saka filo biyu na jera su a tsakanin mu, sabida bana so a maimaita ‘yar daren jiya, hutu kawai nake bukata yanzun, da samun sararin shirya kalaman da zan yi masa amfani da su a kan abubuwan da suka addabi tunani na a kan sa.
Na dauka Hamzah yayi barci, jin yana sauke numfashi a hankali, sai ji. . .