Skip to content
Part 41 of 73 in the Series Sakacin Waye? by Sumayyah Abdulkadir Takori

Barci nake ji sosai domin lokacin kusan karfe sha biyu na rana. Ina fatan kafin azahar in tashi don yin sallah da nema mana abinda zamu ci.

Duvet din na daga na kwanta daga can gefen sa, cikin dabara da wayo na saka filo biyu na jera su a tsakanin mu, sabida bana so a maimaita ‘yar daren jiya, hutu kawai nake bukata yanzun, da samun sararin shirya kalaman da zan yi masa amfani da su a kan abubuwan da suka addabi tunani na a kan sa.

Na dauka Hamzah yayi barci, jin yana sauke numfashi a hankali, sai ji nayi ya mirgino inda nake, ya janye filallikan dana jera a tsakanin mu ya janyo ni cikin nutsuwa ya rungume ni tsaf, ya kuma lullube mu ruf, da lallausar duvet din. Daga sama har kasa.

Cikin muryar barci, maye-maye barci-barci yace. “idan kika ce min kina son hutu, I will adhere strictly to that, ba sai kin gina mana pillows a tsakanin mu ba, don’t ever do that to me.

I’m sorry for going out early, kina barci shi yasa ban tashe ki ba, ina so ki samu barcin da zaki huta sosai.”

Na lumshe idanu na cikin jin dadi, shi dai bai gajiya da bada hakuri a inda ya san ya yi laifi, Hamzah Mawonmase ne, ina jin wata irin ni’ima na saukarwa ruhi na idan na tuna cewa he’s indeed my long-term dream husband, the dream guy I’m always dreaming of…. The apologizer Hamzah Mowonmase… (mutum mai yawan bada hakuri). So abu ne da ba zai fassaru ba jin sa cikin jiki na bakidaya yau, in reality (cikin ido biyu) ba’a cikin mafarki ko fantasies ba, yana bani hakurin wani dan laifin da yake ganin ya yi min, wanda ni a wuri na bai taka kara ya karya ba.

Maimakon in ce komai kan abinda ya fada, sai na amayo da abinda ke damu na, ganin cewa wannan shine lokaci mafi dacewa da ya kamata in yi masa tambayar.

“Yau ni da wanne suna zan kira ka ne? Kowanne na fada sai in ga bai kai ba kuma bai yi daidai ba. Mr. Hamzah mijin Aisha- Siyama Boddo? Koko The Berom Man mijin Mambillah girl, my Mr. Radio my Habeeby Hamzahn VOA, idan na yi maka tambaya zaka bani amsa tsakanin ka da Allah?”
Hamzah bai san sanda ya kara kankameni ba yana dariya. Yace “Yi tambayar ki Habeebty, ko ta mecece kuma ko wacce iri ce, ban iya karya ba, kuma ko na iya ke kam bazan yi miki ba. Na yi alkawarin baki amsa.”
Murya na rawa cikin jin nauyi, amma na yarda gara in amayar da damuwa ta in huta, kada zullumin cikinta da taraddadin amsar ta su taru su kashe ni, in ya so duk irin amsar dana samu in yi hakuri da ita; bi ma’ana, mai dadi ce zan samu ko mara dadi? Na cusa kaina a cikin kirjin sa cikin jin kunyar abinda zan tambaya.

Hamzah bai katsi hanzari na ba sai kwantaccen gashin kaina da yake ta faman kitsewa yana warwarewa, nace “shin ka taba tarawa da wata macen kafun ni? Ina nufin, kana yin zina a can baya kafin mu yi aure?
Kana shan giya? Irin wadda turawan kasar nan da sauran wadanda ba musulmi ba ke sha suna shirme da tambele a kan hanya?”
Wuta ta daukewa Mr. Hamzah, na ‘yan dakikai, domin bai taba kawowa ran sa tambayoyin da zan yi masa kenan ba. Da bai yi saurin daukar alkawarin amsawa da gaskiya ba.

Da gaske ya san giya haramun ce a musulunci domin ko ba’a gaya masa ba ya gane tana shagaltar da bawa daga sallah da sauran ibadodin da suka hau kan sa, ko tasa yayi shirme a cikin sallahr sa, kuma tana gusar da Imani in yayi la’akari da halin data saka shi a ciki dazu, gabadaya imanin da ya yi da Allah daukewa ya yi ya koma tunanin addinin wahala zai zame masa, yanzu kam ya yarda addinin musulunci is broad kuma yana da fadi da zurfi sannan sai a hankali zai san shi.

Bai ce min komai ba, amma shirun da yayi shi ya tabbatar min bashi da amsar bani, kasancewar baya karya kuma ya yi alkawarin fadin gaskiya shi yasa ya zabi yayi shiru kawai.

Sai kawai na ji kuka ya zo min. wani irin kuka mai cin rai. Idan Hamzah ya sha tarawa da wasu matan kafun ni, ni da naci wahalar soyayya shekara goma da doriya ashe fanko na samu? Na soma kokawa da shi ina hadidiye shi. Gani nake in nayi kukan nan na gama faduwa a gaban Hamzah. Cikin rawar murya da daga sauti na ce.

“Ka bani amsa ko hankali na ya kwanta Hamzah, ko karya ce kayi min Hamzah zan fi son ta akan ka yi min shirun nan, ka ce min kawai duk duk abubuwan dana ambata dinnan baka taba yin ko dayan su ba!”
Na fada (in despair) murya na rawa da karkarwa jin kukan na son kece mini ba control, jiki na ya hau rawa da kyarma kamar masassara na son kama ni, Hamzah ya rike ni sosai a cikin kirjin sa, ya matseni kam-kam domin ya tsorata da rawar da jiki na yake yi, ya sumbaci kasan wuya na cikin damuwa ya ce “cool down, Siyaaam, please”. Sannan ya mika hannu ya kunna fitilar da ya kashe mana da farko, dakin ya gauraye da kyakkyawan haske.

Hasken da ya haske min kyakkyawar fuskar sa, ma’abociyar annuri da sparkling, da murmushin kwantar da hankali da ya kawo ya shimfida mata. Su suka hadu suka bata wani launin kyau mai ban sha’awa. Kafin ya soma yi min magana cikin taushin murya yana tallafe da fuska ta cikin tafukan sa.
“Na rantse da Allah Siyam ban taba yin zina ba, ban taba neman maza ba, sai kananan zunubi wadanda bawa mara addinin musulunci bashi da ikon kauce musu, musamman wanda addinin shi bai yi masa shamaki da aikata su ba.

Amma babban magana (as in sex) ban taba yi ba Allah kin ji na rantse, sabida I’m choosy, kuma ina da kyankyami, ban san yadda ake yi ba sai jiya a kan matar aure na Siyama Gembu. Na rantse miki iyaka gaskiya ta kenan.”

Akwai dai ‘yammata wadanda har gidannan suna biyo ni amma… amma… ya hau in ina. Kafin ya daure sabida kaifin idon Siyam da yake tsikarin shi ya ce. “Dan kauda idon ki a kai na sannan in gaya miki.”

Wata irin nutsuwa na ji ta saukar mini, at least, ya nuna yana jin nauyin idanuna ma wani privilege ne dana tabbata baya yi wa mata da yawa irin sa, kukan dana ke yi ya tsaida kan sa da kan sa. Na yarda duk abinda yake shirin fada a yanzun iyaka gaskiyar sa zai fada. Hamzah ya sunkuyar da kai ya ce,
“akwai wata yarinya anan kasar suke zaune, Suhaila Barkindo sunan ta, ta fi kowa naci a kaina, ita ce gida ita ce ofis, kamar ta hada iri da mayu, at times tana kokarin yaudara ta don in aikata, ita a tunanin ta hakan ne kawai zai sa na yarda na aure ta duk da addinin mu ba daya bane, har watarana ta saka min magani a glass cup, na sha cikin ruwa ba tare da na sani ba.

Wallahi na san dai naji sha’awar ta ranar, amma ko kusa ban iya na aikata ba, I was about to do that mistake tare da ita, but in the process… sai na ji na koma mace, duk wani ‘ego’ dina na Da namiji ya koma babu shi, sai dai dan kanana-kananan zunubi haka wanda bawa bashi da ikon kauce musu, musamman wanda ba shi da aure kuma bai tashi cikin saka idon iyaye ba, sannan ba cikin addinin musulunci ya tashi ba.”

Yana fadin haka ya yi maza ya kifa kan sa a kan cinyoyi na ya rufe ido cikin damuwa da jin nauyi, ya ce kada ki kalle ni da hakan fa, wallahi ko ranar ma ban aikata ba, I just…just….”

Nayi wani murmushi da yafi kama da kuka, na karasa masa “…you just kissed her!” Ko ba haka kake kokarin cewa ba ka kasa? I know you kissed several girls ma bayan ita Barkindo din, amma zaka linke ni a baibai. Shin dama zunubi yana da kanana yana da manya ne Mr. Hamzah?

Ai duk zunubi sunan sa zunubi. Babba da karami. Kai har cikin kallon kwayar ido Annabi yace ana yin zinar ido Hamzah. Ka daina fadin kananan nan. Kuma ka yi istighfari akan zunubin da ka raina din. To dayar fa kuma? Kwalba nawa kake sha a rana?”

Ya dan ciza siraran labban bakin sa kafin yace.

“Actually, I don’t take it often. Is once in a while depending on the circumstance. You know alcohol consumption is common to our people (non Muslims) and I’m not an exception.

Ma’ana (Kin san cewa dai ba wani abu bane shan giya ga wadanda ba musulmi ba, kuma nima ba’a dauke ni daga cikin su ba).
But gradually I’m trying to follow the Islamic teachings… I… I…. I’m sorry Siyam,

very sorry. I seldom take it! But not always”. Ma’ana, (Amma a hankali ina kokarin bin koyarwar Musulunci, ki yi hakuri Siyam, ina baki hakuri, da abunda zan fadi, na kan sha wani lokacin! Ba kullum ba).

Duk yadda yake so ya gayawa Siyam gaskiyar cewa yau ma ya sha, ko don ta yafe masa, ya samu rangwamen damuwar da ke zuciyar sa na ganin rashin kyautawar sa kan abinda ya yi din da sunan rage excitement, ya kasa. Ya riga ya san wadda ya sha a yau din ce zata fi ta kowacce rana yi mata ciwo, ganin cewa godiya ya kamata ya wuni yana yi wa Ubangiji ba butulci ta hanyar sabawa umarnin sa ba.

Idan ya fada, ya san Siyam bazata daina son sa ba, in dai ita Siyam ce ba abinda zai sa ta daina son sa banda ikon Allah, tunda bayyanar sa a dan addinin kirista da ba nata addinin ba bai fidda shi daga zuciyarta ba, baya jin akwai abinda ya fi hakan muni da zai hana soyayyar cigaba da tasiri, ya fahimci da soyayyar sa a ka halicce ta, in the course of that shi kuma ya koyi nasa son, ta shige ran sa sukuf, kamar dama yana jiran zuwan ta, kamar dama yana jiran isowar soulmate din sa, but he will offend her, idan ta ji cewa ya sha giya a washegarin cikar mafarkanta, wani abu da idan ya aikata shi bisa sanin sa ba zai taba iya yafewa kan sa ba, wato ya batawa Siyama rai da gangan.

Idan ta ji abinda ya aikata yau (she will lose all her trust on him). Ba abinda zai yi ta kara yarda da ingancin musuluncin sa. Kawai sai ya kifa kan sa da sauri a kan kirji na, ji yake kamar ya zubar da martabar soyayyar sa da kimar sa bakidaya daga idon Siyama daga yau, ya san ta da tsantseni da ikhlasi a kan umarnin Ubangijin ta, ya shiga fadin.

“Na tuba Siyam, na tuba na bi Allah, ba zan kara sha ba!”

Mun dade a haka. Ina kokawa da ‘mixed emotions’ dina, na so da kaunar sa da ke kara-kaina a zuciya ta suna kara hautsina ni, suna yin fatali da  ganin laifin sa don ya sha giya as a non-moslem, suna kara yi wa zuciyata dabaibayi a kan sa, wanda a yau ya hadu ya cakude da wani irin azababben kishin Mawonmase, kishin nawa akan wadda ya kira da suna ‘Suhaila Barkindo’ ne.

Ban gan ta da idanu na ba amma sai nake tantamar anya bata da matsugunni a zuciyar sa ko yaya ne? Tunda har zai iya sumbatar ta, duk da a bayanin sa ya kauce ya nuna maganin sanya sha’awa ta sanya masa? Amma me yasa ya bar ta take zuwa har gidan sa har ta samu access din yin hakan in har babu shakuwa? Idan kuma na tuna ba amshi kalmar musulunci ba a lokacin sai in ga nasa da sauki sosai, in yi masa uzuri sau saba’in wanda addini ya ce in yi masa. A yanzu kuma har da tausayin sa ke dawainiya da ni, duka sun hadu wuri guda (tausayi da so) suna ba shi kariya ta ko’ina a waje na, suna yi masa uzuri da rashin hasken addinin musulunci a wancan lokacin.

Hakika babu addini mai tsafta mai kuma tsari irin addinin Annabi Muhammad SAW. Amma maganar sa babu karya, babu alamun yaudara a cikin ta.

Na zuki wani dogon numfashi na fesar, cikin rashin sanin abin yi ko abin cewa, ganin cewa Hamzah na kara cusa kan sa a kirji na ne yana neman balle bra dina, me zan yi yanzu? Ko me zan ce a kai? Ban da in yi masa uzurin da ya roka, in karbi tuban nasa da zuciya guda, in kuma taya shi rokon Allah ya gafarta masa?

Koda yake ina da yaqinin daga sanda yayi shahada duka ya wanku a wajen Allah. Sai ko wanda zai aikata a gaba bisa ganganci ko sakaci, bayan amsar musulunci.

Zuciyar tawa dama tuni SO da kuma kaunar gaskiya sun riga sun yi mata dabaibayi bazata iya rike komai ba in dai a kan Mawonmase ne! Tunda har bayyanar sa a matsayin ba musulmi ba bai hana ni son abina ba, bana jin shan giyar da ya yi a baya kafin ya musulunta ko abinda ya gaya min a kan ‘yammatan sa kuma wani abu ne da zai sa ko zai hana komai ga zuciyar Siyama, musamman da ya ce kafin ya musulunta ne duk hakan ya faru.

Abin bukatar shine ya zamanto cewa ya cika sharuddan tuba, wadanda malam mai Akhdhary ya fada, ya rike alkawarin da ya dauka na ba zai kara maimaitawa ko komawa ga zunuban ba.

Sai na bar zancen a kan dole. Ba don na so ba, sai don bani da abin yi a kai. Hausawa suka ce “kowa ya sayi rariya ya san zata zub da ruwa ai”.

Don haka ya kamata in san cewa Hamzah tubabbe ne ko na ki ko na so wannan ita ce ‘bitter reality’ dina kuma reality din da har ‘ya’ya na sai sun sani. To shin amma ba gara hakan ba akan ace ni nayi riddah don in aure shi?

Haka na hadiye ‘yan koke-koke na na kishin Suhaila Barkindo, ina ta hango shi yana ta kissing din ta kuma a cikin gidan sa, ko da yace babu SO magani tasa masa a ruwa ya sha, sai na ji tamkar in dora hannaye na aka in saka ihu! Ko na samu rangwamen tafasar da zuciya ta ke yi.

Daga karshe dole na hakura na yayyafawa zuciyata dake tafarfasa ruwan sama, na kora da ruwan sanyi. Musamman saboda ya fara rikirkita ni da salon soyayyar sa mai wuyar bari, alamar zancen ya ishe shi haka ga irin wanda yafi so mu yi. Mai ma’ana kuma wanda zai amfane mu a duniyar mu da lahirar mu ba tone-tone ba.

Har na ji shi cikin kokarin hade bakin sa da nawa, yana cewa “past is past SEEYAMA HAMZAH, let the bygone, bury the hatchet…please Siyam I need you now”. Muka koma farantawa juna rai kamar ba wata magana mara dadi da ta hada mu yanzun.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 1.5 / 5. Rating: 2

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Sakacin Waye? 40Sakacin Waye? 42 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×