Skip to content
Part 42 of 73 in the Series Sakacin Waye? by Sumayyah Abdulkadir Takori

Sai da na ga Hamzah ya nutsu, ya samu gamsuwar data dace da shi, bayan yayi wanka kamar yadda na gaya masa duk bayan intercourse sai an yi wankan janaba, irin wanda yayi na shiga musulunci ne sai banbancin niyya, ya dawo cikakken Hamzan sa wato bayan ya shirya cikin shirt da wando samfurin Bloomingdale’s, ya fito a dan gayen sa sosai wato Hamzan nan na Siyama a VOA, ya zauna daura da ni yana danna wayar sa, sai na karya murya ina mai shafa physique chest din sa ta hanyar zura hannu na cikin rigar sa na ce,

“na manta in gaya maka a akwai sallah da ake yi ta neman albarka cikin aure a daren farko, unfortunately mu bamu yi ba, amma an ce better late than never, ka tashi mu yi yanzu.”

Na gaya masa duk yadda ake yin sallar daren farko da muhimmancin ta ga ma’aurata. Na ce yayi alwallah mu yi, da babu gara babu dadi.

Hamzah ba musu yayi alwalar ya dawo, yana daura alwalahr yana fadawa ran sa to ko don basu yi sallahr bane washegarin daren farkon su yasa ya karya kumallo da giya? Da sauri ya kawar da wannan tunanin tunda dai Allah ya cece shi daga kotun inquisitive Siyamah. Yayi alwalar da sauri musamman da yake har lokacin cikin guiltness yake, duk ya gama shan jinin jikin sa, yana tunanin ko dai Siyam ta ji smell din giyar ne a tare da shi, ko kuma wani nata ya gan shi a Bar din da ya je dazu ya kira ta ya gaya mata, shine dalilin da ya sa ta tsuye shi ta yi masa wadancan titsiyen tambayoyin?

Amma ai bata san giya ba, don haka bazata san smell din ta ko alamomin shan ta ba, kuma ba tada wani anan banda family din ta Adam da Nasara. Su kuma me zai kai su Bar? Ko kawa guda daya bai taba ganin Siyama tare da ita ba.

Kai ko da ta ji smell din daga bakin sa bazata tantance ba, a irin kyakkyawan brush din da ya dauka da turare mai sanyi. Da wannan ya samu karfin gwiwa ya yarda mu yi sallahr nafilar da na ce mu yi (bayan already mun riga mun gama tabbatar da auren namu sabida rashin hakuri irin namu tun gabanin nema masa albarkar).

Kafin mu tada sallar nake gaya masa akwai wasu nafilfilun da ake yi kullum wadanda Annabi SAW ya kwadaitar kuma duk sunan su ya fito a Al’qurani, (Shaf’I, wutri, Dhuha) nace ya dinga yin shafa’i da wuturi kullum bayan sallahr isha’i, suna da falala sosai ga rayuwar Musulmi. Haka salatul Dhuha, idan hantsi ya dubi ludayi”.

“Su din kuma ya ake yin su?”

Hamzah ya tambaya da doki, babu girman kai ko kankani a dabi’ar sa. Na yi masa bayani dalla-dalla ta yadda zai samu saukin fahimta. Hamzah akwai brain, tuni ya fahimce ni. Ya kuma rike komai.

Mikewa yayi muka gabatar sallahr ma’aurata na karanta masa addu’ar da zai kama kaina ya karanta. Sai da na maimaita masa kamar sau biyar sannan ya iya fada daidai, muka yi sallahr ya kuma kama kai na ya karanto addu’ar.

Dukkan mu barci muke ji, don haka muna shafa addu’ar muka kwanta, bayan ya hada mana tea mun sha, yana makale dani kamar kaska. Kamar mai tsoron kada wani ya sace masa Siyam, a haka muka yi barcin.

Hankali na bai kwanta da Hamzah ba, don na dauka zai nemi kari washegarin ranar, in roke shi alfarmar ya daga min kafa ko na kwana uku ne, ina bukatar hutu daurewa kawai na yi jiya, in samu in yi healing.

Bawan Allah shi da kan sa ya nemi in huta din. Na yi ajiyar zuciyar samun sa’idah lokacin da yace min “Habeebty, relax, today ‘no round’ na ga daga dan shafar ki kin fara makyarkyata”. Na harare shi cikin jin kunya. Ni kadai na san wuyar da na sha jiya da shekaranjiya a hannun Hamzah dole in yi makyarkyata dana ga yana shafata kamar mussa, duk da son da nake masa yana danne komai.

Sai Hamzah ya nuna min cewa ya fi ni sanin ciwon jiki na, ya fi ni bukatar hutun nawa, domin har zuwa kwanaki uku bayan nan bai yi attempting sake neman komai daga gare ni ba bayan sumba wadda dama baya gajiya mata.

Ban yi zaton hakan ba kuma, domin daga ‘first night’ din mu zuwa yau na gama gano weakness din Hamzah, shima kuma ya san abinda na fi so daga gare shi, amma hakan bai sa ya fifita bukatar kan shi a kan samun lafiya ta ba.

Wannan ya kara tabbatar min zan ji dadin zama da Hamzah saboda saukin kan sa, da rashin son kan sa, da yawan tausayin sa, ga far’a ga tsokana,s bayan saukin kan nasa kuma yana da muhimmanta bukatar abokin tarayyar sa sama da nasa bukatar.

Bayan Sati Daya

Ana kiran sallahr magriba, ni na fara zamewa daga jikin Hamzah na shiga toilet nayi wanka, brush da alwallah. Na lura wani irin barci mai nauyi Hamzah ke yi wanda ya wuce normal sleep, a rashin sani na (intoxication) ne. A kwanakin da ya baiwa Siyama hutu, giya ce ke debe masa kewa, kullum yana fita ya sha kadan ya dawo ba tare da na gane ba.

Bana so in yarda da zargin da zuciya ta ke halarto da shi na cewa, fitar da yake dan yi dinnan ya dawo min ido a lumshe, yana fadin barci yake ji, giya yake zuwa ya sha, tunda ya tabbatar mun sau tari ya kan sha din, ita ce kuma tayi cooling din sa ya kyale ni nake ta hutawa ta.

An ce zato zunubi ne, koda ya kasance gakiya, don haka na yi gaggawar jan istighfari ga zargin da ya darsu min a rai na, duk da na san cewa hakan mai iya yiwuwa ne amma na yarda da mijina har zuciya ta ba zai gaya min abinda ba haka yake a zuciyar sa ba. Tunda ya ce ya tuba ya bi Allah ba zai sake din ba.

“Ka tashi haka Mr. Radio, na rasa irin wannan barcin naka na rana da yamma, wanda baka tashi yin sa sai lokacin sallah zai fita. A yi maganar duniya ka yi bakam kana faman lumlumshe ido”, na sunkuya ina fadi a cikin kunnen sa. Duk da cikin barci yake bai fasa jawo ni ba, sai ya ce “bani da suna ne wai sai Radio? Ko ni na kirkiri radio sai haka Siyama!”.

Dariya ya bani sosai. Ban san me yasa bana iya ambatar sunan Hamzah kai tsaye ba, sunan na min nauyi a baki na, ko don kasancewar sa suna mafi soyuwa a gare ni, na kuma rasa sunan da ya dace in kira shi da shi, kowanne na fara sai in bari daga bisani don sai in ga bai dace da shi ba.

A can baya kafin mu yi aure na kan ce “Berom Man”, idan na bushi iska in ce “Mr. Radio”, ko Mr. Hamzah, amma yanzu fa? Wane sunan ya dace in kira shi lokacin da ya karasa goge duk wata hadda da ke kaina da nau’ikan soyayya iri-iri mai sanyaya zuciya da ratsa ruhi, masu wuyar mantawa ga diya mace, kuma masu wuyar samu a mazan wannan zamanin, ya yi formatting zuciya da kwakwalwa ta duka, bai bar komai a cikin su ba, sai zallar darussan da ya ke bani kullum masu kara min so da kaunar sa?

Na tuna ranar dana fara ce masa “Habeeby” a falon Young Abba ne, yadda ya rikice cikin soyayyar sunan.

Ni kuma wani abin mamaki a yanzu ba soyayyar ce tafi damu na ba, ina son gyara Hamzah ne da saka ido a kan dukkan ibadodin sa. Abinda zan fi so shine Hamzah na ya koma Shaihin Malami, Ustazu, ya zubar da duk ta’adun nasara da suka yi masa katutu, ya manta tarbiyyar Kaka Veronica, ta yadda duk ranar da muka je gaban Abbana da Ummati zan bugi kirji a gaban su in nuna musu zabe na ba zaben tumun dare bane, ko sa fi yafe mini da sauri, ya kuma zamanto ba zan ji dar din gaya musu cewa a baya ba musulmi bane ko na fada ya zama da kyar za’a yarda da ni.

Duk da haka daga yanzu zan cigaba da ce masa “Habeeby” don babu sunan da ya dace da shi sai wannan. Tunda ko ta ina aka je aka dawo Hamzah zai amsa sunan masoyi a gare ni. Ko in ce masa “Shaheed” tunda ya yi shahadah kuma ina so albarkar shahadar ta bi shi.

Ko da naso Dream Husband dina, ban taba tunanin zai zo min a ba musulmi ba, da ya zo din kuma, a matsayin Ahlil Kitab, sai Allah ya sallada shiriyar sa ta hannuwa na, ya kuma kaddari aure a tsakanin mu da gaggawa, kenan dole in zage damtse don mayar da shi yadda nake so ya koma, don haka in har soyayyar da nake yiwa Hamzah ta gaskiya ce dole in tabbatar ya kama addini ka’in da na’in yanzu.

I know it will not be easy for him and for me, Aunty Nasara ta ce babu wata makarantar addini da Hamzah zai shiga wadda ta wuce tawa, kamar yadda yace da Young Abba “It should be gradual,” nima kuma ya gaya min dazu (I’m gradually trying to follow the Islamic teachings), na yarda da shi a kan hakan, sai a hankali din, kuma zan jure kamar yadda malami ke jurewa sabon dalibi dan aji daya in tabbatar da shi a kan bautar Ubangiji.

“Don Allah ka tashi karfe bakwai na magriba fa, lokacin sallah zai fita Shaheed”.

Ina! Hamzah ya juya ya koma barcin sa, cikin magagi yake fadin “Siyam…. I love you. I love the new name!”.

Nace “ka rike love din ka bana so, tunda ba zai taya ka kwanciyar kabari ba, nima bazan taya ka ba, ka tashi ka yi sallah ka gaida Ubangijin mu, ya fi min dadin I love you din Habeeby”.

Hamzah ya dan bude idanun sa kadan, da suka kankance suka yi ja, yana dan murmushi cikin lumshewar ido, murmushin da ya kara ma kyakkyawar fuskar sa kyau, amma da ace na san giya da na gane, a karshen buge yake a lokacin. Ya ce.

“I’m sleepy, Sweetheart!”.

Daga haka ya maida su ya rufe, ya koma barcin sa cikin kwanciyar hankali.

(Barcin da bai tashi ba sai karfe goma na dare).

Amma ya tashi ne cikin hayyacin sa. Ko da ya duba lokaci da sauri ya bar gadon, a gurguje ya fada wanka yana fadin “Siyam, zamu raba alhakin nan na rashin sallah ni da ke, shine ko ki tashe ni?”

Ko kula shi ban yi ba, don na cika da takaicin kin tashin sa yayi sallah a kan lokaci, a rayuwa ta bana son jinkirta sallah babu uzuri karbabbe, ko yin kara’in salloli, koda yake an ce wai barci uzuri ne? Ban dai sani ba. In ma uzuri ne in an tashe ka fa?  Na cigaba da shafa lipstick da nake shafawa a gaban madubi na ban ce masa komai ba.

Yana barcin nasa naje nayi wanka na tsala ado da atampa embellished wadanda musammman Anti ke bada sautu Katsina a kawo mana in ta samu mai zuwa Najeriya, bayan nayi sallahr magriba da isha duk yana barcin asarar lokaci. Ya zo yayi kara’in sallolin la’asar, magriba da ishar sa a gurguje, sai na tuna masa shaf’i da wuturi sannan yayi.

Washegari da safe na yi kwalliya ta tsaf cikin swiss lace ruwan zuma, na kafe daurin kai a saman goshi kamar mai shirin zuwa dinar babbar aminiya. Dai-dai lokacin da Hamzah ya fito daure da towel iya kugun sa, ga wani karami a hannun sa yana tsane ruwa daga tarin sumar kan sa da baya askewa sai tsananin kulawa da yake bata, wadda yanzu ma ya wanke ta cikin kumfar Arganavita (Argana care&Lavender). Ta cikin mudubin na hango shi, ba shiri na sunkuyar da kai, my handsome hunk husband, looking obviously ravishing, sunkuyar da kan nawa ya faru ne kasancewar ban taba ganin namiji babba a fili cikin wannan yanayin ba, balle nawa mijin mai zati na gaske, mai kirar fadin kirji wadanda ake ma lakabi da giant, with physique chest, and handsome face, ga wani lallausar gashi da ya bi ya kwanta lambam a saman kirjin nasa, ya bashi cikakkar suffa, ta kasaitattun maza.

Sai a lokacin ya gama shiryawa, cikin bakaken suit da suka yi matukar amsar jikin shi, kodayake kowacce irin suttura Hamzah ya saka karbar sa ta ke yi ta kuma dace da zubin halittar sa, ta kasan idanu na nake satar kallon sa kaina a kasa, na kasa dagowa in sake kallon sa ido da ido sabida kunyar da ya bani daga irin kallon da yake yi mun, kato dashi a tube, ya zagayo inda nake zaune ya russuna ta saman kafadu na. Kyawawan fuskokin mu suka koma cikin mudubin, tamkar wata dan daren goma sha hudu da tauraruwar sa Zahrah, don haske da kyallin amarci da fuskokin mu ke yi.

Santsin gargasar da ke gefe da gefen fuskar shi da ke jike jagab da ruwa mai dumi ya shiga goga min a fuska, wadda baya rabo da gyaran ta da tsaftace ta, kamshin bath gel din ‘Argan’ da yayi amfani da shi ya mamaye ni, lokacin da ya russuna ta saman kafadu na yana goga min santsin jikakken sajen sa.

Sai naji ba abinda nake so a lokacin irin ya sumbace ni, ina so in sa hannu in riko wuyan sa amma na kasa, gashi ni bazan iya fada masa na warke I need him now ba, ko fara aiwatar da sumbar da kai na sabida fulatanci na.

Kamar Hamzah ya san me nake ciki sai bai sumbace ni din ba, sai gashi na da ya gyara min ta hanyar tufke shi a baya na. Sannan ya mike hannun sa dogare da kujerar dana ke zaune.

Daga tsayen da yake cikin kulawa da sanyin murya ya ce.

“Siyam zan tafi office, me kike so in taho miki da shi? Ko kina da sako gun Aunty?”.

Ji nayi kamar in dora hannuwa a ka in saka kuka. Cikin damuwa nace “office kuma? Basu baka hutu bane? Ni ban taba jin angon da bai yi sati biyu da aure ba a office ba.”

Dariya ya yi, ya ce “idan kina so in dauki hutu ki gama naki hutun daga yau, na fara gazawa, inna dawo yanzu ki daure ki dumama ni, ki armasa min daren yau yadda ya kamata in san cewa hutun amarci nake yi.

Tun jiya ina kallon ki wani sabon kallon so kike min, amma fulatancin ki na cutar ki, har da jera wasu munafukan filallika a tsakanin mu.

Bude baki nayi cikin mamaki kafin in rufe ido ina dariya nace “ni din Shaheed?” Yace “kwarai kuwa, inada kula fa akan komai nawa balle mata ta uwar ‘ya’ya na, sai wani kallon love kike min ta kasan Ido a fakaice kina fuskewa. Ki cire rigar fulatancin kawai mu yi ta kawar da arna, mu mori ni’imar soyayyah da Allah ya yi mana”.

Ban san sanda na kama dariya ba, nace “Sabida Allah Shaheed a ina ka koyi Hausa ne har haka? Har ka san wani a kashe arna?” Sai ya hau warware necktie din sa, ya fara undressing kan sa yana cewa “zancen kike so, bari ki ga yadda ake kasha arnan, ni nan da kike gani har Hausa Bakwai da Banza bakwai na sani, na san Barbushe da Tsimbirbira da Bayajidda har da Sarauniya Daurama.”

Sai dariya na ke kyakyatawa  shikuwa ya samu gangara ya soma cakumar kirji na yana fadin “ki min adalci mana Aisha_Siyam, in hutu ne ai na bar ki kin huta sosai fa. Kada abin ya koma da daukar hakki.”

Wani hali irin namu na mata sai na soma kokarin kwatar kaina ina fadin “Shaheed! Ba office ka ce zaka bane yazun?”

Hamzah ya yi min kyakkyawar rikon dana kasa kwacewa yana fadin “yarinyar nan kada mu fara ‘yar haka da ke, zan jure komai ciki har da duka amma ban da wannan yaren a lokacin da nake tsananin bukatar sa. Ko don kinga duk abinda naga kina so shi nake yi babu musu, shine zaki dauka har na gama amarci na?

Daga kawai na bar ki ki yi healing? Sai ki mike kafa ki dauka an gama? Wani abun ma ai sai mun dangana da Miami Resort, ba’a yi komai ba fa, sai bude hanya”. Na rufe ido ina dariya kunya kamar ta kashe ni. Daga haka ya shiga seducing dina ko ta ina, in the way and manner (ta hanyar da ya san) duk zukewar da nake faman yi bazan iya na kaucewa bukatar sa ba.

Domin wannan karon da canji ya zo; ya zo ne da sassanyar soyayya da na kasa tankwabewa. Haka hanyar da ya biyar da ni wannan lokacin daban take, wato ba irin ta lokacin farko bace, (so soothing and so romantic), ban san lokacin da na sakar masa ragamar rayuwata da gangar jiki na bakidaya ba.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Sakacin Waye? 41Sakacin Waye? 43 >>

1 thought on “Sakacin Waye? 42”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×