Skip to content
Part 44 of 73 in the Series Sakacin Waye? by Sumayyah Abdulkadir Takori

Har office ya tadda surakuwar sa anty Nasara suka gaisa, kasancewar ranar rahoton safe gare ta, ta tambaye shi Siyama da kwanan ta, yace “mun tashi lafiya Anti, tana gida tace in yo mata cefane. Ya ce,

“gashi ni ban taba cefane ba Anti, so ban san me da me ake ajiyewa a gida ba, the house is empty she said, kafin aure I use to go to restaurants to eat, ko in ci snacks in sha tea shikenan fa, a haka nake maneji, don haka nace ta bari in dawo sai muje tayi da kan ta.”

Nasara tayi dariya tace “wannan shine amfanin auren ai Mr. Hamzah, a kula da kai, a kula da cikin ka, sannan kuma a kuma kula da komai naka.

Baban ta ma yace in gaya maka zai kawo ‘gara’ gobe. So baku bukatar sayen komai banda nama da kayan lambu dana gwari.

“Menene GAARA?”

Hamzah ya tambayi Anty Nasara innocently, da accent din sa mai kama da na Asians.  Tsakani da Allah bai san wani abu gara ba. Dariya ta sake yi da yadda ya ja harafin ‘A’ din din ya furta “Gaaara”, ta ce “wata al’adace mai kyau ta dangin mata ga miji, in an kawo anjima zaka gani, ganin idanun ka.”

Hamzah bai jima da fita ba Aunty Nasara ta nufi office din Director Philip Carter. Suka gaisa sannan ta gaya masa auren Director Mawonmase da diyar ta. Tana bukatar su hada masa (grand dinner) ba tare da sun yi shawara da shi ba.

Dr. Philip was excited, da jin cewa ashe amaryar ma diyar Nasara Alkali ce, so abu duka ya zama nasu maganin a kwabe su, domin Hamzah na hannun daman sa ne sannan na kowa ne a VOA, kowa nasa ne yana da son mutane, yana da yawan taimako ta fuskar aiki ga na kasa da shi, bai da abokin fada. Sai mai wasa da aiki da gangan, shine kadai zai ga fushin Hamzah, nan da nan Director Philip ya hau buge bugen waya department by department yana bada umarnin abubuwan da za’a tsara washegari. Ba tare da Hamzah ya sani ba. Karin armashin abun Nasara ta ce masa yar tata da Director Hamzah Mawonmase ya aura is an intern yanzu haka tare da su a political department.

Sosai VOA suka shiryawa Hamzah (grand dinner) din taya murnar aure irin wadda ba’a taba shiryawa kowa a ma’aikatar ba, ba tare da ya sani ba, a babban dakin taro na ‘Muryar Amurka Hausa’. Yana isa gida dai-dai ya isa ma’adanar motar sa Nasara ta kira shi.

“Mr. Hamzah ka je gida lafiya?  Gobe da dare misalin karfe takwas na dare kuna da wani schedule ne?”

Hamzah ya ce “no Antin mu, ai daga yau na rufe fita kuma sai bayan sati biyun nan da office suka bani, in Allah ya sa muna cikin rayayyu. Zamu tafi (MIAMI RESORT) cikin satinnan, ba inda zan kara lekawa sai dalili yayi dalili”,

Aunty Nasara tayi murmushi cikin jin nauyin sa amma shi ko a jikin sa, Hamzah ba zai daina bata kunya ba, shi sam baya surakuta, a ranta tana tausayawa ‘yar ta Boddo-Siyama. A irin rawar jikin nan da Hamzah ke yi a kan ta, Allah kadai ya san irin tumurmusar data ke sha, poor Siyama!

Amma ta taya ta murna don ka auri mijin da ke son ka, yana mararin ka, yana gayawa duniya lokacin hutun sa naka ne, kuma a kayi sa’a kaima kana son shi, irin son da Siyama ke yi wa Hamzah, wani babban alfarma ne da ba kowa Allah yake yi wa ba. Ba kowa ke dandana irin ni’imar da ke cikin irin wannan auren ba.

“Alright, ku shirya Young Abba ya ce zamu zo mu dauke ku zuwa wani guri, kada ka damu (is just for thirty minutes), kada ka tambaye ni ko ina ne amma fa”. Ta karasa da dariya. Kamar mai Magana da kanin ta.

“To shikenan Anti sai kun zo. Amma dai Siyam Jilbaab (hijab) din sallahrta zata sanya ko? Idan har kin san akwai maza a wurin?”

Aunty ta rike baki tana hadiye dariya, sai kuma tace “duk shigar daka zabarwa matar ka Hamzah ita zata yi!”. “To babu matsala Anti, Allah ya kara girma, sai kun zo”.

Duk hirar da suke yi shi da Anti a kunne na ne, don lokacin ya iso gida, ya adana motar a ma’adanar ta, sai ya shiga takowa ya iso falo, daidai inda inda nake kwance cikin doguwar kujera ‘three seater’ ina jiran dawowar sa ya tsaya, yana tafe suna magana da Antin tun daga waje, kasancewar a handsfree ya saka wayar.

Zazzafar kazar nan ta kamfani wato (Kentucky Fried Chicken) Hamzah ya taho mana da ita hade da chips da sassanyar madara (fresh milk) a hanyar sa ta dawowa, anan falo muka zauna muka ci muka sha yana ta jan magana ina basarwa cikin fulatanci irin nawa, sannan  muka yi wanka kowa a toilet din sa, kowa kuma ya shirya a dakin sa, don yafi samun privacy na shiryawa yadda yake so sosai.

Yau a master-bedroom Hamzah ya zabar mana mu kwana, ba nawa dakin ba idan mun dawo daga cefane. Yana ta korafin wai tunda na zo gidan shi yake bi na daki na ni na ki zuwa nasa dakin, me yasa? Sabida kawai ina so in maida shi mijin Hajiya.

Muka fito daga kitchen tare, inda na kai kasusuwan kazar da muka ci na zuba a shara, shi kuma ya sha ruwa a fridge ya mayar ya rufe muka fito, yana ta koda kwalliya ta kamar zai lashe ni, amma sai ya dauko jilbab ya sanya min, wai saboda mazan shagon masu kalle matan mutane, muka je walmert supermarket nayi cefane na ba mai yawa ba muka dawo gida.

A hanya yake gaya min cewa jibi zamu bi jirgin kasa zuwa Miami Resort, don yin hutun amarcin mu a can. Har na tsayin tsayin sati biyu da VOA suka bashi. Miami shine garin da nake burin zuwa a duniya baki daya, yau gashi Hamzah zai cika min wannan burin.

Washegari ko kofar gida Hamzah bai leka ba tunda muka dawo daga Walmert jiya, inda nayo ‘yan tsince-tsince na sama-sama don ya gaya min sakon Anti na “GAAARA” da za’a kawo. A yadda ya fadi din zaka gane bai san meye garar ba. Da ba zai bari a kawo masa ita gida ba.

Karfe takwas daidai kuwa na safe aka danna kararrawar neman iznin shigowa Condo din mu.

Ilai kuwa ma’aikatan babbar mota ne, tare suke da motar kayan abinci. Hamzah sai fitowa yayi ya ga ana sauke masa buhunhuna da caton katon na komai da ya danganci kayan abinci. Baki sake yake tambayar wadanda suka kawo “ko kayan menene wannan? Daga ina kuma? Ko sun yi batan hanya ne?”

Sai suka ce “sako ne daga Adam Gembu (Young Abba)”, sai kuma ga kiran Young Abban ya shigo masa. Yana dagawa Young Abba ya ce masa “gara kenan, dana ce da Nasara ta gaya maka za’a kawo, naku ne”. Zai yi magana ya ce “kada ka ce komai, al’adar Hausawa da Fulani ne, ba ma al’adar mu bane na Mambillah ba, Nasara ce ta ce sai an yi maku, don ita bahaushiya ce ziryan, ku shirya karfe takwas na dare zamu zo mu dauke ku mu wuce inda zaku raka mu dinnan, ana jiran mu takwas na dare dot”.

Hamzah ya same ni a daki na yana yi min bayanin sakon Abban mu, sai yace amma jilbaab din nan zaki kara sakawa ko, ban san ina zasu kai mu ba, tunda sun ki fada, na san dole akwai maza a wurin kada su kalle min mata alhalin ko ni ban gama ganin ta ba”.

Sannan ya shiga mitar kayan abincin da Young Abba ya aiko dasu, wadanda sai muyi shekara bamu sayi komai da ya danganci kayan abinci wanda zai ajiyu ba. Yana korafi ne kan cewa sun yi yawa, shi bai taba sanin ana haka ba, wannan wahala da me tayi kama? A baka aure cikin mutunci sannan babu jimawa kuma a cika maka gida da abinci” Na yi murmushi kafin nayi maza na ce, “kuma ba’a maida hannun kyauta baya addinance, a al’adance kuwa idan ka maida masa ma ya zama raini tunda surukin ka ne”.

Sai na kashe bakin sa da wannan, daga nan bai kara korafi a kan garar ba. Sabida yana girmama Young Abba matuka.

Ban manta ba da daddaren sai nayi yadda yace din, na zuba Egyptian jilbaab dina sababbi kar ruwan kasa-kasa, wankakke kuma gogagge muka tadda su Aunty a mota don yayi-yayi sun ki shigowa da suka iso kofar Condo din mu, sun ce zuwan musamman zasu yi. Daga nan ni da Hamzah muka shiga bayan motar Young Abba, don ya ce mu bar tamu motar a gida, shi zai dawo da mu.

VOA CONFERENCE HALL

A babban conference hall din gidan rediyon VOA, duk wani sabo da tsohon ma’aikacin su ya samu halarta tare da mai dakin sa, in mace ce tare da mijin ta, in namiji ne tare da matar sa, wato liyafar cin abincin daren da VOA suka shiryawa Mr. Hamzah Mawonmase ta ma’aurata ce kadai (for couple). Daga ni har Hamzahn an shammace mu, don sai shiga confderence hall din muka yi muka ji an rude da tafi da sowar;

“Congratulations Mr&Mrs Mawonmase!”. Hamzah ya dube ni excitedly nima na dube shi ina murmushi, a cikin kwayan idon mu babu komai sai tsananin farin ciki da soyayyar juna wadda ta ki boyuwa ta fito sarari a kan kyawawan fuskokin mu, sai ya saka hannu ya janyo ni kwibin sa, ya makale ni cikin hannun sa, a haka muka karasa mazaunin da aka tanadar mana.

Ni na san wannan ba aikin kowa bane na Anty Nasara ne da Director Philip Carter, don naji sanda tace da Young Abba sai kowa a VOA ya san da auren mu, sai kuma an san Hamzah Mawonmase ya musulunta ya kuma auri ‘yar ta musulma.

Shiga ta kadai ta bayyana komai game da addini na, amma da yawa basu kawo wai da gaske Hamzah ya Musulunta ba shima, kasancewar addini (is a personal affair) a kasar, ba damuwar abokan aiki bane wane addini kake yi ko kake bi, wannan damuwar ka ne kai kadai. Amma a ko’ina baka rasa mutane masu tsegumi da saka ido.

An ci an sha, daga abinciccika na alfarma, sannan aka yi hotuna da vedio, daya bayan daya aka shiga bamu kyaututtuka na taya murnar aure. Abin ya sanya ni cikin farin ciki sosai.

Sai karfe goma na dare taron ya tashi su Aunty suka maido mu gida da kyaututtukan mu rankatakaf.

A washegari muka wuce ‘Miami Resort’ dake kwaryar birnin Florida domin yin shahr al asal (honeymoon) kamar yadda Hamzan ya kira tafiyar tamu.

Da yammaci lis, muka shiga Greater Miami Beach, a hotel din “The Pinch, Downtown Charleston” inda anan Hamzah ya kama mana daki a bakin beach tun kafin isowar mu. Wani irin amarci muke zubawa tun saukar mu a Miami tamkar Lailah da Majnoon, soyayya gangariya kamar don mu kadai aka halicci duniya, kuma ‘yar uban su ta bada labari a littafan hikaya, wanda in nace zan fade ta dalla-dalla zai iya cika littafi guda ban gama ba.

Abinda zan iya cewa shine Hamzah ya sha wahala kafin ya samu ya dan canza ni zuwa yadda yafi so in koma wato shyless, when it comes to his needs, tuni na zama ‘yar gari a harkar love, yadda Mawonmase yake so in koma, duk da haka a mafi yawancin lokuta fulatanci na bai bar ni ba, kuma ba zai bar ni din ba, don bana taba yarda mu zauna a bakin beach sai-dai a dakin mu, in ya so sai mu yaye curtains muna hango abinda masoya maziyarta daga al’ummatai daban daban ke yi a bakin  resort din.

Al’umma daban daban daga kasashen duniya na kashe makudan kudi su je Greater Miami ne kawai don hutawa, tun ina alkunya har aka zo gejin da wani lokaci na fi shi son abun. Ya ce a kwayar idona yake ganewa whenever I need him. Dream Husband wato HAMZAH MAWONMASE ya tabbatar mun shi miji ne abun bugun kirji in yi tunkaho da alfahari da samun sa a ko’ina in dai ta fannin soyayya da ruwan zumar ta ne, macen da Allah ya yi wa dace irin nawa manta komai take yi na damuwar duniya sai mijin nata kadai, tuni na manta da damuwar zuwa wajen Abba neman gafara, amarcin da gardin sa da zakin madarar da ke cikin sa ya mantar da mu maganar tafiyar mu zuwa kasar Najeriya, ya mantar da ni damuwa ta a kan Abba.

Ba ni Siyamar ba, ba shi Hamzan ba kowanne sai da ya murje yayi wani irin fresh da shi cikin sati biyu a Miami. Ana I gobe hutun sa zai kare muka koma Washington. Sai bayan kwana biyu da dawowar mu muka koma office.

Sai ya zamanto daga ranar kullum tare muke fita VOA ni da Hamzah, kuma sai ya tabbata ya raka ni har kujerar ofishin mu, sannan zai wuce nashi ofishin, yana mai jaddadamin in kula da kai na in kula masa da Siyama-Boddo ko a bayan idon sa, kafin lokacin da zamu tashi kuwa zai kira ni a waya ya kai sau biyar.

Idan ni na riga shi tashi zan tafi nasa office din in jira shi ko in tafi wurin Aunty Nasara ya zo ya tadda ni, in ya gama mu wuce gida.

Hamzah bai damuwa don ya rike min handbag zuwa mota a bainar VOA gaban kananan ma’aikatan sa, ya kuma bude min gaban mota da kan sa in shiga. Ya mayar ya rufe with so much respect. Ire-iren kulawar da ke kara min kaunar sa a kullum. Saukin kai da tawali’u a cikin jinin sa ne.

Ba jimawa na kammala internship dina da VOA watanni hudu bayan auren mu kenan, na koma Jami’ar mu wato George Washigton University na cigaba da hada B.A dina a kan Journalism, saura bai fi watanni shidda in kammala ba gabadaya.

Don haka muka canza shawarar cewa sai bayan na kammala karatun nawa gabadaya zamu je gida Najeriya. Amma bayan da giyar amarci ta fara saki na kusan kullum sai na yi mafarkin na ga Omar.

Mun gama komai na shirin kwanciya bayan mun rage nauyin kayan jikin mu na yi sallahr isha da ban yi ba, lokacin Hamzah yana nasa dakin bansan dai ko me yake yi ba dai. Na kashe wuta na kwanta kenan sai gashi ya shigo dakin cikin ruwan tokar kayan barci masu kauri ‘yan gidan ARMANI. Yana tazar gashin kansa da ya wanke cikin kumfar (Argan).

Bana gajiya da kallon fuskar miji na Hamzah, kamar yadda idanu na ke son gargasar gefen fuskar sa da ta saman kansa wato tarin lallausar sumar kan sa da yake tarawa mai dan karfi irin ta Black Nigerian Men. Ina so na tambayeshi ko yayi sallah amma na daure na yi shiru, don bana so ya gane cikin kwanakinnan na saka ido a kan sallahr tasa. Wadda na lura in ban ce ya yi ba, tun bayan da amarcin ya soma sauka a kan sa to ya daina yin ta sam. Hoping yau zai yi din kafin ya kwanta, ba tare da nace ya yi din ba.

Amma har ya hawo gadon da nike kwance da niyyar kwanciya barci bai yi sallolin ke kan sa ba na magriba da isha. Bai kuma san na lura da hakan ba.

Ina jin sa ya ja duvet ya lullube mu, ya soma laluba ta, ban san lokacin da na kwaye bargon ba, na dauki filo na jefa can gefe na maida mu kwanciyar kai da kafa.

Cikin mamaki Hamzah ya ce “idan na shure idon ki fa ban sani ba da kafa ta? Wannan wane irin sabon salon kwanciya ne na wulakanci? Ko in ce sabon raini?

Tukunnama, kin ji na ce ina neman wani abu ne, just daga kawai mutum ya rungumi matar sa?” Na dai yi masa shiru, ko na samu ya gane fushi na akan rashin sallahr sa ne ya tashi yayi amma gogan sam bai gane ba.

Hakan ta sha faruwa, ba koyaushe Hamzah ke iya yin salloli biyar a rana ba, watarana asubah kawai yake yi itama don ina saka shi a gaba ne in ce ya yi mana limanci.

A haka muka kwana, zuciya ta ta yi duhu, yayi maganar duniyar nan ya yi ban-bakin duniya akan in gyara kwaciyar da na yi shi ba abinda yak enema yau, ban ce masa kala ba. Don kan sa ya gaji ya juya min baya shima ya kwanta, kan sa daidai kafafuna kamar yadda na zabar mana.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Sakacin Waye? 43Sakacin Waye? 45 >>

4 thoughts on “Sakacin Waye? 44”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×