Skip to content
Part 45 of 73 in the Series Sakacin Waye? by Sumayyah Abdulkadir Takori

Haka washegari na tashe shi don yayi asubah in gani ko zai hada dana jiya da bai yi ba? Hamzah juyi yayi cikin barci yace “Siyam, zan yi in na tashi, yanzun I’am sleepy”. Daga haka ya juya ya cigaba da barcin sa cikin kwanciyar hankali.

Watanni bakwai kenan na auren mu, wadanda watanni ne na wata irin koriyar soyayya shar, da fahimtar juna tsakanin ma’aurata mai shiga rai, babu komai a cikin su sai sassanyar soyayya mai tsayawa a zuciyar masoya, musamman wadanda suka yi dace da kasancewa karkashin inuwar aure.

Amma kuma daga wata biyar baya Hamzah ya kasa sallah yadda ya kamata, in har ba na ce tashi ka yi ba. Abinda ban fahimta da wuri ba shine Hamzah baya wankan janaba (guslul janabah) sai na sabulu da gel-gel din sa kala-kala na gayu masu dan karen tsada. Sannan ya koma shan giyar sa har fiye da shan da yake mata a baya.

Ina ganewa ya sha barasa idan ya buya a dakin sa alhalin na san yana cikin gidan, da kuma duk lokacin da yake barcin da ya kasa daga ko dan yatsan sa. Amma hakika ya cika umarni na wanda yake kira severe punishment a gare shi, bai kara attempting neman komai daga gare ni ba, tun daga lokacin da na tsiri mana kwanciyar kai da kafa, da jera filallika a tsakanin mu.

Sannan ya kasa ganin walwala ta ko kankani. Ya dauki hutun karshen shekara musamman domin yayi settling abubuwan da na tsiro a tsakanin mu ya kuma samu Siyamar da ya yi kewa, amma ya rasa kaina ya rasa kasa na duk da hakan, ni kuma na kasa fitowa fili in gaya masa bazan iya hada jiki da shi alhalin ya kasa tsaida sallah kuma yana shan barasa duk irin son dana ke masa.

Ta fannin abinci bana wasa da yi masa girki mai kyau, tuwon Acca ma akai-akai nake yi masa, sai kazo shimfidar mu ka gan mu kai da kafa, kowa na fama da dacin dan uwan sa da rungumar filo, Hamzah na ganin Siyam tana kwarar sa babu hujjah babu dalili sai halin rashin godiyar Allah irin na mata, tunda da me ya raga mata?

Kusan duk alkawuran da ya daukar mata daga auren su zuwa yanzu ya cika su banda na zuwa Najeriya. Shima kuma ai sun yi shawara ne sai ta kammala karatun ta. Kullum ita yake tunawa kafin ma ya tuno kan sa ko Kakar sa. Amma duk bata ga wannan ba sabida halin su na matan da suka samu miji na son su, ta gwammace ta canza musu rayuwar farin cikin da suke ciki zuwa gaba.

A yanzu a yanayin da muke ciki (idan har ban yi kuskuren fahimta ba), idan har ba shaidan ne yake ingiza ni ga yarda da wannan sabon tunanin ba, na fahimci Hamzah ya koma kiristancin sa ne kawai, wato ya shigo musulunci da fuska biyu (da boyayyar manufa), ba don Allah bas ai don ni Siyama, ba kuma don ya tsira daga azabar wuta ba, tunda in bai musulunta ba babu ta yadda zan yarda in aure shi ko su Young Abba ma bazasu aurare shi ba, ko da soyayyar zata kashe ni.

A sabuwar fahimtata ta yanzu, Hamzah ya aure ni da niyyar in ya sameni ya gama daukar abinda zai dauka a jiki na, sai ya daina sallahr ya koma rauwarsa ta kafurci yadda yake yin ta babu yadda zan yi da shi tunda na riga na zama karkashin ikon sa, a lokacin da ban isa in ce bana auren sa ba, don in har ba kuskuren fahimta na yi ba a halin yanzu inada karamin juna biyu, aure na kuma bai sa ya daina shan barasa ba, bai hana shi zuwa Bar da clubs yin caca ba, duk da yana boyewa har na zo na gane da kai na.

A sannu na kara fahimtar abubuwa sun sauya a tare da Hamzah na, dokin musuluncin ya sake shi daga lokacin da na samu ciki na ragebashi hadin kai a shimfidabsabida bana son turaren sa, yana murna da cikin kuma yana matukar son a haife shi lafiya ya samu aboki ko magaji. Sai daga baya na fahimci wani abu, ashe duk sanda muka yi auratayya baya wankan janabar da na koya masa, Young Abba ma ya koya masa tun ranar da aka musuluntar da shi.

Kuma a haka zai zo ya yi sallahr sa idan na takura sai ya yi, wadda baya bata nutsuwa da lokaci, babu ikhlasi da khushu’I a cikin ta sharp-sharp yake yin ta kullum, wannan yasa duk na yi wani irin sanyi da ni a kwanaki nnan, gwiwata ta sage nna sare daga all’amarin Hamzah, jiki na ya yi yi la’asar, na koma wata irin sukuku! Da ni abun tausayi. Gaba daya na birkice na zama kullum cikin damuwa da tashin hankali. Musamman idan na tuna hukuncin wanda ya yi RIDDAH daga addinin musulunci.

Ko far’a ta Hamzah ya daina gani, wanda hakan shima ya birkita shi ya sa ya maida zaman sa a gidan sai lokacin barci kadai, don in zai wuni zaune a daki na uffan na daina ce masa, kallon arziki wannan ya daina samu daga Siyamar sa, rarrashin duniya yayi min daga bakin sa don ya ji laifin da yake yi min ya gyara mu koma rayuwar mu ta baya na ki magantuwa, wai an ce shiru ya ishi mai hankali, idan yayi kokarin taba ni kuwa nan zai ga tashin hankalin da zai gwammace mu raba daki, ko jiya da ya shigo rokon in dafa masa ruwan zafi ya sha, sabida baya jin dadi hararar sa na yi, na kuma gaya masa yayi harkar sa in yi tawa tunda ba kabarin mu daya ba, ba kuma tare za’a binne mu in mun mutu ba, tunda ba tare muka zo duniya ba.

Wannan ne dalilin da yasa ya zabi kullum idan ya tashi aiki sai ya zarce ‘Bar’ ko wajen caca (Casino), ya sha giya iyaka shan sa, a ganin Hamzah tunda Siyama ta tsane shi yanzu, meye amfanin sa banda ya koma drunker?

Na kuma rasa wanda zan iya samu in gayawa damuwa ta a kan Hamzah ko shawara in samu, sai in ga kamar dariya duniya bakidaya zata yi min. Idan har ban manta ba Aunty Nasara da kan ta tun da farko ta fada min cikin karaji, lokacin da ta dawo Atlanta ta fahimci har lokacin da ta yi min bayanin wanene Hamzah Mawonmase ban rabu  da shi ba, bazan manta ba Nasara da yake mai hangen nesa ce ta ce da ni tun a lokacin “HAMZAH MAWONMASE DA TA SANI KARYA YAKE YI BA ZAI TABA MUSULUNTA SABODA NI SIYAMAH BA!”.

Ta kara da cewa “kafun ni an yi dubu na, da suka fi ni komai a kan sa, sai dai su su yi riddah, kuma hakan baya sakawa ya aure su”.

A lokacin na ji Anty ne kawai, a matsayin ‘yar hana ruwa gudu, kuma maganar ta ta bayan kunne nata bi ta wuce fit, thinking that, in everything there’s exception, wato case dina is different dana sauran matan, don ni Allah ne ya qadarta shigowa ta cikin rayuwar sa ba kyale-kyalen da ya mallaka ba, wanda na ke da tabbacin su sauran matan shi suke bida, da kuma kasancewar sa ‘media celebrity’, a tunani na a lokacin, ni Siyama daban nake da sauaran mata ‘yan uwa na, 

Yanzu na yarda babu wadda tafi wata ni da sauran ‘yammatan da ke macewa a kan soyayyar Hamzah Mustapha, idan a da ina tunanin hakan to na yarda da gaske na yaudari kai na, banbanci na dasu daya ne; ni na zabi addinin musulunci sama da Mawonmase din, amma kuma ai na bar Abba na a kan sa.

Ni da shi mun zama bakin juna yanzu. Soyayya ta rikide ta zama wani abu da ya riga ya wuce cikin past kundin mu (littafin mu na baya) a lokacin da muke watanni tara kacal da aure. Ni na kasa fadar dalilin fita hanyar sa da na yi rana daya, wai jira na ke ya gaya min da kansa da bakin sa ya fita daga addinin musulunci, shi kuma ya kasa complaining ko titsiye ni a kan sai na fada masa, kamar ya sha jinin jikin sa akan laifukan nasa.

Tun lokacin da yayi rarrashin duniya ban ce masa komai ba, ya gaji ya rabu da ni shima, baya magana kamar da, yayi cooling sabida giya da yake faman sha kullum ya baro office don daukewa kan sa damuwar Siyamah. Sai ya zo ya yi min kwance-kwance a kan doguwar kujerar falo ko sofa din dakin barci na, ya kifa hular sa a kan fuskar sa, daga nan har garin Allah ya waye bana kara sanin me yake ciki.

Ya daina magana kwatakwata, sallah kuma baya yi ko zan hadiyi zuciya bai sani ba. Daga ni har shi bama barcin kirki, gara ni ina tashi in yi nafilfili tsakar dare in roki Allah ya yi masa gafara, kada ya tashe shi a sahun “wailun likulli hummazatun lummazah”, shi kuwa Hamzah saidai juyi a kan kujera.

Sai gidan namu ya koma tamkar gidan kurame babu mai cewa da dan uwan sa uffan. Tamkar ba amarya da angon nan na Miami Resort, masu neman cinye juna don soyayya ba.

A daren yau na kasa jurewa jin sa ya shigo gidan wajen karfe daya na dare. Koda na leka da ya fito daga motar sa da dafa bango ya idasa shigowa, wannan ya tabbatar min Hamzah a buge yake (fully intoxicated). Kuka ne mai karfi ya taho min nayi maza na saki labulen na fita falon na cimmasa.

Ya zube cikin doguwar kujera yana maida numfashi yana wani irin lumlumshe ido, na tsaya a kan sa kamar an jefo ni falon. Takaicin ganin ya daga ido ya kalle ni da rinannun ‘almond shaped eyes’ din sa, ya kuma dauke kai kamar bai ganni ba, ya fusata ni matuka.

Nace “kaico na da zaben son zuciya ta! Kaico na da zaben kafiri a matsayin abokin rayuwa ta, wanda ya zabi ya gusar da hankalin sa fiye da bautar Ubangiji, kaico na da tunanin zan iya maida mushriki musulmi, kaico na da auren mai fuska biyu! Kaico na akan biyewa abinda zuciyata ke so da neman samun sa kota halin-kaka. Kaico na da rashin baiwa Allah zabi da yiwa kai na addu’ar zabin Allah.

Yadda ka yaudareni Hamzah, ka aure ni da sunan musulunci a fatar bakin ka Allah ya saka min tun a gidan duniya”. Sai ji kake kwaf! Hamzah ya sa kafar sa daga zaune ya kwaso ni ya warbar, saida na fada cikin kujera da baya na, yace,

“ni kike cewa kaico da ni Siyama? Ana neman kafura mara tsoron Allah da sanin hakkin aure kuma mayaudariya aka same ki an gama Siyama.

Ya yi murmushi cikin lumshe ido. “Wawiya kawai, sai tutiyar addini da fadin Allah a baki, alhalin bata san komai na daga martabar da Allah ya yiwa iyaye ba, ko ni da na tashi in Christianity da ace na tashi na tadda Babana a raye ba zan sha poison don in rabu da shi in rayu da wata mace ba.

“Kaico” ai yana wuyan ki Aisha-Siyamah, kullum tunanin ki shine kin fi kowa tsoron Allah, kin fi kowa sanin addini da kyautata shi. A hakan kuma na ga kin zabi marital-sex din wanda kike kira kafuri kuma wanda kike so duk da kafurcin nasa, sama da Baban ki da ya haife ki, ya raine ki ya yi dawainiyar rayuwar ki da ta ilmin ki. Umhhh?

Ya lumshe ido cikin maye sannan yace “Amma kullum ki yi ta nunawa mutum shi kafuri ne, bai san Allah ba sai ke, na riga na yarda Allah guda daya ne, idan wuta da aljannah mukullin kofofin su a hannun ki yake, in kin tashi hisabi ki jefa ni a wadda kika ga dama.

Ni ban ce kin yaudare ni ba, ni da kika yaudara da Kalmar SO, kika koyawa wahalalliyar soyayya mai wuyar bari, sannan rana daya ban ankara ba kika yasar da ni a kwalbati, ko in mutu ko in yi rai (after this deprivation) ba damuwar ki bane.

Ban san soyayya ba sai a kan ki Siyam, rana daya kin fahimtar dani cewa you married me to have my body and my sweet sex only, tunda kin gama samun su da duk abinda kike so daga jiki na da zuciya ta, har da cikin haihuwa kin samu, shikenan ni Hamzah banida sauran amfani a gare ki ko? Kin gama da ni!”.

Tunda ya fara maganar nan nake dafe da hannuwa a baki da kunci ina sauraron sa, hoping duk wadannan muggan maganganun dana ke ji yau suna fita daga bakin Hamzah Mawonmase cikin ire-iren mafarkai na nake jin su.

Fata nake in farka in ga ba haka bane, fata nake in farka in gan mu cikin mayafin rufar mun nan na duvet mai tsananin laushi, muna makalkale da juna muna sumbatar juna kamar zamu cinye juna, ina addu’ar wannan ya kasance mafarki na guda daya rak a rayuwa da bazai taba zama REALITY ba.

Amma har zuwa wani dogon lokaci mai tsaho da Hamzah ya gaji da gasa min maganganun da suka dade da nuna a bakin sa, bai taba samun damar amayar da su ba sai yau da ya samu damar data dace da shi, da ya gama ya tashi a daddafe ya shige dakin sa ya banko kofa, ban farka daga mafarkin nawa mai kama da ido biyu ba.

“Lahaula walaquwwata illah billah.. Allahumma ajirni fi musibati….” kawai nake iya ambato, wasu hawaye masu zafi da dumi suna shimfido min suna sauka a kan kirji na, irin wadanda zafin su daga zuciya yake fitowa.

Karfe uku na dare agogon Washington na kira Aunty Nasara a waya, tana dauka na ji dukkan kukan duniya ya kwace min. Kukan da ko sautin sa na musamman ne, wanda tun bayan awanni biyu da suka wuce nake so in yi shi na kasa, sai ajiyar zuciya da nake ta faman yi.

Kewar gidan mu da al’ummar cikin sa ta dawo min sabuwa. Kewar Abba na Mamman Gembu, da tsayin lokacin dana dauka ba tare da shi ba da nadamar abinda nayi masa su suka sani yi wa Aunty Nasara wani irin kuka da kururuwa mai tsirga kwakwalwa da firgitata.

Ni na tabbata alhakin Abba ne da rashin albarkar sa cikin aure na kadai suka sa Hamzah yau ya yi min abinda ban taba zato ba, an ce idan aka yi depriving men from sexual life, suna aikata komai cikin bacin rai, amma ban zaci ko kusa Hamzah ko me zan yi masa zai taba iya yi min gorin nan ba.

Aunty Nasara dana katsewa barci cikin tashin hankali ta ce.

“Siyaman VOA, ya aka yi?”

Na dauki lokaci ban amsa ba sai kukan nadama da kaico da kai. Cikin wannan halin na ce da Aunty “tabbas Aunty kin yi gaskiya, abinda babba ya hango yaro ko hau rimi ba zai hango ba. Hamzah ba zai taba musulunta sabida ni ba, sai don ya samu mallakar aure na da amincewa ta ga kaddarar auren sa, daga nan kuma ya cigaba da kafircin sa, tunda duk abinda yake so a Siyama ya gama samun sa.

Na dakata na ja numfashi na da ke sarkewa kamar na mai ciwon asthma, na fyace hanci na sosai sannan na cigaba.

“A wancan lokacin ban saurare ki ba, karewa ma na ji ki ne kawai, sabida SO da son zuciya sun rufe min ido. Amma hakika zan dawo gaban iyaye na a safiyar gobe, ba zan zauna da shi a haka ba. Zan je kuma in fidda cikin sa tun ban haife shi ya tambaye ni dalilin kin zaba masa uba nagari ba, sai tubabbe mai shan giya.

Na gode Allah da ban bari ya kai kan sa ga Abba na ba, na kara ma kaina bakin fenti a wurin sa ba, in ya ji tun asali wanene Hamzah.

Aunty na dade ban gaya miki Hamzah bai bar giya ba, don kullum tunani na shine a hankali zai bari, kamar yadda ya alkawarta muku, tun yana zuwa ‘Bar’ yana shawowa a can ya dawo ya buya, har yanzu ya daina kunyar idanu na ya fara zuwa gida da abin sa, ko jiya na ga kwalaben giya (wine) a karkashin kujerar motar sa, wasu an sha, wasu ba’a bude ba”.

Sai yanzu na fahimci nauyin barcin sa na lokaci-lokaci mai hana shi sallahr asubahi da sauran sallolin farillah ashe ba komai bane intoxication ne.”

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Sakacin Waye? 44Sakacin Waye? 46 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×