Skip to content
Part 48 of 73 in the Series Sakacin Waye? by Sumayyah Abdulkadir (Takori)

Daidai lokacin da ya kawo kofar dakin Siyam, sai ya kashe wayar ya saka a aljihun jamfar sa.

Yana shiga dakin ina fitowa daga toilet, daure da tawul iya gwiwoyi na, wanka na fito na kuma wanke gashin kaina yana ta yararin ruwa, duk ya hautsine ya jike, yana bukatar in busar da shi da (hand-dryer) kafin na kwanta barci.

Ina jin sa yana ta magana a waya amma ban san me yake cewa ba ko da wa yake maganar, kamar dai cikin yaren sa yake maganar, na dai tabbata daga shigowar sa zuwa yanzu ya ci abincin da na ajiye masa don a kan Gwaten Acca baya da fulako.

Ido muka hada ni da shi ta cikin hasken kwan lantarkin da ya dallare dakin nawa kamar rana, ga mamakin sa, abinda bai taba zao ba da ‘yar far’a na ce da shi “sannu da zuwa” ba tare da na dago na dube shi ba. Amm na cire kalmomin nan guda biyu ‘Shaheed’ ko ‘Habeeby’ da na ke kiran sa da shi a lokutan mu na dadi. Wasu sunaye da yafi son ji daga Siyama, sunaye ne da ya rabu da ji daga bakin Siyam din sa kwana da kwanaki, so he missed it. Rabon da in ce masa sannu da zuwa ma ba zai iya tunawa ba.

Shigowa ya yi cikin dakin yana taku a hankali zuwa gare ni, hannayen sa duka biyu zube cikin aljihun wandon sa, kallo daya nayi masa naji tausayin sa ya kama ni, domin na ga ya fada sosai na alamun rashin kwanciyar hankali a tare da shi, sai karan hancin da ya kara tsini, ya tafi dodar ya tsaya a tsakiyar kyakkyawar fuskar sa. Almond – shaped eyes din sa, sun yi ciki sosai, sun dan kada, launin su ya canza zuwa brown, wannan dan sannu da zuwan da ya samu daga baki na yau shi ya bashi kwarin guiwar isowa gare ni.

Hannun sa yasa yana taba jikakken gashin nawa, ba karamin sha’awa gashin nan yake bashi ba, da lallashi a muryar sa yace “where’s your dryer? Can I help you with this (ina abin busar da gashin ki, zan iya taimakawa da wannan?) Yana nufin yana so ya busar min da gashin da kan sa”.

Fuska ta ba yabo ba fallasa, zuciya na son tuno min da kalamansi na jiya wadanda koda ya kasance cikin maye ya furta su na san yana nufin su har zuciyar sa amma ya zanyi tunda ni na saya aka sayar min dole in karba, da hannu na nuna masa inda take ajiye, ina mai kai zuciya ta nesa, ina kawar da kai daga duban sa.

Sai Hamza ya ja hannu na zuwa kan stool din mudubi, ban yi musu ba nayi yadda yake so, ya zaunar da ni, ya dauko dryer din ya jona ya hau steaming gashin nawa, daya daga abubuwan da yake so a cikin halittar Siyama kenan; gashin ta na asalin fulanin Mambillah yana kayatar da zuciyar sa. Ya yi wa Siyam alkawurra da dama wadanda har yau bai gama cika su ba, sabida sabon gap dindata saka a tsakanin su na rashin dalili da ta tsira. Daya daga abubuwan da na fi so a Hamzah kenan, duk da shortcomings dinsa musamman ta fuskar kula da addini wato kula min da gashi na da yake yi da kan sa (at his leisure times).

Ya gama busar da gashin da dryer din, ya kama shi ya tufke daga tsakiyar kai na, sai na koma cute kamar kankanuwar yarinya, ya saki jelar ta kwanto lambam a wuya na, ya dawo ya hada fuskokin mu wuri guda, yana sunsuna ta, karan hancin sa mai tsayi yana gugar nawa karamin hancin, goshin mu a hade da juna, hannayen sa duka biyun zagaye da kugu na, bakin sa daidai nawa kamar mai shirin sumbata ya soma magana a matukar tausashe.

“Kin daina fushin Siyam? Kin huce da ni? Kin ga ni ban san laifin dana yi miki ba. You are just punishing me for nothing. Jiyan nan jiyan I was…. I was…” (so yake ya ce he was drunk a jiyan amma ya kasa). Sai ya kifa kan sa a kafaduna ya soma hawaye. In ya tuna Allah kadai ya san irin zagin da ya yi wa Siyama sai ko ni kaina. “Ki yi hakuri Siyam ki yafe min don Allah.  Na yi alkawarin haka ba zai sake faruwa ba, in sha Allahu.

Yau za’a cire min filallika? Punishment din is too severe……”.

Hawayen da suka kwanta cikin idanun sa sun gama nuna nadamar sa koda bai furta duka ba. Na yi dan murmushin jin kunya, na russunar da kwayar ido na kasa.

Hamzah sai ya sumbaci saman idanun nawa, idon sa kan kirji na da suka tasa sosai kamar baloon. Yana mamakin Siyam da yadda har yanzu bata san cewa cikin ta ya fara girman da ya isa awo ba tayi tunanin zuwa fara antenatal, ban yi aune ba naji Hamzah ya zare tawul din jiki na ya sauke shi kasa, ya kurawa cikina ido kafin ya rungume shi, daga haka ya soma sarrafa ni ta hanyar da ya san zai samu contentment din da ya dade bai samu ba, (in the way and manner) da ya san bana iya kaucewa tayin sa.

Duk wani weakness dina a wannan fannin, ni na san Hamzah ya gama sanin sa ba tun yau ba. Kamar yadda nima na dade da gama sanin nasa.

Na soma tunanin kwace kaina ta ko ta halin kaka, duk da na san ba lallai in yi nasara ba a yanzu, don a irin wannan lokacin ba abinda zaka ce ko zaka yi Hamzah ya saurare ka, ko ya fahimce ka idan bay a samu nutsuwar da yake son samu ba, da na tuna bai fa yi sallah ba, in aka bibiya tun safe. Wani bakin ciki ya taso ya tokare min a wuya, amma sai na tuna nasihar Anty na Nasara, cewa maza irin Hamzah masu tsananin bukata ta nan kawai ake cin galabar su, maimakon tureshin dana yi niyya da farko,  sai na kara tunzura shi, ni da kaina na fidda kunya na zage ina seducing dinsa, na hana shi aiwatar da komai yau, ni ce ma nake jagorantar sa ta hanyar bashi ragamar abubuwan da ke gigita shi.

Sai da na tabbatar Hamzah ya kai makura ya kai kololuwa wajen bukatuwa, yayi min maraba da dukkan zuciya da ruhin sa, ya gama sakankancewa yanzu zai samu biyan bukatar da yake ta hankoron samu, sai na janye kai na, ba don ban yi kewar sa ba nima, sai don na riga na rantse babu ni babu Hamzah, tunda ya daina sallah! Kuma ya komawa giya, sannan baya wankan janaba. In fact kawai sai ince ya koma kafircin sa, a fatar baki kawai yake amsa sunan musulmi yanzu tunda kowa ya san banbancin musulmi da kafiri sallah ce da tsarkin jiki da na zuciya.

Ina mikewa toilet na nufa na maida kaya na a jiki na. Ba tare da na sake waiwayar sa don ganin halin da yake ciki ba. Ina jin sa da dakusassar murya yana fadin “Siyam yaya haka?” Muryar Hamzah ko fita bata yi saboda galabaita. Ya yi matukar gigicewa da wannan dandani haukacin na Siyama. Ba don na kasance cikin masu kyakkyawan ji ba, na tabbata da bazan ji shi bama.

Wata dabara ta zo min, maimakon in ce masa sabida baka yi sallah ba, ni kuma bazan iya auratayya da mijin da bay a sallah ba, sai na danne na cije nace. “Ka yi hakuri HAMZAH! Tunawa nayi ban yi sallahr Isha ba, alwallah zan yi.”

Hamzah sai yayi dif! Ya shiga lissafi cikin kwakwalwar sa. Abu biyu ne ya sa shi yin dif din, sunan sa da Siyam ta ambata garangatsau kai tsaye babu wannan sakayawar ta soyayya yadda ta saba, wanda ya tabbatar masa akwai magana mara dadi a kasan ran ta. Da kuma tunawa da ya yi shi tun safe ma ai bai yi sallahr ba. Kai ba zai iya tunawa bama yaushe rabon sa da yin sallah.

Na fara alwallah a toilet ina hawaye, Hamzah bai ce yayi riddah ba amma daina sallah ga wanda ya amshi musulunci da gaskiya yaya sunan sa? Bana so in yarda da tunani na cewa Hamzah ya yaudare ni da fake shiga musulunci don ya aure ni, tunda bai yi kama da masu fuska biyu ba. Ni Siyama yaya zan yi da rai na idan tunani na daidai ne? Bazan iya zama da wanda ya kasa tsaida sallah ba komin son da nake yi masa, alhalin yana ikirarin shi musulmi ne.

A wannan lokacin sai na tambayi kaina; auren Hamzah da na yi a matsayin tubabbe ‘Sakaci’ na ne ko na Young Abba ko kuwa abinda Anti Nasara ta taba hasashe ne ya ke tabbata?

A farkon haduwa ta da shi in ban manta ba Anti nasara ta yi rantsuwa kan Hamzah ba zai taba musulunta sabida ni ba.

Ta ce an yi dubu kafin ni, sai dai su matan su yi riddah, amma ba dai shi ya koma nasu addinin ba.

Ina alwalar ina hawaye, ina sharewa da tafuka na, na kasa tsayar da ruwan ido na, lokacin da Aunty Nasara ke cewa in yi hakuri a matsayin jigon zaman aure, cikin zama na da Hamzah dole watarana zan ga abinda bana so tunda tubabbe ne, jin ta kawai nake yi.

A gani na a lokacin son da nake yi wa Hamzah ya isa ya tare komai, ma’ana ba abinda zai yi da zai bata min rai ko ya sa na tsane shi tunda ya musulunta, amma wallahi yanzu ko ganin sa bana son yi, in na tuna baya iya sallah.

Na yarda nafi son addinin musulunci sama da Hamzahn VOA, kuma son da nake masa ne yasa bana so Allah ya azabtar da shi ranar gobe kiyama, ya tashi a sahun rafkanannu masu wasa da sallah wadanda Ubangiji ya saukar da surah guda a kan su, tunda ya tsallake sahun mushrikai ya yi shahada.

Sai ji na yi ya shigo toilet din, ya maida kofar ‘silently’ ya rufe, jin shesshekar kuka na ya yi daga daki inda na baro shi a kwance, kukan dana kasa rikewa ya soma fitowa fili duk da kokarin rike shi dana ke yi cikin makogaro na har Hamzah ya jiyo.

Fitilar bandakin dana kashe Hamzah ya kunna, towel dina na dazu ne daure a kugun sa, da mamaki yace “kukan me kike yi haka? Siyam har ta kai mu ga haka? Kina kullace da ni irin haka a kan laifin da bansan na yi ba amma ki kasa fitowa fili ki gaya min in gyara? Is this the kind of love we believe in? Sai ki bar a bin a ran ki yana cutar da ke? Shin Siyam ko kin daina so na ne yanzu? Ko kuwa kin gaji da zama da ni ne?”

Idanuna jike da hawaye sun kada sun yi jazur na dago kaina na dube shi da su cikin ido, wani abu da ba kasafai nake yi ba wato kallon Hamzah cikin idanun sa.

“Mai yuwuwa ne duka abubuwan da ka zano din haka ne! (Na daina son ka, na kuma gaji da zama da kai), ba kuma don ka yi min laifin komai ba, wannan tsakanin bawa da Ubangijin sa ne”.

Sakin baki yayi cikin kaduwa da mamaki yana kallo na da tsoro, jin yau inata cewa HAMZAH gaba-gadi, sannan murya ta babu wannan taushin da girmamawar dana saba yi masa magana da shi a kowanne lokaci.

Yau da kakkausar murya nake ta fada, har da zaro jikakkun idanu na waje. Duk da Anty tace wai lallashin sa ya kamata in yi na ji bazan iya lallashin ba domin ya kawo ni makura. Shi karamin yaro ne da za’a lallashe shi yayi sallah wadda itace zata tserar da shi a lahirar sa? Alhalin yana ikirarin shi cikakken musulmi ne a yanzun?

Ya tako zuwa cikin toilet din ya kama kafaduna duka biyun ya girgiza ni da karfi, ya ce “what have gotten into you Siyam a kwanakin nan, kina cikin hankalin ki kuwa? Ko kin yi gamo ne? ni Hamzah yau kike cewa kin daina so kin gaji da zama da ni?

Na kasa gane inda kike dosa, kina ta sa ni a duhu, kawaici na ya fara karewa da sababbin halayen da kika kirkira, kike azabtar da ni da su, alhalin ban san laifin dana yi miki ba” na ce “ka san Dawanau ta garin Kano? To ita ce a kaina bakidaya Hamzah!” Hawaye suka biyo bayan furuci na. Sai Hamzah ya sassauta tone din sa, cikin sanyin murya ya ce “follow me, please Siyam”, tare da janyo hannu na ta karfi muka fito daga ‘toilet’ din.

A gefen gadon mu ya zaunar damu, kafin ya janyo ni ina hawayen ina komai ina tirjewa ina ture shi, da karfi ya rungume ni a kirjin sa tsam-tsam, ya ce “Siyam, na san ruwa ba ya tsami banza, haka kawai Siyam bazata taba cewa ta gaji da ‘dream husband’ din ta ko ta daina son sa ba, sai bisa babban dalili”.

Cikin tsokana Hamzah ya kara da cewa, “ni ne fa Hamzah-Mawonmase Dream Husband din siyama, ni ne wanda aka sha ‘poison’ a kan sa alhalin ko sani na ba’a yi ba, tun gabanin a san ni mummuna ne ko akasin haka, mai sallah ne ko mara sallah, aka bata da Abba da matsoraci (Ya Omar) duk saboda ni, a tunanin ki akwai abinda zai sa wannan son ya jijjiga ko ya kwaranye cikin ‘yan watannin da har yau basu kai ga cika shekara ba babu wani dalili?

Ai sai dai ki fadi hakan (out of frustration) din wani bacin ran dana saka ki ba tare da na sani ba.

Ki yarda da ni, Hamzah&Siyam are meant for each other. Ours is made from the heaven!!!”.

Maimakon in ji kalaman sa sun min dadi, kamar yadda suke tafiya da ni da Imani na a baya, musamman idan na tsinci kaina a kan ingarman kirjin sa irin haka, yana rungume da ni, yana shafa kwantaccen gashin kaina da baya gajiya da shafar shi, yana rada min kalaman a cikin kunnuwa na kamar dai yadda muke a halin yanzu, sai na ji kalaman nasa sun rikide sun sake koma min GORI mai zafi fiye dana jiya, kamar Hamzah yau GORIn nasa na cikin ruwan sanyi ne yake mun ba irin na jiya na keke-da-keke ba, a yadda kwakwalwata ta fassara min.

Wannan ya kara dugunzuma fushi na, na shiga bugun sa kota’ina ina kokarin kwacewa daga cikin rikon sa amma ya ki cika ni, ina kuka wurjanjan ina fadin “dole kayi min gori, kana da dukkan damar yi min shi, nima na yarda ni wawuya ce, wadda ta zabi soyayya a kan ubanta, kaico na!”.

Hamzah kyale ni yayi, na yi har na gaji ba tare da ya sake ni ba, ba kuma tare da ya nuna yana jin zafin dukan dana ke masa ba, ba tare da ya raba ni da kirjin sa ba, sai da na bari don gajiyar kaina, kasancewar karfin mu ba daya bane.

Harshen sa na ji yana sauka a saman kunci na, yana dauke hawayen fuskata, yana side kuncin bakidayan sa affectionately. Kafin ya soma magana cikin tsananin damuwa.

“Kin sani Siyam, ajiye damuwa a zuci baya maganin ta, baya kawo maslaha a cikin zamantakewar aure, ‘we must be open and straight forward to each other’ in muna son kwanciyar hankali a rayuwar mu. Don Allah Siyam in laifi nayi miki kiyi hakuri ki gaya min, I’m tired of your silent punishment!”.

Ya dora hannu na a kan kirjin sa, daidai saitin da zuciyar sa take harbawa, ya ce “ki ji yadda ta ke bugawa da wannan gashin kumar naki. Da azabtuwar fitar hawayen ki. Ni ban damu ba, ba kuma zan damu ba don mun shekara bamu hada shimfida ba, domin ba abinda ya assasa auren mu kenan ba.

Soyayya ce ta hakika ta fisabilillah a tsakaninmu, wadda itace jagorar komai, na damu ne sabida sabida nasan bazan yafewa kaina bai dan na bata miki bias sani na, na damu ne don na san na yi miki laifin da kika kasa tara ta gaba da gaba ki fada min. Ki ka zabi ki hukuntani ta hanyar cirewa zuciyar ki soyayyata wadda ba ke kika sanyata ba, Allah ne.

I think ko menene ki gayamin yanzunnan zai fi, tsakanina da ke babu ‘yar haka kin ji SIYAAMA! Wallahi na horu, na kuma yi alkawarin dainawa ko menene.” Ya kara kankame ni. Jikin sa yana shaking.

<< Sakacin Waye? 47Sakacin Waye? 49 >>

1 thought on “Sakacin Waye? 48”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×