Skip to content
Part 52 of 73 in the Series Sakacin Waye? by Sumayyah Abdulkadir (Takori)

Girgiza kai na shiga yi da sauri hadi da zaro idanuwa ina kallon sa cikin tsoro, da firgici da kaduwa, kallon da na gani cikin idanun sa ya tabbatar min yana nufin kalaman sa, na cewa in bai sha giya ba a halin yanzu zai zautu, na dauka mun dade da baiwa maganar giya baya, na dauka Hamzah ya bar komai da ya danganci sabon Allah da wasa da addini daga ranar da yayi min alkawarin canzawa, ya kuma canza din, ni kuma na kuma karbi tuban sa da dukkan zuciya ta?

I will no more accept his “zan bari, amma a hankali, na gaji da jin kalmar “zan bari amma (gradually)”, na gaji da wannnan statetment dinnan na rashin hankali.

Ba wannan ya fi tayar min da hankali ba kamar maganar da ya yi yanzu a kan iyaye na (Young Abba). A cewar sa ya tabbata maraya gaba da baya a yanzu, in bai sha giya ta tafi da damuwar sa ba zuciyar sa zata buga ya fadi yanzun nan ya bi bayan Kakar sa.

“Duk me ya jawo?”

Ban san lokacin da na tambaye shi ba curiousity na neman fasa mun kai.

“She did everything good to me a duniya, everything to build my future for good, amma sakamakon ta shine na saka mata da betrayal, na canza addini na, na guji kabila ta, na yi aure duka babu yardar ta, sabida son dana samu kaina ina miki farat daya, da son cika mafarkan ki su zamo gaskiya, da son cika nawa burin na auren macen dana ke so kadai,  ba wadanda suke so na ba har suke willing su bar nasu addinin zuwa nawa.

Ni nawa na bari sabida naki, sabida ke nake so, wanda bakin cikin hakan dana aikata ya aika da ita barzahu, bayan duk duniya ita kadai ta san ciwo na”.

Saura kadan in yi fitsari a wando na sabida yadda kalaman Hamzah ke birkita ni. Ni na san dama akwai wata irin shakuwa mai tsanani tsakanin sa da Kaka, na san rashin ta will touch him in every way amma ban zaci wadannan kalaman na gushewar Imani daga bakin sa a daidai wannan lokacin ba.

Ina sane da cewa, duk da ya rasa iyayen sa tun yana karami Kaka ta sa Hamzah bai san kalmar maraici tana existing a duniya ba, saboda ta maye masa gurbin iyaye dana kakanni gabadaya, a cewar sa yau gatan sa ya fadi!  Tunda ya rasa Grandma din sa, ba tare da ta yafe masa laifukan da take tuhumar sa da aikata mata ba, ya fara ganin hakkin ta a kan sa.

Gashi ni din dana yi masa sanadin rasa ta; Young Abba ya ce masa lallai mu tsaida haihuwa, don kada mu yi ta haifar ‘ya’ya sikila ko carriers, harda bashi misali da abokin sa mai arziki ne sosai, amma yanzu sabida hidimar sikilolin yaran sa hudu sicklers bashi da komai yanzu,  shi (Young Abba) ba zai yarda Siyam ta haifi sikila again ba kada ta kawo musu ‘sickle cell’ a family din Ummati, don amana ce ita ta mahaifin ta a hannun sa. In ya so zai taimaka mana muyi adopting yaro ko yarinya daga orphanage ko cikin dangi na na wajen uwa daga kauyen Gashaka.

Hamzah ya share zufa daga goshin sa, ya dube ni da budaddun idanuwa ya ce “Me Baban ki (Young Abba) yake nufi da wannan maganar? Da har zai kira ni officially ya gaya min hakan? Ba tare da ya yi la’akari da halin rashi uwa/kaka ta da na yi ba, zai kara min da wannan bakar maganar ta son kai da rashin kauna? Banda in disguise yana nufin yace yana son raba auren mu kawai?

Me yasa ma kika gayawa Abban sirrin ‘genotype’ din mu, wanda daga ni sai ke sai Ubangiji sai likitan mu muka san wannan maganar?”

Maganganu dai rututu irin na wanda ke cikin bacin rai har ta kai shi ga yake neman rasa imanin sa da hankalin sa, ya kuma manta dukkan tarin kaunar Young Abba a gare shi. Yau daya don ya bata masa rai ya juyar da alkhairin sa, ya kalli maganar sa ta wata fuska daban, da wata manufa daban, don haka na kasa kare manufar Young Abba da nawa laifin da yake tuhuma ta na fadawa Nasara, ita kuma farfesa ta fesawa mijin ta.

Karo na biyu dana ga Hamzah ya zauna a gefe yana kuka riris. Bayan kukan komawar dan sa. Sai jiki na ya dau rawa. Na kama kafafun sa cikin tashin hankali na ce “kayi hakuri Hamzah, ni fa ban fada masa ba da Aunty kawai na yi maganar nan, ka san dai ba abinda zan iya boye mata da ya shafe ni balle Magana mai muhimmanci irin wannan, mai yiwuwa ita ta fada masa, shi dama Young Abba dan boko-akida ne fa, kai ne baka sani ba, kullum tunanin sa na yahudawa ne, ni ko zan yi ta haifar ‘ya’yan suna mutuwa washegari, na yarda duk shekara in dau sabon ciki in haifa maka ‘ya’ya su zame mana na amfanin can, babu wani adopting da zamu yi namu zamu haifa mu rike.

Yana daga cikin shika-shikan Imani yarda da kaddara Hamzah, mai dadi ce ko mara dadi, barasa bata maganin maraici ko damuwa, kuma bazata sa Kaka da Baby su dawo duniya ba, haka bazata canza kalar jinin dake cikin jikin mu ba, idan ka sha ta gurbata imanin ka kawai zaka kara yi yanzu. Musamman a wannana lokacin da shaidan ke son taka muhimmiyar rawa a zuciyar ka. Yana ta kada maka ganga kana hawa a kan Young Abba.

Ka tuna alkawarin da ka yi min Habeeby-Shaheedy, da kuma wanda ka yi wa Young Abba na cewa bazaka kara sha ba kafin ya yarda ya baka aure na”.

Murya ta ta karye, nima kukan ya kece mini da karfin sa, na ce “na gama yi maka uzuri akan shan giya da wasa da sallah daga yau wallahi”.

Hamzah ya gyada kai. Sai cewa yayi “zaki fadi haka mana tunda ke kina da iyayen da suka san ciwon ki, har suke guje miki haihuwa da ni yau, wadanda basa so ki haifa musu jika sikila, sabida ke suke so ba ni ba, kuma zasu iya raba mu su aura miki wani mijin ki samu ‘ya’ya masu lafiya musamman dan uwan ki OMAR wanda na lura har gobe hankalin ki bai bar kan sa ba, balle yanzu da ya kasance ni jini na na haihuwar marassa lafiya ne.

Kuma ai na dade da sanin cewa don shi (Omar) kike son komawa Nigeria, to har abada ke da kasar Najeriya, daga kasar Amurka zamu lula mu shiga uwa duniya mu rayu tare, daga ni sai ke a inda babu kowa!

Ya zama bani da iyaye kema baki da su, in ya so mu yi ta haifar ‘ya’ya sikila kada mu tara komai din. Kada mu kai muku su cikin family. Tunda hakan kuke gudu. An gaya muku ni duniya da tara arzikin cikin ta yana gaba na ne ko ya fiye min ‘ya’ya na?

Ba zan ce na daina sallah ba, but ba zan taba barin giya ba. Ki karbi wannan assurance din ki saba da shi sai ki zauna lafiya. Life is not fair to me at all! In ban sha giya ba hadiyar zuciya zanyi?

Kakata babu, dan da na kallafawa rai ya zo min ko a sikilan ma, babu!.

Kuma dole ki zauna da ni har abada a inda bamu da kowa tunda kin janyo ni cikin kaddarar ki, kin girma kina rokon Allah ya hada kaddarar mu, Allah ya amshi dukkan rokon ki ya dabaibaye zuciya ta a kan ki, sai don kaddarar mu ta zo da lalura zaku yi min halin ku na hausawa na kabilanci da ‘yan ubanci, koda ‘ya’ya masu kanjamau zamu yi ta haifa ba masu SCD ba Siyama yanzu muka fara aure, kuma yanzu zamu fara haihuwa. Wannan sako na ne ga Young Abba da nake rokon ki isar da shi gare shi”.

Ya mike ya janye kafar sa dana rike daga hannaye na, ya dau mukullin motar sa da sassarfa ya fita, ya bar ni da budadde kuma sakakken baki. Ina cikin tantama da tababar anya HAMZAH na ne wannan?

<< Sakacin Waye? 51Sakacin Waye? 53 >>

2 thoughts on “Sakacin Waye? 52”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.