LITTAFI NA HUDU
Rana ta farko kenan da Hamzah bai kwana a gida ba tun auren mu, kazalika rana ta farko da muka raba shimfida zukata a bace, sakamakon ran kowa na tafarfasa ne da fishi da bacin ran dan uwan sa. A can baya ina yin fushi da Hamzah a lokuta da yawa idan ya bata min rai amma sai dai ni in yi fushin nikadai, in huce a sanda nake so, zai kuma rarrashe ni iyakar rarrashi ta duk hanyar da zai iya. Idan ya kasa rarrashi na ya shiga matsananciyar damuwa kenan da ko abinci ba ya. . .