Skip to content
Part 53 of 73 in the Series Sakacin Waye? by Sumayyah Abdulkadir Takori

LITTAFI NA HUDU

Rana ta farko kenan da Hamzah bai kwana a gida ba tun auren mu, kazalika rana ta farko da muka raba shimfida zukata a bace, sakamakon ran kowa na tafarfasa ne da fishi da bacin ran dan uwan sa. A can baya ina yin fushi da Hamzah a lokuta da yawa idan ya bata min rai amma sai dai ni in yi fushin nikadai, in huce a sanda nake so, zai kuma rarrashe ni iyakar rarrashi ta duk hanyar da zai iya. Idan ya kasa rarrashi na ya shiga matsananciyar damuwa kenan da ko abinci ba ya iya ci. Amma na yau ya banbanta dana kullum, akasin da aka samu shi ne shi Hamzahn ke fushi, har fiye da wanda ni nake yi.

Ita ce rana ta farko da ya kwana a ‘Bar’ a tarihin rayuwar sa gabadaya har kuwa da sanda yake cikin addinin christianity, ji yake kamar shi kadai ya saura a fadin duniya, kamar yana gab da rasa Siyama; wata kwayar mutum guda daya wadda ta zamo masa barin rayuwa kuma cikon farin ciki, ta maida rayuwar sa cikakka mai ma’ana ta fuskar addini da mutuntakar aure, tun farkon rayuwar sa har girman sa bai taba kwana a ‘bar’ ba sai yau. A tunani na Hamzah yayi hakan ne don ya bakanta min, ya bani haushi, ya saka ni a bacin rai da damuwa irin wanda Babana Adamu ya saka shi, amma a Zahiri damuwar Hamzah ta fi gaban nan tunda dama yana cikin alhinin rashin Grandma, don bai taba kawo mata mutuwa a wannan lokacin ba yana mata kwadayin musulunci ne idan ta gama tambotsan ta, ga kuma damuwar rashin Babyn mu da ya kallafawa rai, ya sakawa burin ya zo ko a sikilan ne yana son abun sa, ga kuma fargabar kada a raba shi da Siyam a dalilin genotype, wadannan su suka taru suka hade da bacin ran maganar Young Abba, ta kada ya kara haihuwa da Siyama su yi adopting Da daga dangin ta na Gashaka, even in Christianity Hamzah Mawonmase na kan ra’ayin kamun kai, wato kame kan sa daga abubuwan zubar da mutunci irin kwanan bar, su clubbing da sauran su, ya kan je ‘bar’ don sayen barasa kadai tunda kamar ta zamewa Beroms farilla amma ba ya zama sam, ko in ya iso gida ya gama uzurorin gaban sa yana son abinda zai dauke masa hankali daga tunanin aure sai ya kara fita ya sayo ya dawo, sai ya zauna nan a babban falon sa yayi mata shan nutsuwa. Wannan ita ce rayuwar Hamzah Mawonmase a baya.

Ya kasa yarda Young Abba da ma mahaifin ta Dr. Mamman Gembu zasu yarda su bar masa ita sabida matsalar genotype. Tunda har Adamu ya fara da saka dokar haihuwa da adoption.

Rashin kwanan sa a gida ya sa na shiga tashin hankali mai girma, domin bai taba yin haka ba duk irin fadan da zamu yi. Ba abinda zuciya ta bata kissima min ba na cewa abinda yake aikatawa kenan a fitar da ya yi wanda nake da yakinin ko me yake yi a hain yanzu na sabon Allah ne bisa jagorantar fushin zuciya da linzamin shedanin da ke ingiza shi, wanda yayi alkawarin sarrafa mutum da zuciyar sa, a lokacin da yake cikin fushi, zuciya ta ta shiga gaya min watakila har karuwa (prostitute) yau Hamzah ya ja daki yau duk da ya cikin policy din sa, zuciyar kishin Hamzah kuma ta ce ko ya koma wajen ‘yan matan sa irin su Suhaila Barkindo sai kuma na tuna ya taba ce min ta bar Amurka da jimawa sakamakon sauyin wurin aiki da akayi wa Baban ta zuwa Misissipi, tunda a cewar sa iyaye na sun kware masa baya sai nake tunanin ya tafi inda zai huce takaici ne ta hanyar da ya san zai bakanta min rai wato rashin kwana a gida, haka dai na yita kissime-kissime marasa kai bare kafa duk a dalilin na damu da miji na, tsoron abinda zai iya kwaso min yau in ya kwana da karuwa ya kara lullube ni, ga kishi mai tsanani. Gani da tsananin kula da lafiya ta, da tsarkin addini na da rashin son raba miji na da kowa. Na yarda soyayyar da nake masa da shakuwar da ke tsakanin mu su ke saka min damuwa irin haka, damuwa ce irin ta kowacce mace a kan mijin ta da take tsananin so idan ya ki kwana a gida ya kwana a waje.

Wajen da take da tabbacin na hatsari ne kuma na sabon Ubangiji, ba cikin iyalin sa ba, wannan wani sabon sauyi ne da Hamzah ya kawo mana wanda zuciya ta taki aminta da shi, kuma son dana ke masa ba irin wanda zai jure kwanan sa a waje bane.

Ko mun yi fada zamu kwana daki daya, yana jin numfashi na ina jin nasa, muna samun contentment na cewa tare muke dai a makwanci guda, idan ya huce in ya ga na yi barci sai yazo ya nanike ni, wanda ya saba hakan in har yana so a shirya kuma ba ya son doguwar magana da dogon roko a kan neman shirin, sai dai kawai in ji shi ya mirgino ya manne mun, ta nan zan gane neman shiri ya ke, ya gaji da biye fushin nawa, amma duk rintsi ko sabanin da zamu samu ko daki bama iya rabawa.

A dabi’ar sa ma baya kwana a dakin sa sai nawa, sabida yace ruhin sa a nan yake, muna shiri ko bama shiri Hamzah ba ya fasa kwanan daki na. Akwai ranar da ya ce min shi ko mutuwa ya yi, ya fi son a binne shi a daki na. Sai ko ranar da Kaka ta zo. Da na bar mata dakin nawa nayi kaura na koma nasa dakin. In ma yayi fushi ya fita falo ba’a jimawa zan ji shi ya shigo sadaf-sadaf ya kashe wuta, ya lallaba ya shige cikin duvet ya kwanta a gefe na. “Allah sarki Hamzah!”

Yau Hamzah sai dai filon sa a space din sa da ya saba kwanciya. Mai dauke da kamshin ‘guerlain vetiver’ ta ko’ina a jikin sa, kamar sai da ya feshe wajen da shi kafin ya fita, a kan laifin da ba nawa ba duk wannan ya kare a kai na. Tunda sanda Young Abban ma ya kira shi suka yi maganar su ni ban sani ba. Sai ganin sa da nayi afujajan a kai na wai zai sha giya in ba haka ba zai zautu, yana maganganun dana kasa gane kan su bare kasan su, irin na wanda ya fuskanci rejection daga wadanda ya yarda da su, ya amince masu kaunar sa ne da zuciya guda. Koda yake ya ce ni na jawo, tunda ni na kasa rike sirrin mu na tona har Young Abba ya sani, dana kasa shiru na fadawa Nasara sabida kaikayin baki na.

Damuwar tawa a kan rashin kwanan sa gida yau ta tabbatar ba zan iya rayuwa cikin sukuni ba tare da Hamzah ba, son da nake masa a cikin jini na yake, sannan bayan auren mu ya inganta son, ya raine shi, ya girmar da shi, yayi ta ririta shi har ya yi nunar da na kasa kwana a gadon auren mu yau sabida babu shi, domin ji nake kamar ya tsinke min zuciya ya tafi da ita, ya riga ya zame min bugun numfashi, in babu kai babu rayuwa.

Saboda Allah meye laifin Young Abba don kawai ya ce mu tsaida haihuwa? Shawara ce, ba dole yake yi mana ba, Hamzah na da damar ya dauka ko ya bari, gyara kayan ka baya taba zama sauke mu raba. Iyakaci da sai ya bude baki ya ce bai amince da shawarar ba, kaddarar mu ce ta zo a haka, ba kuma wanda ya isa ya sauya kaddarar sa, (idan baya bukatar shawarar kenan), tunda ba jikin sa bane ba aljihun sa bane shi Young Abban. In fact, ba cewa yayi zai raba mu ba.

Zan iya rantsewa kan cewa Young Abba tsakanin sa da Allah ya fadi wannan maganar, ba don ya bata masa rai ba, ko don baya son hada jini da shi, saidai kuskuren fahimta, saboda da dukkan zuciyar sa yake son Hamzah wani irin so kamar kanin sa, wanda har Anti Nasara ke kishin son da yake masa, bana jin wata lalura irin haka zata sa yace wai zai raba auren mu, a hakikanin gaskiya ma ya hada auren ne domin ya tallafawa soyayyar ba don ya zalince ta ba. Ina tunanin ya fada ne domin ya nemo mana maslaha ga rayuwar yaran namu da cirewa kai wahala (a ganin sa, a kuma irin tunanin sa na ‘yan boko).

Young Abba mutum ne mai tsananin kirkin gaske, kai dai bar shi da boko-akidar sa, wanda a kullum shi ke hada shi fada da mutane masu sahihi kuma saitaccen tunani na addini da dayanta Allah da bar masa komai.

Da can bai san da Omar din bane ya dage ya bashi ni ko yaya? Ko bai san Omar din shima dan sa bane? Amma yah ana shi ya bashi ni? Har ya yarda ya bata da dan uwan sa shakikin sa da ya haife ni, ya tsaya tsayin daka ya tabbatar da soyayyar mu ta samu damar actualizing ta hanyar aura mana juna?

Shi Young Abba in an fahimce shi kullum tunanin turawa kawai gare shi. Banda wannan bai da wata matsala ba ya rike kowa a rai. A wurin bature da a haifi wahala gara ba’a haifa ba tun farko, mu kuwa addinin mu bai yi mana wannan horon ba. Ya hore mu ne da karbar kaddara da Imani da ita. Mun sani Allah shine mai rayawa kuma shine mai kashewa, shine mai azurtawa kuma shine mai talautawa ga wanda ya so. Rayuwa da mutuwa duka suna hannun sa, bawa bai isa ya kaucewa abinda Allah ya rubuta masa ba duk dabarar sa. Mutane dubu nawa dake da cikakkiyar lafiya ne suka fadi suka mutu mutuwar fuju’a, suka bar masu cutar SCD (Sickle Cell Disease) a raye a duniya???

Na fi yarda cewa mutuwar kowanne yaro da kowanne babba lokaci ce.

A gani na Hamzah ya dauka da zafi da yawa, watakila don dama yana cikin zafin rasa Kakar sa da Dan mu da ya kallafawa rai, sai Young Abba ya zo yayi sara a kan gaba, ko in ce ya zubawa wuta fetur, don  na tabbata ba manufar Young Abba kenan ba, Hamzah ya manta idan hankali ya bata, hankalin ake sawa ya nemo shi.

Na yi ta kiran wayar sa amma tanata ringing ya ki dagawa. Na yi masa text wanda bana tunanin ya karanta ma. Babu amsa babu alamar Hamzah ya gani. Dare ya tsala, na zama kamar wata zautacciya na figo mayafi na fito harabar gidan mu, da niyyar tafiya neman Hamzah, na manta girma da fadin babban birni Washington D.C da yawan mashayar barasa dake garin, ban san ta ina ma zan doshi neman nasa ba, I’m just absent-minded on my huband’s whereabout, ga daya motar tasa a fake a ma’adanar ta, amma abun takaicin ban iya tuka mota ba balle in je neman sa, ban san halin da yake ciki ba na kuma tabbata ba zan iya barci ba a dalilin hakan, na fi kyautata zaton yana mashaya (Bar). Kyankyamin sa da gayun sa na halitta bazasu bar shi ya iya neman matan bisa titi (black Americans matan club) ko na turawa ba. Na yi masa wannan shaidar har a gaban Allah.

Sai na dauro alwallah kawai na zauna ina hailala, ina yi ina kuka, ina rokon Allah ya inganta imanin miji na abin so na, kada bacin rai da zafin rasa Kakar sa da Dan sa ya gusar da dan burbushn imanin nasa da Allah da nake ta tattali da riritawa.

Washegari da safe (fully intoxicated) na gan shi kwance a babban falo yana barci sadidan, kamar an zare ran sa banda kirjin sa da yake dagawa a hankali. Kuma a hakan, wai a yau zai tashi zuwa Najeriya da gawar Kaka (for burial). Ko kuwa ya fasa tafiyar ne ko ya manta ban sani ba. Nasa hannu na shafe hawayen da suka tsatstsafo min, wai miji na ne wannan mashayin ni Aisha-Siyama, ko in ce; mijin da na zabarwa kai na ko ko ince, kaddarar rayuwata take cikin tasa. Ni Siyama wadda ko mashayin sigari bana kauna, (wato in da abunda ‘yan kabilar Birom suka rika da muhimmanci babu irin shan giya, musamman a lokacin bacin rai, sun yi amanna ita kadai ce maganin damuwa da yayewar bacin rai a garesu, sai yanzu na san zai yi wuya Hamzah ya iya barin giya (as long as) yana ganin ko jin abinda zai bata masa rai, ko abinda zai daga masa hankali.

Ni kuma na yi rantsuwa bazan zauna da shi a haka ba, sai dai son ya yi ajali na. Canji na kwatakwata nake so ba na gradually din sa da bata karewa ba. Da dai in haifi ‘ya’ya watarana su tambaye ni, a lokacin da bani da amsar basu idan suka ce “Mama meye dalilin zaba mana Uba mashayin giya? Bayan kasancewar sa tubabbe? Bayan asalin su da na gurbata daga tsatson wankakkun fulanin Mambillah da kabilar Birom arna makiya musulunci da musulmai???

Kallon bakin ciki nake yi wa Hamzah yau, abinda ban taba yi ba tun aure na da shi, ba wai don na ji na tsane shi ba, ko don na daina son sa sabida abubuwan da ya yi min daga jiya zuwa yau, hasali ma ban taba jin tsanar sa ba kome zai min, ko sanda na fahimci ba musulmi bane Christian ne ban tsane shi ba, amma na rokawa kaina tsari daga auren sa da soyayyar data yi wa zuciya ta katutu, sannan soyayyar ta zama under control dina ba kamar da farko ba da bana iya sarrafa kai na a kan sa.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 2 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Sakacin Waye? 52Sakacin Waye? 54 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×