Skip to content
Part 54 of 73 in the Series Sakacin Waye? by Sumayyah Abdulkadir Takori

Ban taba bakin ciki da auren Hamzah ba, kuma har abada bazan yi ba, don na yarda Hamzah Mustapha (Mawonmase) yana cikin kaddarata ne. Ba Abba na ba, ba wani mahaluki ba, irin wannan rubutaccen auren namu tamkar ZANEN DUTSE ne, jayayya da afkuwar sa zai iya tafiya da rayuka don tabbatuwar sa, auren da tun ban balaga ba na san da afkuwar sa da suffar mijin kan sa da muryar sa cikin wata qudura da iradar Ubangiji, na girma tare da shi ina mai ganin sa cikin mafarkai na dare da rana, don haka na amince Hamzah kaddarata ne, matar mutum Hausawa suka ce kabarin sa, tun kafin ya zo duniya an riga an rubuta masa a Lauhul-Mahfuz haka mijin da mace zata aura. Kenan in reality Hamzah ba zabi na bane, rubutaccen miji na ne. Kuskure na shine kafiya, taurin kai ga mahaifi da rashin barwa Allah zabi. Amma da na yi hakuri na yi wa Abba biyayya a ko’ina nake tunda akwai rabo a tsakanin mu Hamzah zai zo ya tadda ni har inda nake tunda allon da ba ya kankaruwa ya riga ya rubuta aure, musuluntar sa ta sanadi na da haihuwa a tsakanin mu. Don haka yanzu nasa a rai na aure na da Hamzah Jihadi ne. Ubangiji ne yake so na da yin jihadi a kan rayuwar sa gabadaya ta hanyar sanya min matsananciyar soyayyar sat unban san kai na ba, ba son zuciya ta bane son da na kewa Hamzah, ba kuma yin kai na bane kawai dai nayi SAKACI wajen biyayyar iyaye. Har ila yau, babu wata kawar zuciya a tare dani wadda ta sa na dage sai Hamzah, ko rasa rayuwa ta.

Lokacin da ya bayyana gare ni a ba musulmi ba, ai na yi duk kokarin da zan iya don gujewa auren sa Allah bai bani iko ba, saboda akwai dalilin shiriyar sa da Allah ke son sanyawa a wuyana, haka da na yi ilmin addini nayi kokari mai yawa na yaki zuciya ta a kan sa, maganar guda daya ce bata kai biyu ba; a cikin dukkan addu’o’ina ban taba addu’ar zabin Allah ba sai nawa zabin shiyasa Allah ya bar ni da zabin nawa, ya kuma soma jarraba ta a kan sa.

Allah ya riga ya rubuta mu matsayin mata da mijin da zasu rayu tare, ya sako shi cikin rayuwa ta domin in ceci wannan bawan nasa mai kyakkyawar zuciya, mai kuma rauni a halayya da dabi’a, in fito dashi daga tsananin duhu zuwa hasken rayuwa wanda shine addinin musulunci, shi yasa ya sallado shi cikin mafarkaina masu kama da ido biyu.

Kenan Abba (is lucky) da ya kasance yana nan a raye aure na da Hamzah ya wanzu, wato an yi yana raye rabo bai kawar da shi daga doron kasa ba, an kuma haifa yana raye, duk da bai ga dan ba ya koma, nagode Allah da yasa rabon ‘ya’yan Hamzah dake jiki na bai kau da Abba na abin so na daga doron duniya ba.

Ina so duniya bakidaya da ke karanta labari na ta yi min uzuri da cewa ba yin kaina bane kaddarar da ta same ni, duk da cewa ni na zabawa rayuwa ta irin mijin da nake son samu nake kuma mafarki, tunda ba wani kyale-kyalen Hamzah ne ya ja ra’ayi na gare shi ba. Karewa ma, ban taba ganin sa a zahiri ba sai bayan dana hakura da shi.

Ya kamata kowa yayi min uzuri iyaye na su karbi hanzari na, duk da na yi kuskure na yi wa mahaifi na tirjiya, taurin kai da jayayya. Babban kuskure na da bazan gushe ina neman rahma da gafarar Allah a kai ba shine neman rai na da na yi ta hanyar shan guba, wai don in samu hanyar tsira da mafarkai na da burika na, alhalin inada masaniyar makomar da Allah ya alkawartawa wanda ya kashe kan sa da gangan.

Ina rokon Allah ya yafe min wannan gangancin, kada ya kama ni da wannan kuskuren nawa, zan kuma tabbata Abba na ma ya yafe min da dukkan zuciyar sa koda wannan shine abu na karshe da zan gabatar a rayuwa ta.

A yanzu na saka a rai na jihadin dana yiwa addinin musulunci na kawo Hamzah cikin sa, shi nake cigaba da yi, zan kuma cigaba da kokarin yi (against all odds) don ganin ya amsa sunan sa mai asali na sahabin Ma’aiki (SAW) Sayyidina HAMZAH ya kwaikwayi halaye da dabi’un da zasu sa watarana a kira shi “good and pious Moslem HAMZAH”, ta hanyar yin koyi da mai sunan sa Shaheedi Sayyidina Hamzah Bappan Annabi SAW, na kuma tabbata lada na na wurin Ubangiji; ladan aure da ladan jihadi, wani ya shiryu ta hanyar ka ya fi a baka jajayen Rakuma.

Zan ajiye Soyayyar daga yau a gefe, zan fuskanci gyaran dabi’un miji na ta hanyar kaurace masa. Struggles dina na son ganin Hamzah ya zama mutumin kwarai, Uba na gari ga ‘ya’yan sa, miji abin alfahari ga musulmar mace, kuma mijin da nake so da zuciya da ruhi na, da yardar Allah ba zai tashi a banza ba.

Rashin biyayyar dana yi wa Abba na kuwa gashi tun ba’a je ko’ina ba, tun auren bai shekara ba ina ta ganin sakamakon sa a kwaryar sha na tun a duniya. Tunda Hamzahn da kan sa ya goranta min kin bin iyaye a matsayin babban zunubi wanda ko shi dana ke yi wa kallo da daukar tsohon kafuri bazai yi shi ba, Hamzah yayi min wannnan gorin ta inda ban taba tsammani ba. A kuma lokacin da ban zata ba.

Ina fatan dukkan consequences din rashin biyayyar dana yi wa mahaifi na su kare a kai na ni kadai, kada ‘ya’ya na su gaji taurin kai da kafiya da naci akan buri irin nawa. Da kuma jayayya da iyaye don ba inda zai kai su sai ga nadama da ganin abinda basu so a rayuwar su.

Amma na yanke shawarar daga yau saidai Hamzah ya zaba ko ni Siyama ko shan giyar sa. Ko zama cikakken musulmi ko rabuwa ta da shi. Wato ko ya daina ko in bar masa gidan sa. Kuma in na tafi na tafi kenan har zuwa ranar da ya shirya dainawa kwatakwata.

Jikin sa ne ya bashi watakila akwai mutum tsaye a kan sa, da kyar ya iya bude ido yana kallo na da idanun sa da suka koma kanana jajir, idanun sun yi ja matuka, sun kumbura sun kankance kamar an zuba musu barkono. A irin kallon dana ke masa ya san rigima ce fal nima a ido na, idan rigima da tada zaune tsaye yake ji na babu gaira babu dalili ya tara ya samu. Hamzah ko a jikin sa da irin kallon dana ke masa. Sai ma juya min baya da yayi ya cigaba da barcin sa.

Nace “ai baka ga ta ramuwar barci ba Mr. Hamzah, Allah wadarannaka ya lalace akan abun maye, bayan kwana a gidan giya da casino, da karasa dare a gidan karuwai, zaka zo kana min ramuwar baccin asara a falo, babu sallah baabu salati, tashi zaka yi ka zaba ko ni SIYAMAH ko shan giya”.

Hamzah ya yi wani miskilin murmushi daga kwance, yana lumlumshe ido irin na wanda ke kan gajimare yace “idan na zabi giyar me za’ayi?”

Hawaye fal ido na nace “sai in koma kasar mu gaban iyaye na, amma bayan ka bani a rubuce, don ba zan tafi da igiyar aure a kai na ba.

Wannan ba shine alkawarin da ka yi min ba Mr. Hamzah, kafin ka yaudare ni ka aure ni.

Ka yi alkawarin gyara tsakanin ka da Ubangijinka, ka yi alkawarin gyara tsakani na da mahaifi na, ka ayi alkawarin bani farin ciki, ka yi alkawarin zama mutumin kwarai, ka yi alkawarin taya ni neman Ya Omar, ko don Abba ya dubi hakan ya yafe mini, amma baka yi hakan ba, ba ka yi ko daya a cikin wadannan alkawurran da ka ambata min ba, sai ma kara nesanta ni da su da kake yi kullum.

Ka yi alkawarin barin giya amma kullum kara dulmiyewa kake a cikin shan ta, kara ninka soyayyar ka da ita kake yi.

Kayi alkawarin tsaida sallah amma na tabbata ko yau baka yi sallar asubah ba.

Kana tunanin na fi son ka a kan addini na ne? Ko kana tunanin nafi son ka a kan Abbana da har kake fadin bazan koma inda yake ba in nemi gafarar sa? Don kawai Young Abba ya bata maka rai?”

Ai Hamzah bai san lokacin da ya mike zaune ba duk da ba wai giyar ta sake shi bane, ya dube ni tsakiyar ido da kumburarrun idanun sa suna wani irin rufe kan su da kan su yace “au kawai ne ma ko? Kawai? Ya ce kada in haihu a duniya da matar halali na kada in aje kwai na sabida kawai jini na baiyi daidai da naki wajen haihuwa ba, kuma ya san bani da kowa a duniya bayan abinda zan haifa din, amma kike cewa wai “kawai”?

Ai ni a wuri na Baban ki ya gama yi min dukkan kiyayyar duniya. Ya yi min wariyar launin fata.

Tsaf zaki iya gayamin komai bakin ki ke son fadi yanzu a kan aure na, ba zan hana ki ba, sabida na fahimci kema auren kike so ki guntile, yau ne kika san da Abban? Ko ni na batar muku da Omar da zan tafi nemo miki shi? Ko kuwa yau ne kika san Hamzah tubabbe ne da har zaki yi dakacen auren sa? Na dauka kin yi kina sani ne?

To bari in gaya miki Siyama aure yanzu muka fara, babban alkawarin dana san na yi miki shine na “SOYAYYAH HAR KARSHEN RAYUWA TA” kuma ban gaza da baki ita ba ta kowanne bangare, soyayya yanzu muka fara, haka haihuwar ‘ya’ya sikila ma Salamu Alaykum yanzu muka fara, ki rubuta wannan ki ajiye, tsakanina da ke babu saki har abada Siyama! I repeat; babu saki!!!

Don haka idan ma kina mafarkin komawa dan uwanki tsohon saurayin ki Omar ne to ki daina. Sai ko in aure bisa aure zaki yi.

Amma ga shawara, me zai hana tunda kin kware wajen shan poison don ki samu abinda kike so ko ta halin kaka? To wannan karon ma kina iya sha, don rabuwa da Hamzah, a can baya kin sha don son samun sa, yanzu sai ki sha don son rabuwa da shi, ko ni ki bani in sha ba tareda na sani ba, dayan mu ya fadi ya mutu, sannan ne kike da damar guduwa daga auren Hamzah zuwa ga auren Dan uwan ki mai lafiyar jinin haifar lafiyayyun ‘ya’ya da kikewa munafukar soyayya kina fakewa da ‘yan uwantaka.

Siyama, wallahi, kinji rantsuwar musulmi kenan ko, bangaren soyayya ta kika sani (the beautiful side of Hamzah) baki sanni ta fannin hali da dabi’a ba (rough side) dina. For your information ke da kanin Baban ki; ba abinda nake so a yanzu irin ‘ya’ya na, ba kuma daga kowa ba sai daga tsatson naku Siyama, ba sikila ba, ko masu cancer ne a haifa mun a cika min gida dasu ina son abu na a haka. Ban ce kowa ya taimaka min wajen daukar lalurar su ba.

In ma zai bi ta karkashin kasa ya hure miki kunne a kan haihuwa da ni, kun yi ta banza na gama yanke wadda zata fishshe mu. Ba’a saka ni ba’ a hana ni abinda ban yi niyya ba. Aure muke yi ba zaman cin gashin kai ba da za’a ce min ga yadda zan yi da iyali na.

Soyayya ta ci abu kaza-kazan uban ta, in dai don ita kadai ake aure, ban aure ki don soyayya kadai ba, na aure ki ne domin mu rayu tare mu kuma tara zurri’a, in har ita tasa kuke tunanin kun isa ku tsara min rayuwa ko ku juya ni yadda ku ke so ke da kanin Baban naki, to na bi ta da gudu yau, na tattake ta da takalmi a kafa ta”.

Sai yanzu na fara gane inda Hamzah ya dosa, duk da haka na yi maza nace “Kada ka kuskura ka zagar min Young Abba! Ya ishe ka haka Hamzah kama sunan sa da kake yi cikin masifar ka”.

Na fada da muryar da na kasa amincewa cewa tawa ce sabida zafin ta. Ban rufe baki na ba ya dora.

“Idan aka zage shin me zaki yi?”

Ya fada yana matsowa gare ni furiously. Idanun sa na kara kankancewa da neman bala’I fal a cikin su. Na dubi tsakiyar idanun sa nace “Mr. Hamzah Mawonmase, idan ka kuskura giyar ka ta gaya maka karya a kai na zaka yi nadama.

Ba ni nayi maka laifi ba, ban san hawa ba ban san sauka ba, ka daina hadawa da ni cikin neman bala’in ka, ni da baki na ban yi magana da Young Abba akan haihuwa ba, tsakanin ku ne wannan, ta yaya zaka zo ka juye fushin ka a kai na? Idan ka kuskura ka doke ni, ka taba lafiyar jiki na ko yaya ko da kuskure ko mayen giyar ka, ka tabbata baka daki banza ba…. don ba daga sama na fado ba”.

Ban kai ga rufe baki ba naji saukar yatsun sa biyar a farar delicate fuska ta, sai dana ga gilmawar wata da taurari, na kuma nemi ji na da gani na na wucin gadi na rasa, kafin in farfado daga wannan suman, ya sake kwashe ni da marin a barin hagu, (hagu da dama duk suka samu) ya hada da sanya doguwar kafar sa ya kwashe ni kasa a kan marbles, na yi wata mummunar faduwar da sai da kwankwaso na ya amsa. (With ego) irin na Da namiji, a lokacin da yake kan ganiyar rashin mutunci na kololuwa Hamzah ya ce,

“na daki Aisha-Siyama yau, kuma na daki banza din! Me za’a yi min banda godiya? Iyayen da kike taqama kina da su kin san zafin su ne? Ko sai yanzu da kika gama shan madarar Da namiji ne kika san zafin su kika san kina da su? Cewa nake barin su ki kai a kai na? Balle don na dake ki su rama miki don basu san zafin rashin biyayyar Da ba?

Idan ke ce ke rike da igiyoyin auren mu a hannun ki, na umarce ki da in kin ga dama ki sa almakashi ki tsitstsinka su, ki gutsitstsira su ta inda ba zasu kullu ba tunda na dake ki, kuma ki sani na daki banza zan kuma kwana lafiya.

Har kotu zan raka ki, ki kai ni kara in ya so alkali ya rama miki don ba nace Abba ba, shi da aka zabe ni aka bar shi, in yaso sai ki gayawa alkali cewa na mari Zinariya ta, tunda kece mijin. Ke ce sama da ni. Sokuwa kawai.

Idan baki fita sabgata ba, abinda yafi mari da barin makauniya zan miki Siyam. Na gaji da matsalolin ki, na gaji da fitinar ki, kin takura min kin matsanta min da maganar addini.

In tambaye ki mana, shin kabarin mu daya ne? Ko kuwa tare za’a yi mana hisabi ni da ke?

Look, I want to be far away from all these worries and unnecessary disturbances din naki. Uwa ta data rage min kwal a duniya da Da na na rasa, wanda na kallafawa rai, baki tausaya min kin rarrashe ni kin kwantar min da hankali a kan hakan ba, daga ke har Baban ki ba ta wannan tausayin kuke ba, a’ah sai tijara, da son nuna min kun samu hanyar gujewa aure na ko? Bayan ni na rasa Kakata a kan ki, na bar addini na na iyaye da kakanni don in rayu da ke, ki bar ni in ji da rashin ta kadai da rashin sanyin idaniya ta, ba rashin mutuncin ku ke da uban ki ba, wanda bai yarda (sickle cell disease) ba shine karshen rayuwar dan adam ba, ko ni da ba’a haifa cikin Musulunci ba na san mutuwa da rayuwa a hannun Allah Al-Hayyu Al-Qayyum suke. Idiot, stupid kawai!”.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 4.5 / 5. Rating: 2

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Sakacin Waye? 53Sakacin Waye? 55 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×