Ban taba bakin ciki da auren Hamzah ba, kuma har abada bazan yi ba, don na yarda Hamzah Mustapha (Mawonmase) yana cikin kaddarata ne. Ba Abba na ba, ba wani mahaluki ba, irin wannan rubutaccen auren namu tamkar ZANEN DUTSE ne, jayayya da afkuwar sa zai iya tafiya da rayuka don tabbatuwar sa, auren da tun ban balaga ba na san da afkuwar sa da suffar mijin kan sa da muryar sa cikin wata qudura da iradar Ubangiji, na girma tare da shi ina mai ganin sa cikin mafarkai na dare da rana, don haka na amince Hamzah kaddarata ne. . .