Skip to content
Part 56 of 73 in the Series Sakacin Waye? by Sumayyah Abdulkadir Takori

Da yamma ina aiki a kwamfutar bisa cinya ta (laptop) a babban falo kamar daga sama, kamar kuma cikin mafarki naji ana bude kofa. Cikin hanzari na dago kai na ina kallon kofar shigowa. Hamzah ya shigo falon cikin nutsuwar sa ta halitta, ya yi min cikakkiyar sallama irin ta addinin musulunci wato “Assalamu alaykum” tare da cewa.

“Hi, Sweetheart”.

Sanye yake da ‘traditional attire’ na kabilar sa (Beroms), ya karkata hular a gefen dama na fuskar sa. Ba karamin kyau ya yi ba. Kasancewar ban taba ganin sa cikin kalar irin wannan dressing din ba. Sai na ga ya fito a wata kala daban, kalar sa a yau ta fiddo zahirin bakaken gogaggun ‘yan bokon Najeriya da suka samu rayuwa yadda suke son ta.

Duk da zuwan nasa a daidai wannan lokacin ya bani mamaki, don ban zace shi nan kusa bama, ko kallo na biyu ban kara yi masa ba, na kauda kai na cigaba da abinda nake yi cikin kwamfutar da ke bisa cinya ta.

Hamzah ya karaso a hankali tamkar mai sanda ya zauna a kusa da ni har kafadun mu na gugar na juna, yasa hannu ya dauke kwamfutar daga cinya ta ya ajiyeta can gefe a saman kujera. Muguwar harara na sakar masa don ko kusa ban ji na yi wani farin ciki ko akasin haka da dawowar sa ba. Hasali ma ni yanzu na riga na saba da kadaicin ina kuma jin dadin sa, wanda a ganin sa mugunta ce yayi mun, tafiya ba kira ba sako, don na sha gaya masa (a lokutan mu na dadi) in ya fita ya bar ni ni kadai a gidan ji nake tamkar ya tafi tare da ruhi na ne, bana kara samun nutsuwa sai na ji sallamar sa ya dawo gidan, amma wannan karon abun ba haka yake ba, ban sani ba ko don bamu yi rabuwar dadi bane? Kodayake bai taba yin tafiyar data yi tsaho haka ba tun bayan auren mu sai tare da ni. Wannan karon tafiyar sa ta sa na samu lokacin kai na sosai, na yi duk abinda ya dace na editing din project dina kafin na mika shi ga jami’a.

Da ya ga har zuwa lokacin ban kula shi ba sai ya zare hular kan sa ya kwantar da kai a cinyoyi na wato yayi filo da kafafuna. Murya can kasa ya ce “Siyama babu ko sannu da zuwa? In ban samu wannan ba ya kamata ki amsa sallama ta tunda amsa sallama ga musulmi wajibi ne. Ko ki tambaye ni yaya burial?”

Wata kasaitacciyar harara na sake zabga masa na soma kokarin mikewa ya danne ni bakidaya a kan dguwar kujerar ya sakar mi nautin sa. Cikin rashin damuwa nace da shi “in tambaye ka burial ko in ce Allah ya kara nauyin kasa?”

Ya ce “menene kuma nauyin kasa?” Na kyabe baki na ce “Addu’a ce irin wadda tafi dacewa da ita””Allah yasa ba zagar min ita ki kai ba har cikin kabarin ta, don ni ban taba jin irin wannan addu’ar ba” ido na yayi rau_rau yana son zubar da hawaye nace.

“Hamzah ashe babu dadi? Ni da ka zagi Baba na fa wanda ka san banida na ukun sa? Wanda ya taimaki rayuwa ta a sanda mafarkan ka da jiran bayyanar gaibun ka suka dagula ta? Wanda yayi min komai kamar shi ya haife ni a lokacin da uba nay a kore ni saboda kai. Wai Young Abba! Hamzah idan da alkawari ruwa ba zai dafa kifi ba”.

Na mike da niyyar barin wajen sai ji nayi ya fizgoni na fada jikin sa, ya rungume ni tsam-tsam yana kissing ta ko’ina, Wani irin mahaukacin kiss. Ya na fadin “yi min komai don ki huce Siyam, tunda kikace HAMZAH na san na kai ki makura. Ki yi hakuri na san ban kyauta ba, na ci amanar Young Abba tunda na doke ki, but I promise to repent everything ta hanyar kai ki gida Najeriya mu gyara komai.

Shirye shiryen tafiyar mu sun yi nisa, zamu tashi nan da wata daya after graduation din ku.”

Ai jin haka dana yi wato tafiya gida sai duk wani bakin ciki na ya yaye, na nemi fushi na da bacin rai na na rasa. Duk da haka bai ga hakan a kan fuskata ba ya shiga yin duk yadda ya san zai yi ya lallashe ni, amma ya kasa ganin ko da murmushi na. Daga bisani kissing din sa ya canza salo domin ya koma yin sa very hot ta inda ban zata ba, na yarda da kiss Hamzah ke saye ni. Don sai da ya mantar da ni cewa cikin halin biki nake har zuwa lokacin, ya soma samo kai na cikin hikimomin iya soyayyar sa, na dokantu, na jarabtu na kuma matsu da kewar sa har muka kusa karya limit.  Allah ne ya taimake ni aka kira shi a waya. Kuma kiran na da muhimmancin da dole ya tsaya amsawa.

Dakatawar da yayi don ya amsa ne ta ankarar dani halin da muke ciki ni da shi a kujerar falon mu na kokarin wuce limit din da addini ya deba mana a halin jinin biki, na yi amfani da damar na sulale na bar masa falon.

Duk yadda ya so ya samu hadin kai na a daren mu yafi juna, mu koma rayuwar mu yadda muka saba domin hakika yayi kewar far’ar Siyam din sa da kulawar ta yadda baya zato a ‘yan kwanakin da ya yi a Jos na burial din Kaka, amma abun da yake ganin mai yuwuwane cikin dan lokaci kamar yadda suka saba in sun samu sabani shi da Siyamar sa yau ya faskara, duk da albishir din tafiya Najeriya da ya kawo min, a zuci nayi murna ta naki nuna farin ciki na a zahiri tun yana ganin rigimar tawa mai lallasuwa ce wato kankanuwa ce har ya ga wankin hula na kokarin kai shi dare, don a daren duk maganar data zo baki na fada masa nake babu taunawa saboda yadda idanuna suka rufe da tasowar bacin ran abin da ya yi min kafin tafiyar sa, da kullenin da ya yi kwana biyar, inda wani abu ya same ni fa babu hanyar fita?”

“to ke ba’a miki laifi a baki hakuri ne Siyam? Ni da ke ai kar ta san kar ne bay au muka fara ba. Ko Allah muna masa laifi muna bashi hakuri ya ji kan mu ba don halin mu ba ya yafe mana, na karya hulata na russuna na roki afuwa daga macen da babu kamar ta a rayuwa ta.”

“Mr. Hamzah ka bar min daki na kawai ka koma naka ko ka tafi duk inda yayi maka dadi, mun gama wannan qarnin (na soyayya), tunda har ka iya ka ce min nympho babu ni babu kara wannan rayuwar da kowane da namiji ba kai kadai da auren sunnah ne ya hada mu ba, zan iya rayuwa ta babu miji yadda kake daukata ba haka nake ba, nib a jarababbiya bace. Don ina so ka ne kawai amma halitta ta ba haka take ba. I can live in peace ba tare da kai ba da duk abinda yake making dinka arrogant, tunda kuma ka kuma ce ba kabarin mu daya ba, to ka fita sabgata na sallamawa giya Hamzah Mawonmase ‘Dream Husband’ dina, kowa ya yi abunda ya zabarwa rayuwar sa wanda yake ganin shi zai fishshe shi a duniyar sa da lahirar sa.

Tunda ka ce ka zabi giya ni kuma na zabi mu raba daki daga yau. Har sai ranar da ka bar giya kwata-kwata.”

Amma bai tafin ba, ya jure dukkan bakaken kalamai na ya shanye su ya kora da ruwa ya cigaba da kaskantar da kai da kwantar da murya, lallashi, ban baki da ba hakuri iri daban-daban. The apologizer Hamzah Mawomase. Wata dabi’a tasa da ke tsananin jan hankali na wato saukin kai da maida matar sa QUEEN OF THE EARTH idan ya mata laifi. Zai iya kwanciya a kasa matar ta taka shi ta wuce in dai hakan zai sa ta huce.

A daren Hamzah kwana yayi yana lallashi na ta duk hanyar da ya san ita ce weakness dina musamman akan zuwa wurin Abba da zuwa gida Mambillah. Ya ce “gobe sai mu fara sayayyar tsaraba wa mutanen Mambillah. Sai Anti Wasila da yaranta, sai kuma wa?” Ban San sanda na ce cikin cin magani “sai Azima Ka’oje”. “Wacece ita din?” Da yake ya gama saye ni yau da zancen tafiyagida sai na ware na hau bashi labarin irin amincin da ke tsakani na da Ka’oje a Regent.

Aka ce mace da miji sai Allah kafin wayewar gari Hamzah ya kalallame ‘yan kayan sa. Hamzah da Siyamah ikon Allah.

Tun daga ranar nake sayen tsaraba wa mutanen gida ina tarawa, domin Hamzah credit card din sa guda ya bani na bankin sa JP Morghan Chase yace in yi ta sayen tsaraba. Anti da Young Abba sun yi matukar mamaki dana je musu sallama na ce tafiya Najeriya zamuyi ni da shi bazamu jira su ba. Young Abba har da kara jaddada min in je asibiti ayi min family planning don bai ga alamar Hamzah yayi na’am da shawarar sa ba. Kuma shi bai ga amfanin haihuwar yara sikila ba. Na bi shi da to, ya kara fada min hujjojin sa ya ce saboda shi za’a dorawa alhakin komai. Ummati Kuma bazata taba yafe masa ba idan ya kawo mata Sickle Cell Disease cikin iyalin ta. Shi kuma sha’afa yayi da maganar genotype da ko zan mutu saboda soyayya da kafiya da ba’a yi ba. Hamzah saidai ya musulunta saboda Allah ba saboda ni ba.”

Na dai fahimci Young Abba bazai taba son in haihu da Hamzah ba, ba kuma don baya son Hamzah ko don ya daina son sa da addinin musulunci ba a’ah, sai don tsoron consequences din da hakan zai janyo tsakanin sa da Abba na da Ummati da hango mana wahalar da bam ai karewa bace ba kamar yadda shi Hamzah ya fassara shi ba. Na dai yi shiru ban fada musu abinda shawarar da ya bashi din ta janyo min ba. Could you imagine har Mari na sha daga yatsun Hamzah a kan hakan.

A sati biyun nan na kammala karatun digiri na daga George Washington University, Karkashin rakiyar Young Abba da Anti Nasara da mai gayya mai aiki maigidana Hamzah Mawonmase. Jami’ar mu ta yi mana convocation ceremony, ranarna amshi kwalin shaidar kammala digiri na na farko a aikin jarida mai daraja ta farko. 

A ranar na yiwa Young Abba kuka Ina godiya ina hawaye. He made me what I’m today, duk wasu achievements dina na yanzu bayan barowa ta gida na san kokarin su ne shi da mai dakinsa. Sun canza rayuwata positively sun kuma tabbatarda dukkan mafarkaina zuwa reality. Su Kuma suka ce ba abin godiya a nan, domin kuwa responsibility din su ne.

Shirye-shiryen tahowar mu gida suka ci gaba kankama. Wani abu da ya ba ni mamaki, Hamzah ya shiga sayar da komai na gidansa, hatta motocinsa guda biyu ya sanya su a kasuwa, ko bai fada ba na fahimci niyyarsa…. ba shi da niyyar dawowa kasar Amurka.

Ana i gobe za mu daga Nigeria Aunty Nasara ta kira ni a waya. Daga yadda na ji muryarta na san a rikice ta ke. Ta ce, “Siyama, da gaske Hamza ya ajiye aiki da VOA? Da gaske in kun tafi ba za ku kara dawowa ba? Da gaske wani aikin ya samu wanda ya fi na VOA?”

Ni ma na rikice na ce, “Aunty ban da wannan labarin ko makamancin sa ko daya, bai gaya minkomai ba, na dai ga ba ya wuni a gidan nan tun bayan convocation ceremonydin mu, ya zama wani irin busy da preparations din da ban san na menene ba,in na yi masa magana ya ce shirye-shiryen tafiya yake mana, bayan wannan bai min wannan zancen ba”.

Aunty ta ce, “To kuwa tabbas na ji labari daga Director Philiph Carter cewa Director Hamzah Mawonmase ya bar VOA”.

A ranar bai dawo gida ba sai can dare. Ban ga alamar buguwa a tare da shi ba, sai ma wani nishadi da yake faman yi. Ina shafa mai a gaban mudubina ya shigo dakin cikin shirin barci, yana daura igiyar pajamas din sa kan sa na yararin ruwa alamar fitowar sa kenan daga wanka, ya ce, “Siyam, har yanzu wai jinin haihuwar bai dauke ba?”

Na zumburo baki na ce, “Kana da lokacina ne da har za ka yi noticing ya dauke ko bai dauke ba? Na dauka yanzu ba ka da lokacin wannan tunda kana ta abubuwanka babu shawara, babu bukatar Sanina.”

Ya zauna a gefen gado yana fadin, “Who the hell is this munafiki kuma?”

Na dube shi a kufule na ce, “Kar kayi saurin kiranta munafuka, ba da niyyar munafurci ta gaya min ba, tambayata ta ke curiouslywai da gaske ka bar aikinka?”

Ya kama baki yana fadin, “Mrs. Alkali and her Young Abba sun saka ma rayuwa ta ido fa.”

Mikewa na yi zan bar wajen ya riko hannuna “Zo ki ji” na fisge cikin fushi ya sake riko ni”.

“Haba sweetheart, gobe i yanzu fa kina gaban Abba in Allah ya so”. Ban san sanda murmushi ya kubuce min ba. Ya samu yadda yake so ya maida allura garma. Sosai muka raya daren. One thing a tare da Hamzah baya ta gundurar matar sa, ko bata ra’ayi ya san yadda zai shawo kan Siyamar sa.

Washegari har da su Anti aka raka mu airport, har da Young Abba, a filin jirgin ne Young Abba ya kuma ja na gefe yana kara jaddada min maganar muhimmancin family planning da ya ce in yi ko ba da sanin Hamzah ba, don Hamzah ya kasa fahimtar sa, ya kasa tsayawa ya fahimci abinda yake nufi, ya ce ko shi zai bani Ahyan halak malak in bamu son dauka daga dangi, Young Abba ya ce mu fara sauka a Abuja mu ga Abba, mu jure duk wasu tambotsan sa don ya fi ni son ya ganni yanzu sai dai kafiya da fulatanci irin nasa su hana shi nuna ya yi murna da ganin nawa, shekarun da muka yi bama tare suna da yawa, kuma lokaci yana warkar da komai, shi Young Abba zai gaya masa cewa mun taho tare da miji na.

A karshe ya ce, suna nan tahowa suma nan da sati biyu masu zuwa insha Allahu da zarar sun kammala nasu shirin tahowar, Hamzah bai yi shawara da shi ba sai jin tafiyar mu yayi katsahan ya kuma fahimci Hamzah ya yi haka ne don yana fushi da shi akan maganar da ya yi na mu dakatar da haihuwa, amma yafi so mu tafi tare zuwan Hamzah na farko gaban Abba ya kasance muna tare da shi don ya zame mana garkuwa, amma tunda Hamzah ya ga zai iya fuskantar Abban da kan sa shikenan mu yi gaba din, ya ce mu tsaya a Abuja har sati biyun su cika, in suka iso shida Nasara sai mu dunguma bakidaya mu wuce Mambillah, don shi kadai zai iya da rigimar Ummati a kan auren da yayi min ba da sanin ta ba, kuma ba bahaushe/bafillace ba, sannan ba asalin musulmi ba, yare kabila da addinin asali sun banbanta wanda ya tabbata Ummati bazata dauka da sauki ba, don ba ya jin har zuwa yanzu Abba ya bude baki ya gaya mata wani abu a kan aure na.

Ina hawaye Aunty Nasara ma tana yi, Ahyan yana kuka yana zai bi ni Abban sa na rike shi yana cewa “idan muka iskosu a gida kai bazaka dawo ba zan baro ka a hannun Anty Siyama, so ka daina kuka ka ji Ahyan? A haka muka wuce terminal, hannu na cikin na Hamzah, muka bi steps muka hau jirgin Turkish Airline wanda zai yi transit da mu a wata kasar. Sai bayan mun zauna a muhallinmu Hamza ke gaya min za mu yi transitna kwana daya a kasar Turkiya birnin Istanbul.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Sakacin Waye? 55Sakacin Waye? 57 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×