Cikin ikon Allah sai ga Ahlam, wato makwabciyar mu wadda ta kawo ni asibitin ta shigo. Ya juya yana tambayar ta ko za mu iya tafiya yanzu? Ta ce, “Go and confirm from the doctor”. Wato ya je ya tabbatar daga likitan, sannan ta bude jakarta ta fiddo passport dina da ta tsinta tare da ni cikin hannuna ta damka masa.
Ya Omar ya bude passport din yana dubawa, bai san sanda hawaye suka cicciko a idon sa ba. Rabon Boddo da Abba shekaru har takwas passport din har ya yi expire. Shin anya ba laifin sa ba ne, ba. . .