Skip to content
Part 63 of 73 in the Series Sakacin Waye? by Sumayyah Abdulkadir Takori

Cikin ikon Allah sai ga Ahlam, wato makwabciyar mu wadda ta kawo ni asibitin ta shigo. Ya juya yana tambayar ta ko za mu iya tafiya yanzu? Ta ce, “Go and confirm from the doctor”. Wato ya je ya tabbatar daga likitan, sannan ta bude jakarta ta fiddo passport dina da ta tsinta tare da ni cikin hannuna ta damka masa.

Ya Omar ya bude passport din yana dubawa, bai san sanda hawaye suka cicciko a idon sa ba. Rabon Boddo da Abba shekaru har takwas passport din har ya yi expire. Shin anya ba laifin sa ba ne, ba shi ya janyo wannan paternal deprivation din ga Boddo ba? Da bai yanke shawarar yin nisa da gida ba da Abba bai kori Boddo ba, da abubuwa da yawa ba su lalace har haka ba. Da ya sani tsayawa ya yi ya yi facing dukkan challenges din. Ya taya boddo lallashin Abba har ya amince da albarkarsa ta auri Dream Man din ta. Amma sai ya tafi, wanda hakan shi ya dagula komai, ya fusata Abba ya kuma jefa rayuwar Boddon sa cikin hali na kaka-ni-kayi. Fushin mahaifi ke ta walagigi da ita. Amma Allah shi ne shaidar sa ya yi ne for her own betterment. Don ba zai yarda a yi mata auren dole da shi ba, duk da cewa har gobe… har jibi… har gata Boddo is like no other a zuciyar sa.

Da wadannan tunane-tunanen Omar ya nufi ofishin likitan da aka nuna masa cewa shi ke duba Boddo ya kwankwasa. Likitan ya ba shi izinin shiga, suka gaisa sannan ya gabatar masa da kan sa a matsayin Yayan patient din da yake dubawa currently, yana so ya tafi da ita gida yanzu, za su kula da ita.

Likitan ya ce, “Me ya sa ba za ka bari ta kwana biyun ba ta huta? Sannan kana da masaniyar cewa ‘ya’ya biyu ne a cikin ta?”

Omar ya lumshe ido ya ce, “A’ah!”

Likita ya ce, “To ka barta ta kwana biyu, mu duba ta da kyau, mu tabbatar da cewa babu alamun bleeding din da ta fara kadan-kadan, yaran kuma wadanda sun shiga wat ana biyar yanzu, mu yi checking lafiyar su”.

Dole Ya Omar ya kyale ni a asibitin, ya yi kokarin biyan bill aka ce wadda ta kawo ta ta biya, so dole ya koma dakin yayi wa Ahlam godiya mai yawa, ya ce, tana iya tafiya gida ta huta, yanzun nan zai je ya zo da wadda za ta kula da ni.

Ai ina jin haka na tubure masa kada ya kuskura ya kawo min matar sa, ya kyale ni in yi zama na ni kadai. Ya dan juyo yana duba na da idanun mamaki, amma ganin Ahlaam na kallon mu sai ya share, ya ce, “to me za ki ci in kawo miki?”

Na soma tunanin abin da na san ba zai iya samowa ba, na ce, “Amala nake so da miyar ugu”.

Omar ya gyada kai ya ce, “Lallai zama da kabila ya yi rana”.

Na ce, “Eh, gara shi akan matar ka mai tafiya kamar kwai ya fashe mata a ciki, tana yi wa mutane kallon hadarin kaji”. Cikin mamaki da dariya yace, “A ina ki ka ga mata ta kuma a ina ki ka santa har ki ka san ta miki kallon hadarin kaji?”

Na juya na rabu da shi, don wallahi sosai nake jin wani irin bakin ciki da matar Ya Omar. Kishin da ban san da sunan da zan kira shi ba. Kishin-sauri ko kishin bal-bal?

Ya gyada kai ya fice yana wani miskilin murmushi.

Ahlaam ba ta tafi ba har sai da Ya Omar ya dawo tare da matar sa Kausar Shettima, tana dauke da dandasheshen food basket, shi kuma yana rike da hannun yaron su Aryan. Na yi maza na rufe ido kamar mai barci don wallahi haushin ta nake ji, bana son ganin ta. Kyan ta da ajin ta har firgita ni suke. Sai ban ga laifin Hamzah ba da ya kama ni ina mu’amala da Ya Omar a boye ba tare da ya sani ba ya haukace irin haka, sannan abin da kunnuwan sa suka jiye masa da shi zai yi amfani, cewa na yi fa I love you Ya Omar kuma da gaske I love him din, he’s my happiness. Ya Omar has been my happiness kuma garkuwa ta sannan karfi na tun zuwa na duniya, ko ganin sa na yi sai na ji wani irin farin ciki ya lullube ni. In kuma cikin damuwa nake, da ya doso waje zan ji dukkan damuwa ta ta yaye in fara blushing. Wannan ne Abba ya rika ya dauka soyayya ne. Eh soyayya ne mai girma daga ubangiji, amma ta ‘yan uwantaka. I cannot have a bodily relationship with him irin wanda nake sakin jiki in yi da mijina Hamzah da dukkan shauki da kuma dukkan contentment na zuciya ta. Wannan hukuncin ba nawa ba ne ba yin kaina ba ne, hukuncin Ubangiji ne Tsakani na da Ya Omar.

“She’s sleeping Honey”. Kamar in bude ido in dalla mata harara, a gabana wata katuwar mata ke kiran Ya Omar honey yau, kuma ban isa in yi magana ba.

Sai cewa ya yi, “Rabu da ita, zuba min amalar ni in ci, in ta ji kamshin abincin su na kabilu za ta motsa ne”

Ai kuwa na bude ido na harare shi ina tsuke baki, ya ce da matar tasa, “You see, barcin karya ne”.

Kausar ta hau zuba masa abincin cikin yanga da gayun ta na halitta. Komai nata cikin sanyi tana lankwasa jiki, kamar macijiya. Ga ta da yalwar gashin kai wanda tudun sa ya bayyana ta kasan dankwalin atamfa Super orange colour da ke jikinta. Ban taba ganin bakar mace mai kyau, aji da kasaitar matar ya Omar ba, kamar wadda ta hada jini da sarauta.

Ina hango miyar Ugu zuku-zuku da naman kaza yawuna ya wani tsinke Malam. Ga shi ina ganin kyashin in ci abincin da matar Ya Omar ce ta girka.

Ita da kanta ta gane ina hadiyar miyau, ta ce, “Siyama Jabbama, lale-maraba da zuwan ki cikin mu”.

Na motsa baki kamar mai ciwon hakori na ce, “Na gode”.

Daga haka ban kara kula ta ba. Ta zubo abincin ta kawo min har inda nake kwance ta gyara min pillow ta taimaka min na zauna sosai sannan ta shiga yanko loma kan loma tana kai wa bakina kamar yadda ake ciyar da karamin yaro. Wannan concern din, da wannan caringattitude din da na gani a tare da ita shi ya fara dan dankwafar da tsanar da na samu zuciyata na yi mata, babu gaira babu dalili.

Kwanana biyu a asibitin bayan nan, Ya Omar da matar sa Kausar na kula da ni. Likitoci kuma sun gama hada dukkan binciken su da report din su a kan ciki na wanda ke cikin watanni na biyar a lokacin.

Na farko dai sun ce yaran guda biyu ne, amma sex din su ya ki bayyana clearly wato sun kasa gane maza ne ko mata, za su sake yin scan din bayan wata daya.

Kuma a zakule-zakulensu sun gani dukkan yaran marasa lafiya ne, daya sickler daya carrier.

Ranar da aka sallame ni na dauka Ya Omar gidana zai maida ni, amma sai na ga akasin haka. Kai tsaye gidan sa muka wuce ya ce, “Sai Hamzah ya neme ni don kan sa, ya kuma nemi afuwar korar da ya yi min. Da dalilin sa na yanke hukunci babu bincike don kawai ya kama ni ina waya da dan uwa na, ko ma mece ce hujjar sa ba shi da damar kora ta daga dakin aure na idan ya san ba saki na yayi ba.

Idan a baya ya sha giyar sa ta gaya masa ya doke ni, ya zage ni ya ci mutunci na yayi min gore-gore ya kwana lafiya, to baya nan ne.

Ya karasa da cewa, “I’m here now!”.

Sai na rasa abin da zan ce, sakamakon wani dadi dana jiya rufe ni, ashe dai da sauran gat ana, don laifi na san na yi wa Hamzah, amma shi ma abin da ya yi min din bai kyauta ba, ya kuma zarce laifi na.

Gidan da su Ya Omar suke ciki flat ne, hawa daya mai dakuna uku, dakin Aryan a nan suka sauke ni, Kausar sai nan-nan ta ke yi da ni. Ni sai yanzu ma nake ganin yadda ake kula da miji da kyautata masa ba irin nawa ba da ban iya komai bas ai discipline, fushi, daukar matakin sex denial da malantaka. Gaskiyar Hamzah ne ba na barin sa kwanciyar hankalin da har zai dauki abinda nake koya masa ta dadin rai, kuma ba ni da manner of approaching sabon mutum a cikin addini kuma na raina kulawa da soyayyar da ni na dinga yi masa da na ga wadda Kausar ke yi wa Ya Omar ko a gaban mu ne. Ga shi komai ya tafi ba yadda ake so ba balle in kara daura dammarar gyarawa.

Tare muke kwana ni da Aryan, kishin Kausar ban daina ba a kasan raina amma ya zanyi? Ya Omar ya min fintinkau, Kausar ta zarce ni a komai, ni ba tsarar yin ta bace banda kanwar miji, sannan kyautatawar data ke min ko naki Allah dole na daga ido in mata murmushi. Tun washegarin ranar Ya Omar ya dauke mu muka tafi immigration don sabunta passport dina, ya biya kudin sabunta fasfo din aka ba shi ranar zuwa ya karba, sannan muka koma gida.

Da daddare mun yi dinner tare gaba dayan mu daga daddadan girkin Kausar mai kayatar da zuciya. Lafiyayyen tuwon shinkafa ne tayi mana miyar taushe da tantakwashi. A ranar ne santi yasa na danne zuciya ta na tambayi Ya Omar yadda akayi suka hadu da Kausar Shettima har suka yi aure ba tare da sanin su Ummati ba.

Kausar ta mike tsaye ta ce, “Wannan hirar taku ce, ni zan je in kwanta, kin san gobe ne surgery dina. So gara in kwanta da wuri don in samu damar tashi qiyamul-laili”.

Tausayin ta ya dan kama ni. Na ce, “Insha Allahu Aunty Kausar za a yi lafiya a kuma gama lafiya”.

Bayan wucewarta dakin ta. Ya Omar ya soma ba ni labari,

“Bayan na bar gida a ranar ban kwana Abuja ba, motar garin Dikwa na hau na nufi wajen aboki na na kut-da-kut da muka yi karatu tare a jami’ar Gwagwalada, ana kiransa Mansur Shettima Dikwa.

Na san Mansur kamar tafin hannu na, shi ma ya san ni. Mun kuma san asalin junan mu da inda kowannen mu ya fito. Mansur dan masarautar Dikwa ne ta jihar Borno. Mahaifin sa Maimartaba Alhaji Shettima Aliyu Dikwa shi ne sarkin garin Dikwa mai ci a lokacin, wato Shehun Dikwa, kuma ya gaji sarautar ne daga mahaifinsa Mai-Dikwa “Mai” yana nufin sarki a harshen su na Kanuri, wato Shehun Dikwa na III Mustafa Mai sango El-Kanemi.

Dikwa, na daya daga cikin manyan masarautun nan na Maiduguri guda takwas; Borno, sai Dikwa, Biyu, Askira, Gwoza, Uba da Shani da kuma Bama.

Tun zuwana Dikwa a dakin Mansur nake zaune ba kuma na kunna wayata sai tsakar dare. Sakonni babu irin wadanda ban gani ba daga Abba da Anti Wasila ba, suna rokona in yi wa Allah in dawo gida an fasa yi miki auren dolen. Wani lokacin in ji na raunata da tausayin su wani lokacin in karfafi kaina da cewa, tafiyata ita ta fi alkhairi domin ita kadai zatabaki damar cika mafarkanki, har dai in su Abba suka gaba ni da niyyar dawowa, na san ba za su yi ta ajiyarki a gabansu ba, dole za su ce ne ki kawo Dream Husband dinki, wanda daga baya jikina ke tabbatar min yana gab da bayyana a gare ki, mafarkan kin nan sun fi karfin a kira su (mere nightmares), don zuwa lokacin na yarda da ke, na yarda Allah na nufinki da abin da ki ke gani cikin barcinki ba shirme ki ke yi ba, kuma dukkanmu mun yi kuskure mun bar abin ya girma tare da ke ba mu dakile shi tun sanda ki ka fara ba. Tun a lokacin ki ke bukatar counselling, attention da monitoring, daga ni har Ummati babu wanda tunaninsa ya kai nan, babu wanda ya dauki abinda kike ikirari da muhimmanci balle kuma shi Abba da ba mazauni ba.

Omar ya ci gaba da cewa, “Zamana a gidan Shehun Dikwa, zama ne na jinyar zuciya da kewar Abba, ke kam kullum kokari na shi ne in fidda ke daga raina don sama wa kaina da zuciyata lafiya. A hankali na soma healing, na fara gane yanayin zaman gidan sarautar Dikwa, har na kan raka Mansur fada gaida Maimartaba, ta haka ne har ya gane ni, matsayin aminin dan sa. Muka saba, kullum Mansur ya zo fada babu ni sai ya ce ya koma ya taho da Omar Faruku. Shehun Dikwa, na da ‘ya’ya da yawa maza da mata, kuma duk cikin su ya fi son Kausar wadda suke daki daya da Mansur. Ban taba ganin Kausar ba sai ranar da Maimartaba Shehun Dikwa ya aika mu ni da Mansur da ita zuwa jihar Lagos, domin a yi mata visar tafiyar ta karatun digiri a kasar Amurka.

Maimartaba ya yi mata wannan alfarmar ne kasancewar fiance din ta (wanda za ta aura) ana saura sati biyu a saka su a lalle yayi hadarin jirgin sama ya rasu. Amma ‘ya’yan sa mata bakidaya ba sa wuce sakandire. A lokacin ya tausaya wa Kausar ya kuma tambaye ta abin da ta ke so, wanda zai debe mata kewa zuwa sanda Allah zai ba ta wani mijin, sai ta ce ci gaba da karatu a jamilar Calcutta, shi ne burinta.

Ana-i-gobe za mu tafi Lagos din don neman visar ta mahaifiyar su ta tubure bata yarda Kausar ta tafi karatu wata kasa babu aure ba. Gabadaya ta daga wa maimartaba hankali, ta daga nata ga shi ita ce Mowar sarki. Sai Shehu ya kira Mansur cikin sirri ya ce yana so su yi magana a kaina, yana so ya san asali na don ya yaba da hankali, nutsuwa da tarbiyya ta, yana so ya roke ni in auri Kausar mu tafi tare, don hankalin mahaifiyar ta ya kwanta da tafiyar tata. Ya ce, babu abin da zai hana yiwuwar auren sai in na ce bana son ta, amma zai yi mana komai.

Mansur ya gaya masa duk abin da ya sani a kaina da nasaba ta, amma ya gaya masa ba zan taba yarda in koma gida nan kusa ba, saboda abin da ya fiddo ni gida ya shafi zaman lafiyar family dina bakidaya. Na gaya masa cewa ko zan koma gida sai bayan shekara biyar lokacin an gaji da jirana, an yi wa kanwa ta aure. Kuma Abban mu ya manta da zancen, Shehu ya ce ya tambaye ni in har zan yarda in auri Kausar to zai tura har Mambillah a yi bincike a kan mu. Zai kuma yi min wakili.

Da Mansur ya tambaye ni, rasa abin da zan ce na yi, daga baya na tuna gubar da ki ka sha wai don kada ki aure ni, yau ga shi ni ake yi wa tayin auren ‘yar Sarki, kuma ‘yar gata irin Kausar Shettima wadda tun ganin farko da na yi mata ta  zauna min a rai sabida sanyin muryar ta da nutsuwar ta. Na yarda musanye na alkhairi Allah ya yi min da gaggawa don haka ba zan tankwabe ba. Musamman da Shehu ya ce, shi zai min wakili ba za a kira Abba ba in har na amince. Don na ce in har an ce sai na gabatar da iyaye na to ba zan amince ba don ban shirya komawa gida nan kusa ba.

In takaice miki zance, ba mu tafi Lagos din ba ma sai muna a matsayin ma’aurata ni da Kausar, kuma an yi sa’a Kausar iri na ce, ba ta da daukan rayuwa da fadi, ba ta ce sai an yi wasu bidi’o’i nasu na kanurai ba, hatta lefen Shehu ne ya yi mata  sadaki kawai na biya daga dan abin da nake da shi a banki da na tara lokacin NYSC dina a Calabar, don a lokacin Abba na ba ni wadatattun kudi duk wata, don haka wadancen kudin na gwamnati shiga kawai suke suna taruwa ba abin da na yi da su. Da su na hada na biya sadakin Kausar naira dubu dari, wanda a lokacin ba laifi darajarsu ta fi ta yanzu.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 1.5 / 5. Rating: 2

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Sakacin Waye? 62Sakacin Waye? 64 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×