Skip to content
Part 64 of 73 in the Series Sakacin Waye? by Sumayyah Abdulkadir Takori

Mun yi honeymoon a Ikko na tsayin sati daya, wallahi sai a lokacin Boddo na san cewa, yes ina son ki, domin na kasa sakin jiki da Kausar duk da ta fi ki komai, sai a hankali na soma sabawa da ita, son da nake miki kuwa bayan kasancewar sa na ‘yan uwantaka to cakude yake da soyayyar da ta zarta tunani na, ga sabo mai yawa a cikinsa. Sai a hankali na soma son matata Kausar, na kuma so ta differently da irin son da nake miki, nata son shi ne pure and natural love, wanda babu interference na soyayyar jini ko sabo ko shakuwa a cikin sa”.

Hararar Ya Omar na yi wani bakin ciki na sukana, shi kuwa Ya Omar bai ma kula da ni ba ya ci gaba da labarin sa.

“Kausar ita ta roki mahaifin ta a kan ni ma ya biya min masters mu yi karatu tare a Calcutta, maimakon in zauna ba na komai ita tana karatu. Shehu duk abinn da Kausar ke so yi mata yake, saboda Allah ya dora masa kaunarta fiye da dukkan ‘ya’yan sa mata, kasancewar mahaifiyar ta ce mowa, kuma ita kadai ce mace a dakin su.

Muka wuce Calcutta ba da jimawa ba, Mansur kusan kullum muna tare a waya. Daga baya shi Mansur ya samu aiki a Oman ya koma can. Ni da Kausar muka fuskanci karatun mu ka’in da na’in.

Matsala ta farko da muka fara cin karo da ita, ita ce Kausar was unable to conceive for almost two years da auren mu. Duk likitan da muka ziyarta sai ya tabbatar mana ko za ta haihu sai dai ta hanyar (artificial insemination) saboda matsalar cutar (Endometriosis) da ta ke da ita.

Da yarda ta da ta Kausar muka yi insemination muka samu Aryan, because we are desperate da haihuwa. Musamman a kasar da ba ka da kowa ‘ya’ya ke debe maka kewa. Kuma ni tun fil’azal ina da son yara, amma ko Shehun Dikwa bai san da wannan sirrin ba, mun bar shi ne a tsakaninmu, sai ke yau da nake gayawa.

Watarana ina kallon talabijin din gidan radiyon VOA ne na ga Aunty Nasara tana broadcasting. Na sha mamaki matuka na yadda ta samu aiki da VOA. Don na san sanda na bar gida a jihar Lagos suke zaune, idan kuwa har da gaske tana hedkwatar su ta birnin Washington D.C zan yi tattaki in je gare ta.

A lokacin Aryan wanda sunan Abba na saka masa, wato Muhammad yana da shekaru uku, ko Kausar ban gaya wa dalilin tafiyata Washington ba, daga Calcutta na bi jirgin kasa na kai kaina gidan radiyon VOA.

Da sunanta da kuma hotonta da nake da shi, da recording din shirin da na ganta tana yi a talabijin na yi amfani na dangana da ofishin Aunty Nasara.

Aunty Nasara aka gaya mata tana da bako daga Mambillah, wannan ne ya sa ba tare da tambayar ko waye ba ta yi wa sakatariyarta umarnin shigo da ni cike da mamakin waye daga Mambillah? Kawai sai ta gan ni a gaban kujerar ta. Ta kusa yin ihu na ce in ta yi ihun kuwa zan koma, kuma ba zan kara dawowa ba. Abu na farko da na fara tambayarta shi ne, ina ki ke? Ya ya labarin Abba? Yana lafiya? Ya shiga damuwa saboda ni ko?

Nasara sai da ta karaci murnarta sannan ta gaya min, ai sun daukoki kuna tare. Tun da jimawa na tambaye ta wane hali ki ke ciki? Ta labarta min komai tun zuwanku, har Darul-Uloom da ta kai ki zuwa George Washington University. She once told me that you have met your DREAM HUSBAND. Haduwarki da Hamza, da maganar aurenku da Abba ya ki amsa, amma watakila ta manta ne ta gaya min cewa ba ki samu Dream Man dinki musulmi ba, ko kuma ta sakaya zancen ne sabida wani dalili nata? Ba zan iya  cewa ba.

Na roki Anti alfarmar kada ta fadi wa Young Abba ko ke maganar zuwana wajenta, na ce akwai lokacin dawowata cikinku, amma da sauran lokaci, ko zan dawo sai kin yi auren da ki ke so kin samu cikar mafarkinki. Na gaya mata canjin da Allah ya yi min da Kausar da karamtattun iyayenta and Nasara couldn’t control her tears. A gabana ta yi ta kuka tana cewa, Boddo ba ta kyauta mana ba ni da Abba, kuma yanzu 100% Young Abba yana bayan zabinta. Na tabbatar mata I don’t have any issue with this now, domin matata na same ta har fiye da burina a kan diya mace. A lokacin ma mun haifi ‘Aryan.’

Na roke ta a kan ta yi min alkawarin babu wanda zai san na zo gare ta, kuma za ta ci gaba da gaya min halin da ku ke ciki da su Abba da ke gida. Har zuwa lokacin da ni da kaina na ga ya dace in dawo gida in komai ya daidaita tsakaninki da Hamzah, zan zo in maida ke gida da kaina don ta gaya min Abba ya ce ba zai karbe ki ba sai kin nemo ni, kuma bai yi na’am da maganar aurenki da Hamzan da ki ka zaba ba. She told me that, he’s that VOA celebrity HAMZAH MAWONMASE.

Na sha yi wa Abba dogon sako na ban hakuri da kwantar da hankali, ina gaya masa ina lafiya, kuma zan dawo a lokaci mafi dacewa. Layi na daban nake sakawa in yi masa sakon in yi maza in cire, don ba zan juri karanta amsarsa ba, kada ya karya lagona, amma na gaya masa ni ban yi fushi da Boddo na ba. Ita ma ‘yar Adam ce kamar kowa tana da BURI as well as ZABI na abin da ta ke so, duk da cewa mafi kyau shi ne ta bi zabin iyayenta, amma duk abin da ya faru da ita akwai kamashon namu SAKACIN a ciki ni da shi da Ummati har ma da Wasila da ba mu taba zama mun koya mata maida al’amuranta ga Allah ba, da zurfafata cikin ilmin addini, da kuma koya mata yin togaciya cikin addu’ar ta, da bar wa Allah zabi cikin kowanne al’amari da muke so da rokon neman dacewa a cikinsa, a’ah, duk mun taru ne ga maida ita mahaukaciya mai matsalar kwakwalwa wanda hakan ne ya janyo ta fandarewa umarnin Abba. Ta bijire wa abin da shi yake hangowa. Na yi masa wannan sakonnin ba sau daya ba ba sau biyu ba, ke duk sanda na samu free time sai na saka bakon layi na gaishe da Abban mu, na kuma ba shi sakon gaisuwa ta ga Ummati.

Ba jimawa da kammala masters dina wanda cikin shekara guda na kammala shi, na samu aikin wucin gadi da bankin (JP Morghan Chase) wato work placement, kasancewar a kan Accounting and Auditing na yu masters dina, suka tura ni branch dinsu na babban birni, wato Washington, Kausar na Calcutta saboda a lokacin ba ta kammala nata karatun ba, duk weekend nake tafiya Calcutta har Kausar ta karasa nata karatun muka dawo Washington muka zauna gabadaya.

A kai a kai muna waya da Anti Nasara, komai ki ke ciki sai ta gaya min, don haka hankalina a kwance yake don har labarin mutanen gida a wajenta nake ji har kwanciya asibiti da Ummati ta yi da kara haihuwar Anti Wasila yaro namiji. So duk abin da ki ke ciki all this while na sani.

Na ci gaba da fafutukar rayuwa iri-iri domin neman na kai da kula da iyalina. JP Morghan suna biyana da kyau, sannan ina kasuwancin solar powerd laptops daga US zuwa kasar Turkey da Cyprus. Iyayen Kausar sun sha kawo mana ziyara, kuma Kausar ta damu a kan son sake haihuwa, shi ne dalilin tahowarmu nan ‘Medicania’ inda ta fara ganin likita tun watan da ya wuce. Na kai ta da zummar zan je in dawo in dauke ta ne Allah ya rubuta haduwarmu. Tun lokacin da na ji cewa Hamzah ba a musulmi ki ka same shi ba, da matsalolin da ki ke fuskanta na san ba komai yake dawainiya da ke ba sai fushin Abba. Amma a yadda ki ka gaya min halayen sa, da yadda ya karbi musuluncin da hannu bibbiyu da farko, na yi mamaki kwarai da canzawarsa farad daya, something must be fishy underneath wanda ba komai ba ne na tabbata fushin Abba ne ba zai barku ku ji dadin soyayyar ba. Amma mutum kamar Hamzah ba na masa zaton fuska biyu, ko yin abin da a zahiri ba zabin sa ba ne, mutane jovial  irin Hamzah are straight forward, don duka halayen da yake muzguna miki da su din idan an nutsu an hada da addu’a da albarkar uwa da uba da kuma lallashi da tattashi za’a iya overcoming dinsu tun da wurwuri kafin su zurfafa. Kamar sallah da azumi. Mai wuyar dama shine addition na shan giya.

Kin so ki bar abun ya zurfafa, ba ki dauki matakin da ya dace ba. Mai son ka-mai son ka ne har illa masha Allah. Soyayya da kauna ce ta hada ku, har suka zamo silar da ya yi sha’awar addinin ki, saboda son da ya samu kan sa da yi miki. Wannan masoyi ne da babu irin sa, ajizancin sa na dan Adam ba zai sa a guje shi ba, wanda shaidan ya yi alkawarin yin tasiri a kan kowanne dan adam a lokuta irin wadannan da ya rabauta daga shirka, don haka nakasun sa ta fuskar addini ba zai sa mu bar shi ba. Maimakon hakan, zamu kara zage damtse wajen janyo shi jikin mu ne, mu karasa jihadin da kika fara, mu nuna masa kauna da karamci irin na al’ummar musulmi har Allah ya taimake mu ya gyara. HAMZAH is a darling! (Hamzah abin so ne), ba zan gaji da cewa ba, ‘ZA MU GYARA HAMZA NI DA BODDO NA in sha Allahu.

Yanzu da na nutsu, zuciya ta ta huce, na fahimci cewa, laifi na ne da na hana ki gaya masa tun farko mun hadu, kuma na ba ki waya ba da izininsa ba. Sannan ina magana da ke a boye ba da izinin sa ba. Ko kara ya kai mu a kan duk abin da zuciyar sa ta gaya masa ya yi daidai, kuma sai mun fuskanci hukunci tunda ya haramta miki rike wayar, ya kuma san tsohuwar alakar da ke tsakanin mu. Kalmar I love you  ba kowa ke yi mata fassara guda daya ba, shaaa, kuma ba kowa ake gaya wa ita ba Boddo”.

Ya Omar ya yi dariya ya ce, “Da kin sani cewa ki ka yi, I salute, ko I respect you, and the things alike…”.

Hararar sa na yi na ce, “Ni har cikin jini da bargo ina son ka Ya Omar son da nake maka ba irin nasa ba ne ba. Kada ka manta uwa daya ta raine mu, Kaka daya ce ta mikar da mu tsaye, muka tashi tare tun ba mu san kowa ba, sai junan mu. Aka bamu tarbiyya iri daya. Don haka ni da gaske I love you din, kalmar I love you yanzu na fara fada muku kai da Abba, wallahi  I so much love you.

Rayuwata babu ku ba za ta taba cika ba”.

Na saka kuka sosai, dama kiris nake jira.

“Kawai don ya ji ina waya? Don kawai na ce I love you Ya Omar, ai ko bai san wane ne Omar din a gare ni ba, ko da kuwa a ce ba kai ba ne ba zai kore ni da ciki ba. Da ban hana shi saki na ta dabara ba ma da sakin nawa zai yi fa. A kansa aka fara kishi? Allah na tuba a irin son da nake wa Mawonmase ya kamata ya shaide ni, amma kullum tunani yake kai nake hange a gaba, hankali na a kanka yake. Eh, da gaske hankali na yana kan ka, amma da kyakkyawar manufa. Kai ne fa wanda Uba na ya kore ni domin sa, wanda ya goye ni a bayan sa tun ban iya tafiya ba, ya kuma koyar da ni ABCD da Alifun Ba’un,, jinin Asshe da Hassu ya gauraya mu, cakude dana Gidado da Mamman, don na ce ma Ya Omar I love you a manufa ta kalmar bature I don’t mean the kind of love he thinks of”.

Ya Omar ya yi tafi da hannayen sa raf-raf-raf ya ce, “So na soyayyah sai Hamzahn VOA, sai Hamzah Mawonmase, a so ka kamar a mutu, a sha guba domin ka, a guji kowa saboda kai, a ki karatu saboda kai. Ka ciri tuta Hamzah Mawonmase, you are indeed a genius!”.

Sosai na ji kunya a kan wannan kirarin da Ya Omar ya yi wa Hamzah, don ji na yi kamar gugar zana yake min. Da gaske duk wadannan kura-kuran na aikata su, da gaske fa ko? Astagfirullah wa’atubu ilaihi”. Na fada a fili, domin yanzu bayan na shiga makarantar hankali na fahimci soyayya inreality ba a yadda kuruciya ta ta fassarata ba.

Da zarar an yi aure, an biya bukatar sha’awar da ke tarnaki a zuciya, to fa aure ba zai ci gaba da dauwama cikin wancan shaukin ba, za a koma zama ne na gaskiya da gaskiya (na hakuri da juna) da abin da yau da gobe ka iya haifarwa.

“Ina so a daren nan ga wayata zan ba ki ki kira Hamzah, ki ba shi hakuri, ki lallashi ‘yan kayan ki, ki fada masa gaskiyar komai, sannan ki roke shi ya ba mu izinin zuwa gayar da iyayen mu. Son samu mu tafi tare da shi a yi ta ta kare, he has to buy a courage as a man ya fuskanci Abba haka nan wannan boye-boyen ba inda zai kai ku, sabida duk abubuwan da yake zaton Abban zai yi in kin koma ba mu da tabbas a kan su. Hasashe kawai yake yi wanda kuma shi ke tsorata shi ga jarumtakar fuskantar Abban. Hausawa suka ce faduwar gaba asarar namiji”.

Da wannan Ya Omar ya mike ya yi min sallama yana fadin, “Ki tabbata kin saka Aryan ya yi fitsari kafin ya kwanta, in ba haka ba jika ki zai yi jagab daga sama har kasa, atoh!”

Dariya na yi na ce, “Fitsarin barka da zuwa ai abun so ne ga bakuwar Uwa iri na”.

Duk da Ya Omar ya ba ni wayarsa ya kuma yi min umarnin in kira Hamzah in ba shi hakuri na kasa kiran nasa, har na yi shirin kwanciya. Na kai Aryan toilet ya yi fitsari na kwantar da shi a gadon sa, ni kuma na jefa filo bisa kilishi ina juya tsadaddar wayar Ya Omar a hannu na. Duk da na haddace lambobin Hamzah kamar yadda na haddace sunana “Siyama Gembu” na kasa kiran nasa, domin sosai na ji ciwon korar da ya yi min, kamar ya samu karya.

Amma Ya Omar ya yi umarni da babbar murya a kan in kira din, dole kuma in cika umarnin nasa. A wani bangare na yi kewar Hamzah heartily kai har da fadace-fadacen namu da basa karewa yadda ba zan iya bayyanawa ba.

Na samu yatsuna suna dialling lambar sa a hankali. Gaba na kuma na tsananta bugawa haka na daure na jira har ya daga. Tun ba’a je ko ina ba daga sautin muryar sa da ke tambayar wane ne a kan layin ya fahimci he’s partially intoxicated.

Wani malolon bakin ciki da takaici ya zo ya tokare ni a kahon zuci, zan fara sirfa masa masifar tawa irin yadda na saba yi masa duk ran da na kama shi ya sha giya na tuna kalaman Ya Omar, inda yake cewa.

“Hamzah is a darling (Hamza abin so ne) bai musulunta da fuska biyu ba, fushin Abba ne ke walagigi da ke. Shi ya hana ki samun kwanciyar hankali da albarkar da ya kamata ki samu da mijin da ki ka zaba, wanda sai kin gyara shi (tsakani na da Abban) za ki ga positive improvement ke ma.

Amma a zahiri Hamzah ya musulunta da gaskiya ba kuma da fuska biyu ba. Circumstances ke saka shi yin abubuwan da yake yi.

Sannan he’s straight forward ba zai yi abin da ba haka yake a zuciyar sa ba. Wanda ya bar addinin sa na iyaye da kakanni saboda ke na kasancewar ki musulma, ki yarda ba karamin so yake miki ba.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Sakacin Waye? 63Sakacin Waye? 65 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×