Ko babu komai zuciya ta ta yi sanyi da wadannan kalaman na Ya Omar, kamar a yanzu yake fada min su. A hankali na kira sunan sa, sunan da na jima na dade ban kira shi da shi ba.
“Habeeby!”
Gabadaya komai da yake yi ya tsaya cak! A cikin ofishin sa yake a wannan lokacin don a can yake kwana yanzun ya kasa shiga gidan, tun daga lokacin da ya kori Siyama ya dawo ya tarar babu ita babu alamar ta a kofar gidan sa, wannan ya kara tabbatar masa Omar ya zo ya dauke ta. Da ma ya. . .