Skip to content
Part 65 of 73 in the Series Sakacin Waye? by Sumayyah Abdulkadir Takori

Ko babu komai zuciya ta ta yi sanyi da wadannan kalaman na Ya Omar, kamar a yanzu yake fada min su. A hankali na kira sunan sa, sunan da na jima na dade ban kira shi da shi ba.

“Habeeby!”

Gabadaya komai da yake yi ya tsaya cak! A cikin ofishin sa yake a wannan lokacin don a can yake kwana yanzun ya kasa shiga gidan, tun daga lokacin da ya kori Siyama ya dawo ya tarar babu ita babu alamar ta a kofar gidan sa, wannan ya kara tabbatar masa Omar ya zo ya dauke ta. Da ma ya san gidan ta kullum ya fita ofis zuwar masa gida yake yi. Duk da Yayan ta ne na jini amma in ya tuna matsayin da Omar din yake da shi a zuciyar Siyama da past relationship din su sai ya ji wani azababben kishi mai tirnika zuciya. So he parked his belongies ya koma TRT ya tare, kasar Turkiye ta fice masa a rai. Hadi da tunanin inda Siyam ta shiga duk da zuciyar sa na tabbatar masa tana tare da Omar. Yana tunanin mafita ga rayuwar sa ne a halin yanzu.

Sai ya koma ga addictions din sa ga giya kacokam, ya kuma dauki leave na sati biyu amma kuma bai bar ofishin nasa ba.

A kujerar ofishin sa yake kwana a zaune, ya shake firinjin ofishin sa da barasa kala-kala.

Ita ta koma abincin sa, kuma abar debe masa kewar Siyama, tun ranar da ya kore ta. And his life contineous very badly, babu sallah cikakka sai in baya cikin maye kuma babu kuzari a tare da shi.

Dan gyaran da aka samu tun bayan bayyanar Ya Omar ya sake bin ruwa, don ma dai Ramadhan ya zo karshe, ana shirin yin bikin karamar sallah a lokacin.

15

Ana I gobe sallah karama ya koma gidan sa. Sakamakon tafiya hutun sallah da TRT World suka yi na kwanaki uku. Siyam ta sha gaya masa ranar sallah kwalliya ake yi da sabbin kaya don neman lada bai san meyasa ya kasa mantawa ba. Musulmi a Turkiya sun yi celebrating sallahr Idi tare da shi a masallaci, sakamakon wani makwabcin sa da ya buga masa kofa a ranar sallah, ya ce ko zai fito su tafi masallacin idi tare?. Kasancewar a ranar an rufe gidan radiyon TRT na tsawon kwana uku don taya al’ummar musulmi murnar zagayowar ranar farin cikinsu, kuma sai bai yi musu ba, ya koma ya dauro alwallah ya bi mijin Ahlam wato Suhail zuwa masallaci.

A hanya ne yake gaya masa, kwana uku da suka wuce matar sa Ahlam ta gaya masa ta kai matarsa asibiti, amma an sallame ta yanzu ko? Shi Hamzan da sister din sa sun je asibitin sun tafi da ita gida. Ya yi masa jaje ya ce, Allah ya kara lafiya. Can kuma ya tambaye shi.

“Amma ya aka yi ka bar matar ka a waje ita kadai alhalin ka san ba ta da lafiya ka tafi wani waje? Mai daki na ce min ma juna biyu ne da ita.

Shi dai har lokacin bai ce komai ba, illa zuciyar sa nata fassara masa wadanda suka zo suka dauki Siyama din, tun da an ce har da mace mai yiyuwa Omar ya kira Wasila ya ce su zo su tafi da ‘yar su da ya sace musu, ko kuma ya kira Nasara sun tafi da ita. Ba irin baragurbin tunanin da bai yi a kai ba. Wata shaidaniyar zuciyar ma gaya masa ta ke zuwa yanzu sun cire masa dan sa daga mahaifar Siyam, wato sun yi terminatingpregnancy din, tunda ba sa so ya haife musu sikila a family.

Suhail Nadir bai ankara ba sai ganin hawaye ya yi a idanun Hamzah. Duk da kokarin dauke su da ya yi cikin dabara da zara-zaran ‘yan yatsun sa guda biyu.

Shi kuma kawai sai ya ji Allah ya sanya masa kaunar Hamza Mawonmase. He has been watching him on TRT News tun fara aikin sa da su, kafin hakan ya san fuskar shi a matsayin popular face daga gidan radio da talbijin na VOA da suke ji da broadcasting din sa. Don haka he was an old fan of Hamzah kuma yana son sa sosai. Gani ya yi duk maraicin duniya da damuwar rayuwa ya bayyana a kan kyakkyawar fuskar sa ta mutanen Berom, wadanda tun salsala tarihi da binciken masana ya nuna daga Ethiopia suka bullo. Suka yi naso cikin kasashen Africa ta yamma.

Shi Suhail Nadir malami ne a jami’ar Istanbul da ke karantar da African Studies, don haka yana da sani sosai a kan tribes, culture da traditions din kasashen Africa. He became highly fascinated ga nutsuwa da gentleness din Hamzah ba tun yau ba, ya ji yana matukar son abokantakar wannan mutumin na Africa, matashi mai ilmi da wadatar jini a jika, wanda tun rana ta farko da ya fara ganinsa yana broadcasting a VOA he admires him, ya shiga tunanin yadda zai samu damar abokantakar sa. Sai kuma gashi a TRT rana daya ta kasar su wato Turkiyye, ya dade yana tunanin yadda zai yi ya hadu da shi in person, ko da in ta kama zai yi tattaki har TRT ne. Ba da jimawa ya gane Hamzah  makwabcin sa ne ma anan cikin shiyyar TaksimSquare. Duk da haka bai taba kula Hamzah ba, to rayuwa ce ake ta babu ruwan kowa da kowa, shi ya sa bai taba gwada yi masa magana ba. Har zuwa ranar da matar sa Ahlam ta gayamasa ta kai matar gidan nan na kusa da su asibiti, ta gan ta kwance unconscious a terrace din gidan su. Ya ce, “Kin fa yi karambani, me ya sa ba ki fara kiran mijinta ba?”

Ta ce, “Ta ina zan kira shi alhalin ba ni da lambarsa, kuma ba ya nan? I just did what’s needful to save her, and to save life. Besides, ta kira su da kan ta da ta farfado sun tafi da ita.

Don haka yau din da ta kasance ranar Idin karamar sallar musulmi Nadir ya ga cewa bari ya yi breaking the silence din dake a tsakanin su da makwabcin nasa ya gwada yi masa magana tunda ya fahimci shi ma Musulmi ne, ya taba haduwa da shi yana sayen dabino da zam-zam a shagon Musulmi farkon watan ramadhan.

Shi ne ya buga masa kofa ya ce ya fito su tafi sallahr Idi tare. Aka yi sa’a Hamzan bai yi musu ba, da karramawa sosai ya karbe shi har falon sa, ya shiga toilet ya yi alwalla kafin ya fito Suhail ya kirga kwalaben barasar da ya gani zube a tsakiyar falon sun fi dozen. And now, he burst into tears a gaban sa da ya yi masa tambaya a kan matar sa.

Ganin Hamzah bai da niyyar ba shi amsa ya sa ya kyale shi. Har suka zo gida ba wanda ya kara ce da dan uwansa uffan. Har Hamzah ya yi masa godiya zai fita daga motar kasancewar a motar Nadir din suka je masallacin idin sai Suhail Nadir ya ce da shi”.

“Ka zo mu je gida na, mu ci abincin sallah tare, tunda Madam ba ta nan”.

Har zai ce a’ah ba ya iya cin komai sai barasa, ya ga hakan zubewar mutuncin sa ne. Giya abar kyama ce sosai a wajen ‘good muslims’ and tana daga manya-manyan abubuwan da suka lalata zamansa da Siyam, suka rage mararin son da ta ke masa, suka rage masa kima da darajar da ta ba shi, har ila yau suka sa tafi ganin kimar dan uwan ta Omar, tunda shi yaushe rabon ta ce masa I love you Shaheed ko Habeeby? Ya koma Hamzan sa gatsau a bakinta. Kuma duka ba komai ya jawo masa wannan faduwar kasa warwas ba da zubewar kima a idon Siyamah sai SAKACI da addini (kamar yadda ta ke cewa) tare da rike giya da ya yi a matsayin maganin damuwa da yaye bacin rai.

Yau da yake Allah ba azzalumin Sarki ba ne, ya kawo mata Omar har inda ya gudu da ita. Shi da kan sa ya dauko passport dinta ya ba ta, ya kuma kore ta daga gidan da yake ta kulle ta din shekara guda wanda ke nufin, ya ba ta licence na ta tafi gaban iyayen ta tare da Omar, wanda ke  nufin ya bata dama ta zabi ci gaba da zama da shi ko ta zabi bin iyayen ta ta shirya da su ta hakura da shi da auren sa.

Shi kuma ya tashi a tutar babu, ya shigo musulunci a banza zai fita a wofi, domin ya kasa tsare iyakokin sa, ya kasa rike shi da hannu bibbiyu. Zai kare ne a tutar wofi; babu islam haka babu Siyama. Duk kuma ba komai ya jawo masa ba sai SAKACI da wasa da addini. Wadanda inda ya rike su tun farko yadda ya kamata, Siyam, zuciyar ta daya ce a kan sa, ya yarda da hakan yana sane yake canza mata manufa akan Omar, tunda ai a kan kada ta auri Omar din ne ta kusa hallaka kanta ta kuma sabawa iyayenta da yake ganin suna son kwace ta yanzu.

Idan kuwa har Siyam ta tona sirrin zaman su da dabi’un da yake ciki ga Ya Omar ko iyayen ta sai inda karfin su ya kare wajen raba su in har yanzu suna son ta a matsayin su na iyaye. Ba ta inda za su kyale ‘yar su girman musulunci haihuwar musulunci da mai shan giya ya yi ta duka da kin yin sallah da kiyaye janaba har ma da wasa da azumi ya ci gaba da auren ‘yar su.

Hamzah sai ya ji bakidaya ya tsani kan sa, yana kuma matukar tsoron hada hanya da iyayen Siyama da ita kan ta Siyamar da yake ji a halin yanzu ta yi masa fintinkau kenan.

Abincin da Ahlam ta hada musu mai rai da motsi na mutanen kasar Turkiya wato Adana Kebab wa Ful wa Tamis ko loma daya bai iya yi hadiye ba. Ya maida cokalin ya aje, ya kasa hadiye abincin, duka Suhail na kallon sa. Kawai sai ya mike ya yi excuse wa Suhail din, ya ce zai koma gida akwai abin da zai yi ba zai iya cin abincin ba.

Suhail ya dube shi cikin tausayi ya kudire a ran sa daga yau zai shiga rayuwar Hamza Mawonmase saboda ya hango nadama ta gaskiya  a tare da shi, zai yi kokarin da zai taimaka masa ya yi overcoming challenges din sa a rayuwa musamman shan giya a matsayin sa na musulmi, zai taimaka masa in har da gaske yana so ya daina, being a good moslem is only by Allah’s favour, wanda duk yanda munka yi don mu shiryar da bawa ba zai shiryu ba, idan Ubangiji bai so shi da rahmar wannan rahmar ba. Ubangiji ya so Hamzah da rahma tunda duk da yana shan giya to ya shaida babu sarki sai Allah kuma Annabi Muhammad (S.A.W) Manzon sa ne kuma bawan sa ne, sannan yana sallah from all indications da ya gani, da baya yi kwata-kwata ko da ba musulmi ba ne ba zai yarda ya bi shi sallar Idin ba.

Da wannan, Suhail Nadir, ya bi shi da kallo har ya fice da takun sa na sassarfa. Kuma yana fita daga gidan Suhail, gida ya koma ya kulle kansa ya kifa kai a kan makeken gadon sa. Ya rasa inda zai sa kansa, ga kewar Siyam ga soyayyar ta da ke ninkuwa duk bayan kowacce dakika, ga rashin sukunin zuciya irin wanda rashin tsaida sallah ke haifarwa wanda ya yarda shi musulmi ne. Jikin sa gaba daya ya yi nauyi, ya saki har ya zamanto ba shi da karfi ko kuzarin da zai iya daga kwalba, wadda yake jin daga yau ko kuncin rayuwa zai kashe shi ya bar ta har abada tunda ita tayi masa sanadin rasa Siyamah.

A cikin wannan halin ne wayar sa da ke daidai hannayen sa ta yi kara. Abin da ya sa ya dago kenan da idanun sa da suka kada, ya kai ganinsa ga fuskar wayar. Bakuwar lamba ce ke kira, amma daga nan cikin Turkiya. Ya samu kansa da amsawa without a second thought kamar a mafarki, sai ya ji siririyar muryar Siyam tace, “Habeeby”. Da wata murya da ya yi kewar ji, tun wani zamani na ire-iren renakun Miami resort da rayuwar amarcin su.

Kasa amsawa ya yi, sai da na sake maimaitawa a karo na biyu na ce, “Shaheed, are you online?”

Nan ma Hamzah shiru ya yi yana kokawa da emotions na soyayyar data yi masa katutu, da kishin dake son cin karfin sa. In ya tuna duk yadda aka yi duk kuma ta inda aka je aka dawo Siyam na tare da Yayan ta Omar a halin yanzu, amma ya yi kokarin dakile tasirin wannan kishin tunda ita ta kira shi da kan ta duk da korar karen da ya yi mata.

“Na kira ne bisa umarnin Ya Omar na in kira in baka hakuri, in kuma yi maka bayanin da ban yi a baya ba. Cewa na hadu da Ya Omar da matarsa a asibitin Medicania ranar da ka kai ni awo. Tsoron irin reaction din da za ka dauka a kaina ya hana in fada maka gaskiya tun a lokacin saboda na san in ranka ya baci you are not giving things a second thought.

Ya ce in zai yiwu, yana son ganin ka nan gidan sa gobe a matsayin sa na Yayana domin mu shirya tafiya gida dukkan mu, ya ce, you have to buy the courage and become bold enough to face Abba haka, a yi bridging the gaps, a yi ta a kare, kowa ya huta da fargaba da bacin rai, za mu karbi duk hukuncin da Abba ya yi mana ne da hannu bibbiyu. Don’t forget one thing, Ya Omar already yana da matar sa Kausar da dan sa Aryan ba abin da zai yi da wata matar ka mai kama da nunar rana. Na kuma gode da kora Shaheed, na gode”.

Daga haka na kashe wayar, jin kuka na son bayar da ni bayan kuma yanzu I want to be stronger and bold enough to face my father for forgiveness and repentence, ko na samu saukin al’amura na da kwanciyar hankali irin na Kausar a rayuwa ta. Ba soyayya ce a gabana ba.

An yi wa Anti Kausar surgery a washegari, kuma daga abin da likitocin da suka yi mata aikin suka ce shi ne, the surgery was not successful. Ko za ta kara haihuwa sai dai ta hanyar artificial insemination din again. Wannan ya sa dukkan mu a ranar cikin wani yanayi mara dadi muke. Wajejen karfe hudu na yamma kawai na ga sakon Hamzah a wayata.

“Send me the address of Ya Omar’s house”.

Sai na ji idanuna sun cicciko da kwalla, at last, Hamzah na Hamzahna ne kowanne irin bacin rai ne zai gitta a tsakanin mu.

A takaice na rubuta masa.

“Come to Medicania, female surgical ward….”

Ina cikin hada wa Ya Omar shayin da zai sha don tun jiya ya kasa cin abinci, ba ya son wannan haihuwar ta insemination sai don ba yadda za a yi, ya so a samu nasara kafin mu koma gida, yadda ba wanda zai san ma yadda aka yi suka haifi Aryan.

Murda kofar muka ji an yi, hadi da sallama, kamshin Guerlain Vetiver shi ya fara bakuntar hancin mu, kafin mamallakin sa Hamza Mawonmase ya bayyana a dakin.

Har zuwa lokacin Aunty Kausar ba ta farfado daga allurar tafi da ranki da aka yi mata ba, wato anaesthesia. Ya Omar yana zaune gaban gadon ta rike da hannayen ta ni kuma ina tsaye jikin cabinet ina hada masa shayi, a haka Hamzah ya shigo ya tadda mu.

Ya Omar ya amsa masa fuskarsa ba yabo ba fallasa, sannan ya ba shi kujerar roba da ke fuskantarsa don ya zauna, yana cewa, “Jabbama-jabbama”.

“Jabbama  koduda esam am Hamzah (Lale maraba da surukina Hamzah).

Hamzah sai ya ji kamar ya yi kuka, ashe haka ya Omar din ke kama da Boddo in sun hadu wuri daya a zahiri? Ashe haka Omar din ke da kwarjini da haiba yake kishi da shi a banza? Omar ya wuce da tunanin sa, sannan kamewar sa da karamcin sa har ma da nuna halin girma ya gama sayo masa martaba a idanun sa.

Ya yi regretting reactions dinsa a kansa, ashe shi tuni ya kama dahir yana da kyakkyawar bakar matar sa har da cute yaro haka ya tsaya yana bata wa kansa rai da lokaci a banza, from all indications Omar bai da abin da zai ci da Boddo yanzu, a irin wannan santaleliyar mata wanke hannu ka taba mai kama da jinin sarauta da Allah ya yi masa sakayya da ita. Duk sai ya ji kunya, nauyi da nadama sun kama shi.

Aryan ya yo gare shi ya kama hannun sa yana fadin, “Sannu da zuwa Uncle. Kai ne Baban Anti Siyama?”

Dariya ya yi ya zauna, tare da dora yaron a cinyoyin sa. Na saci kallonsa gaba daya ya rame ya koma kamar wanda ya tashi daga jinya, duk da cewa still yana nan a dan gayen sa Hamzah Al-Mustapha da na sani. Ya sha sabuwar shadda mai maiko wato Sheraton, ya bai ma ya Omar hannu suka yi musabiha. “Ashe mara lafiya ce da ku? Allah ya bada lafiya, Ya sa kaffara ne.”

Ya Omar ya amsa, “Eh wallahi, amin Ya Rabbi.”

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Sakacin Waye? 64Sakacin Waye? 66 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×