Skip to content
Part 66 of 73 in the Series Sakacin Waye? by Sumayyah Abdulkadir Takori

Duk sai suka yi shiru, kowanne na jin nauyin dan uwansa, ya rasa daga ina zai fara.

Na kawowa Ya Omar shayin sa da na kammala hadawa na juya zan wuce toilet don yin alwallar la’asar, Ya Omar ya ce, “Boddo am, nonnon be jabata kodo? Do na tarbiyya je be wanni ma ba. Kodo kam handanai ni sam ha amin sakko gorkoma” (haka ake karbar bako? Wannan ba tarbiyyar da aka yi miki ba ce. Mu bako abin darajjawa ne da girmamawa a gare mu ko wane ne, balle mijinki).

Zumbura baki na yi, ni ma na mayar masa da fulatancin don dai in samu in kular da Hamzah, don na san ba ya jin ko alif a ciki.

“Konko mo farti am? To warino be tsautsayi hunde fere hebi am bo? (Shi da ya kore ni? Da ya zo da tsautsayi wani abu ya same ni fa) nan da nan na shiga kuka ina share hawayen da gefen gyale na ina cewa, “An jei vi dona mo sai a jabba mo no handi kadi.”

Ma’ana (Kaida ka ce a kirawo shi sai ka karrama shi din)”

Abin nawa har da tsohuwar shagwaba irin wadda na dade, na jima ban samu na yi wa Ya Omar irin ta ba, bayan a da can kullum sai na yi masa ita.

Ai kuwa nan da nan ya rude shi ma Hamzan zuru-zuru ya yi don bai san me muke cewa ba, amma from all indications and facial expressions ya fahimci Omar ya fi maraba da zuwan sa fiye da ni, da kuma ya tuno irin korar da ya yi min ina rokon sa kada ya sake ni sai ya ji duk ya kara muzanta, nadama goma da ashirin ta lullube shi.

Yana da nasa natural techniques din na lallashin Boddo, amma ba zai taba yi a gaban Ya Omar ba, wanda ya koma masa a ido tamkar Abban da ya haifi Boddon saboda tsananin kamannin su da juna.

Cikin lallashi Omar ya ce, “Duk na ji na yarda, amma ai duk a cikin fadan masoya ne, balle fada na Siyam da dream husband dinta, wa ya isa ya shiga bai sha kunya ba?”

Hamzah ya yi ‘yar dariya kasancewar Ya Omar da hausa ya fada, har yana wara hannuwa yana yarfar da su irin wa ya isa din? Ya kara cewa, “Babu! Sai shaidan la’ananne kadai, shi ma kuma in ya dage sai ya shiga tsakanin Siyam da Hamzah kunya zai ji. Yanzu dai ki zubo masa shayin shi ma.”

Na daure fuska sosai na ce, “Tunda ka damu sai ya sha, kana iya hakura ka bar masa naka.”

Ya Omar ya ce, “Wannan abu mai sauki? Hamzah have my tea. Annabi Sallallahu alaihi wasallam ya ce, ‘Bakon ka Annabin ka.”

Ya mika ma Hamzah tea din.

Shi kuma ya ki amsa yana fadin, “In ba za ta hada min wani ba Ya Omar ka kyale ta, don na zo gidan su ne kuma ba wajen ta na zo ba Allah ya sani wajenka na zo, don ta ce min kai ke kira na.”

Ya Omar ya ce, “Kayyasa! Kai da ka yi kora kuma maimakon ka yi ta lallashi sai ka fi mai kora shafawa?? Korar ta kayi fa! In rai ya baci hankali ba ya gushe ba, yau da bata rike lambar waya ta a kan ta ba ina kake tunanin zata je ga ciki? Ban ji dadi ba ko kadan, kuma rai na ya baci da farko, duk da cewa Boddo ta yi laifi bai kamata ka biye zuciya ba don hankalin ku ba daya bane. Ba’a biyewa mata don wataran zasu sa ka ka yi abinda zaka zo kana nadama.”

Hamzah ya dukar da kai ya amshi laifin sa gun Ya Omar yayi ta bashi hakuri, the apologizer Hamzah Mawonmase ban hakuri ba abu ne mai wahala a gare shi ba. Kafin ya ce.

“Ya Omar ba ka san Siyam ba ne wani lokacin lallashi ba ya biyar da ita sai wuta, haka itama bata lallashin mutum, ita in tana son mutum ya yi abu, to ba za ta lallashe shi ba, sai dai ta yi ta fushi da shi a tunaninta fushin ta ne zai sa ya yi yadda ta ke so”.

Omar ya dora kafin Hamzah ya rufe bakin sa.

“Ni kuwa na san ta. Ni kuwa na san ta da wannan halin tun tana tsumman goyo. Kafiya da naci kan abinda take so. Namiji kuwa kamar yaron goye ne, ya fi son lallashi a kan tsawa da tsiwa, kuma ya fi biyuwa ta sauki in aka lallashe shi. Fushin sai dai ya sa ya kara botsarewa.”

Ni dai na shige toilet na barsu suna ta caccakata, Hamzah na ba shi labarin irin yawan fushi na, ya ce, “Sai ta yi wata guda ba ta yi min magana ba wai tana fushi na kin yin sallah on time ba. Ni na rasa irin wannan abu, shin mata da miji kabari daya ake binne su ne?”

A nan ne Ya Omar ya bi baya na, ya ce, “Soyayya ce ta sa ba ta so ta riga ka shiga aljannah, ko Allah ya musanya mata da mijin aljannah (zauj Al-een) a lahira, ta fi so ku zama mata da miji a duniya da lahira, ku kuma tashi gaban al’arshin Ubangiji tare matsayin ma’auratan da suka so juna saboda Allah, suke son juna da rahmar Allah”.

Sai jikin hamzah ya yi sanyi, ya kasa cewa komai, Ya Omar don ya ba shi kwarin gwiwa ya ce, “Amma da gaske fushi ba ya biyar da mu, she could have adopt another strategy ban da fushi. Kina ji na ko Boddo?”

Daga toilet na yo masa gyaran murya, “Uhm.”

Duk suka bushe da dariya.

Ya Omar ya gaya masa cewa, makasudin kiran shi ne, ya sanar da shi in zai yiwu ya dauki hutu ko na sati biyu ne mu tafi gida gaba dayan mu tare, zai gabatar da shi ga Abba da Ummati, zai kuma yi kokarin komai ya daidaita tsakanin mu da iyayen mu, because we need their blessings.”

Ya kara dacewa, “Ka yi wa Young Abba laifi mai girma, you need settle it also, dauke Boddo ku bar kasa ba solution ba ne na kada a raba ku, zai kara fusata iyayen ta ne, kowa fa yana son dan sa Hamzah.”

Young Abba bai cancanci ku taho wata kasa ku kafa rayuwa ba da saninsa ba, duk da cewa, matarka ce kana da damar kai ta ko ina ka ke so ku rayu. Amma ban da parental deprivation. This could in turn affect her mental and psychological well being za su hana ku samun albarkar iyaye a tare da ku. Za ka so naka surukin ya raba ka da ‘yarka da ka haifa, ka rabu da ita ba don ba ka sonta ba sai don bakin cikin ta ki yi maka biyayyah?”

Hamzah ya hau girgiza kai da sauri, “Ni ma na sha yi mata wannan gorin cikin bacin rai, don na tabbata rashin albarkar Abban ne ya hana mu samun kwanciyar hankali. Ba ta kyauta ba, amma na fi yarda da cewa rabo da kaddarar da ke tsakanin mu mai karfi ne kuma rubutacce ne shi ya kaita ta ga tsallake umarninAbba har ta cimma kaddararta.

Boddo I’m sorry for everthing! Idan na ce komai ina nufin komai.”

Ina gab da tada sallah ya zo gabana ya hada hannuwana cikin nasa yana wannan rokon, ya ce, “Boddo am, I’m sorry (wai shi ma ya kwaikwayi Ya Omar).”

Na ce, “Ka matsa Malam, sallah zan yi.”

Ya ce, “Sai kin ce kin yafe min Malama, tun daga kan SAKACI da addini, kora, gori, duka, everything! Gani durkushe kan gwiwoyi na yau a gaban ki ina mai amsa dukkan laifuka na.”

Ya Omar ya kasa jure ganin irin kallon da ke fitowa daga almond shaped eyes din Hamzah kai tsaye zuwa ga na Boddon, wadanda ma’aurata kadai suka san ma’anar irin wannan kallon, a ka ce zuciya bata da kashi, balle irin tasa a kan Boddon sa, wadda ke kokarin rusunar da nata idanun sabida kunyar Yayan nata, na ce, “Malam ka matsa, cikin mutane ne fa.”

“Ba wasu mutane anan, banda Yayan mu da Antin mu, don sune shaida na cewa kin yafe min kada mu koma gida ki ci gaba da gasa ni ya waina a tanda, wallahi na nutsu. Na daina duk abin da nake yi daga yau, idan na sake ko daya, Ya Omar ka yi hukuncin da ya dace a tsakanin mu.”

Kan Ya Omar na kan wayar sa, ya ce, “Boddo am, ki yafe mana! Allah yana son masu afuwa.”

Na saka kuka, ina fadin, “Ya Omar Hamzah green snake ne, ko ya bar komai ya kuma tsaida sallah ba zai bar giya ba. I know him better than you do, kada marairaicewar sa ta sa ka ji wani tausayin sa. Na rantse Hamzah ba abun tausayi bane. Gobe zaka gan shi da kwalbar barasa.”

“Ni ma ban ce a ji tausayi na ba, tausayin Ubangiji kawai nake so a bisa dukkan kurakurai na, don shi nake saba wa ba ke ba. Astagfirullah! Astagfirullah wa’atubu ilaihi.

Ke afuwar bacin ran da nake saka ki a ciki nake nema, kin ji Sweetheart? Siyam din Hamzah, Boddon Ya Omar… Azumin Ummati… Siyaman Abba…”

Ai kuwa na idasa rushewa da kuka, na ce, “Kana so in yafe maka? To ka shirya mu tafi wajen Abba tare da kai, ka baiwa Younng Abba hakurin laifukan da ka yi masa.”

Ya ce, “Na yi wannan alkawarin Boddo-Siyamah! Kuma na yi alkawarin daukar duk hukuncin da Abba ya zartar a kan mu.”

A daren dai shi kadai ya koma gidan sa don na ce ni jinyar Anti Kausar nake yi a asibitin. Ba musu ya amince don lallaba ni suke yi.

Kwanan Anti Kausar hudu kafin a sallame ta daga gadon asibiti.

Kafin kuma mu koma gida sabon passport dina ya zama ready, Ya Omar ya karbo ya hada da na Hamzah da nasu gabadaya ya fara yi mana shirin izinin tahowa gida, da komai ya kammala  ya saya mana tikiti bakidaya har Hamzahn. (Halin girma a cikin jininsa ne).

Ana-i-gobe za mu taho Najeriya Ya Omar ya dage sai na hada komai nawa ya kai ni gidana, na yi kukan shagwabar na yi komai amma ya ki jin tausayi na ya ce, Hamzah zai daina ganin girman sa. Besides, duk kawaicin da ya kamata ya yi a kan zamansa shi kadai ya yi, kada abun ya koma da daukar hakki.

Ita ma Aunty Kausar duk da jikin ta ba karfi a kwance ta ke ta yi magana wannan karon, ta ce, “In yi hakuri in tashi Ya Omar ya maida ni, wannan shi ne girman sa, in yaso gobe sai su biyo su dauke mu zuwa airport mu tashi. Ta yi kasa da murya ta ce, “Kuma kin ga har a cikin idanun sa cikin ragaita yake, those almond shaped eyes expressed how much he missed you.”

Dariya na yi, na kuma rufe ido cikin jin kunya. Ta dauko wasu tablets da ita kadai ta san amfanin su da turarukan humra na asalin Dikwa ta ba ni da sauran tarkace amfanin matan aure.

Aryan kuka ya saka a kan sai dai mu tafi gidana tare amma iyayen suka ki. Dole Aunty Kausar ta kama shi suka koma cikin gida, mu kuma muka wuce Taksim square.

Hamzah bai san da zuwan namu ba, kawai ya yi kararrawar zuwan baki ya zo ya bude kofa. Daga shi sai farar singlet da dogon wandon jeans. Ido hudu muka yi ni da shi. Ya dan tsura min ido, ya kuma cusa hannun sa a cikin sumar kan sa yace “ko dai gizo ido na ke min Sweetheart?” Kafin ya hango Ya Omar daga baya na kunya ta kama shi, ya soma sosa keya yana lale da Ya Omar, Ya Omar sai ya ce, ba sai ya shigo ba yana sauri gobe in sun biyo daukar mu sun shigo. Mu hada kayan da za mu tafi da su kafin gobe. Hamzah godiya har da durkusawa kai ka ce Ya Omar din ne Abba. Ya Omar na bada baya ya rufe kofar ya kuma sunkuce ni zuwa dakin barcin mu (master bedroom). In da nan take halin mu na mata ya motsa na soma zillewa. Hamzah kuma ya nuna bai san wannan yaren ba.

“Yi a hankali dai, Mr lover man, an ce ‘yan biyu ne a kwance a gicciye, in ka wujijjiga su da zungura kai ka sani.”

“What? You mean…..?”

Na samu damar zamewa ya sake riko ni cikin rawar jiki. Na sunne kai a kasan katafaren kirjin sa na soma kukan kissa, “ka kore ni da ciki me zaka ce min in yarda kuma?” Hamzah ya rufe ni da sumba ko ta ina yana fadin, “na tuba fa, na tuba na bi Allah na bi ki har a gaban Ya Omar na jaddada tuba na bisa wannan laifin, kada ki zamo cikin mata masu mita a kan laifin da mijin su ya yi musu.

Ki taimake ni uwar ‘yan biyu zan bi ki a hankali (so soothing and so romantic). Tabbas “Hakuri mai tadda rabo” na yi hakuri da rashin wancan Allah zai mayar min da guda biyu a lokaci guda.”

Alhalin ba ni da wani nagartaccen aiki da na cancanci wannan kyautar daga Ubangijin sammai da kassai, lallai ne shi Sarki ne da babu kamar sa wajen kyautayi ga bayin sa, hakika ba ni na bai wa kaina ba. It’s ALLAH’S GIFT.”

Ya dire ni a kan gadonsa mai dauke da watermattress, ya zube gwiwoyin sa a kasa, ya soma sumbutar tafin kafata tun daga kan babbar yatsar kafar tawa yake moving upward zuwa sama da wata irin sumba mai ratsa zuciya da bada sauti, mai tsayi da zurfi wadda ke fitowa tun daga karkashin zuciyar sa. Yana fadin “Boddo ki yafe min, na tuba na bi Allah daga yau na bi ki.”

Da ya iso kirji na kuwa sai da ya furta, “Ya Subhnallah”. Ganin yadda suka kara kasaita suka tumbatsa tamkar za su tsage sabida shayarwa ta kusa isowa.

Hamzah ya gigice ya kidime, ni ma kuma gab yake da ya zauta ni da irin sumbatar da yake yi wa kirji na bayan ya zare duk wata suttura da ke jiki na ya manna ni a jikin sa.

It was a wonderful and sweet night then ever!

Ana tafka ruwan sama a lokacin kamar da bakin kwarya mu muna tafka soyayya kamar ba za mu rage wa gobe ba. Sai da na tausaya masa na kuma tausaya wa kaina, ranar da wata kaddara ta gifta ta katse wannan jin dadin da ke tsakanin mu, ko ya ya rayuwata da tasa za ta iya kasancewa?

Ganin cewa sati biyu kawai da muka yi ba tare da juna ba sun sa tamkar ran mu zai fita kafin mu samu kaiwa ga ecstasy, kafin mu samu contentment a cikin jikkunan mu, ruhi da zukatan mu.

Alkawura iri-iri na Hamzah ya daukar min a daren yau, wadanda kuma haka suke har zuciyar sa, yake rokon Allah ya bashi ikon cika su a sauran rayuwar mu mai zuwa har zuwa tsufa ko karshen numfashin mu.

Washegari tun karfe tara na safe kararrawar su Ya Omar ce ta tada mu daga barcin da muka koma bayan sallar asubahi. Su suka zo mana da abin da za mu ci a cikin food basket. Tare dukkanmu muka yi breakfast a tsakar falonmu a kan ledar cin abinci.

Aunty Kausar na ta tsokanata, “Amarya kin sha kamshi! Kinga yadda kike sparkling?”

“Ango sai kyallin goshi ka ke.” In ji Ya Omar.

Mu dai duka sai murmushi muke yi wanda aka ce labarin zuciya a tambayi fuska, daren jiya babu kamar sa a tarihin rayuwar auren mu don ko first night albarka, Ya Omar ya taimaki aure da ya maido masa Siyam daren jiya suka yi kwanan sallama, juna biyun bai hana komai ba, sai ma kara armasa masa komai da ya yi, wannan kuma halittace kuma kyauta ce ta Ubangiji ga mace mai juna biyu, inda zaka samu mace duk rashin ni’imarta in tana da ciki sai ta koma shu’ara, ba ta gundurar miji, shi ma ba ya gundura da ita sai ma wata sabuwar samartaka da ta dawowa Mr. Hamzah. Hadiya Siyam ne kurum bai yi ba, shi ma don ba zai iya ba ne, amma babu inda bai bi ya side ya tande a jikin Siyam ba. It was just an amazing and splendid night ga ma’auratan.

Da muka fito daga gidan dukkan mu zuwa motar Ya Omar Hamzah ji ya yi kamar ana warning din sa, ya ja Siyam su koma cikin gida su ci gaba da kyakkyawar rayuwar su a haka. Ji ya yi kamar in sun tafi ba za su dawo ba, kamar tafiyar kenan, kamar karshen komai tsakanin sa da Siyam kenan, kamar Abba ba zai bar masa matar sa ba, kamar karshen rayuwar sa ya zo muddin ya sake Siyam ta taka gidan Abba.

To amma me ya isa ya yi a daidai wannan lokacin da har ga su suna taka matattakalar jirgin Turkish Airways, wanda kai tsaye ma a birnin Tarayya (Abuja) zai ajiye su.

Abin yin kawai shi ne, karfafa imani da dammarar daukar kaddara mai dadi da mara dadi. Allah shi kadai ya san abin da Ya boye cikin wannan tafiyar.

A cikin jirgi, daidai jikin tagar dama ta barin (economy class) can na hango Siyam kwance a kafadar mijin ta Mawonmase. Ta rufe ido ruf, ita ma shigen irin nasa tunanin ta ke yi. Cewa idan Abba ya ki karbar Hamzah ko ya ya rayuwata za ta kasance? Abin da na sani, nake kuma da tabbacin sa a yanzu shi ne; a shirye nake wajen daukar hukuncin Abba komai tsaurin sa don samun rabauta a duniya da lahira, in ba haka ba na tabbata na kuma amince wannan jin dadin da fahimtar junan da muka samu a banza man kare zai kare. Kwanciyar hankali na dindindin babu shi a gare ni ba tare da albarkar Abba ba.

Da wannan tunanin na kwarara zuciyata na kuma karfafa ta da ta zama mai karfi, mai juriya mai halin daukar kowanne irin laifi Abba zai tuhume ni ya kuma hukunta ni da shi in dai a karshe zai yafe mini, ko da hakan na nufin rabuwa da Hamzah ne.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Sakacin Waye? 65Sakacin Waye? 67 >>

1 thought on “Sakacin Waye? 66”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×