Skip to content
Part 67 of 73 in the Series Sakacin Waye? by Sumayyah Abdulkadir Takori

DR. MAMMAN GEMBU

Yau tun safe da ya tashi da Siyama ya tashi a ran sa, yayi mafarkin wai ga ta tana ta binsa tana kuka ya ki kula ta, ga Omar tare da ita yana ta cewa, “Abba ka yafewa Boddo na”.

Da wannan ya tashi a ran sa wanda ya sa begen ‘ya’yan nasa guda biyu da kewarsu ta addabe shi. Har Wasila da ke hada masa shayi ta lura ya yi zugum cikin tunani. ‘Yammatan Abba wato Maryam-Jamila da Shukra-Nadiya na ta ba shi labarin primary school graduation din su da aka yi jiya da bai samu damar zuwa ba, amma Wasila da ta fahimci hankalinsa ba ya jikin sa, sai ta ce,

“Don Allah ku kyale Abba da labarin nan haka, ba jin ku yake yi ba, ku je ku yi wanka tunda gobe ne tafiyar ku Mambillah, kowacce ta hada kayan da za ta tafi da su, ku yi wa kanin ku wanka ku shirya shi kuma”.

Da gudu suka tashi cikin rige-rigen cika umarnin ta, don yara ne masu tarbiyyah da jin maganar na gaba (ba irin Siyama sarkin taurin kai da tsayawa a kan ra’ayin ta ba), su wadannan Shukra da Jamila akasin Siyam aka samu ta ko ina. Kuma ganin irin matsalar da aka samu wajen tarbiyyar Siyama yasa Wasila bata musu da wasa.

Bayan wucewar su Wasila ta lura har zuwa lokacin Abban bai san me suke yi ba ga dai shayi a gabansa yana ta juya shi da cokali, amma ya gagara kai wa bakin sa. A karshe ma sai gani ta yi ya mike hadi da ce mata zai yi wani aiki a system dinsa, kada kowa ya dame shi. Cikin damuwa Wasila ta ce, “Toh Abba, a fito lafiya”.

Ya shige sassansa ya rufo kofar tare da murza mukulli.

Kasancewar saukar safe muka yi a Abuja daga Istanbul kuma Ya Omar ya gaya min su Young Abba ma za su taho shi da Anti Nasara, amma jirgin dare za su biyo daga U.S, don haka karfe goma na safe muna kofar gidanmu.

Ya Omar na danna kararrawa kafin ya murda kofar ya tadda ita a bude, muka saka kai dukkanmu bakin mu duka dauke da sallama, zukatan mu kamar su fito daga allon kirjin mu da dokin yin tozai da Abba, fargaba, taraddadi da tsoron abin da zai je ya zo.

Don kuwa ba mu sanar wa kowa muna tafe ba. Ban da Anti Nasara da Ya Omar ya kira ya gaya wa tahowar mu tun farkon da Hamzah ya yarda za a taho din. Ta ce in mun saka date ya gaya mata su ma za su yanki tikiti daidai lokacin tahowar mu su taho mu hadu a gidan Abba gaba daya. Don haka su ma suna hanya yanzu ko kuma sun riga mu sauka.

Anti Wasila ce kawai a falon lokacin da ta amsa mana sallama muka shiga ba tareda ta dauki murya ba. Ya Omar ne a gaba, ina biye da shi, rike da hannun Aryan, sai Kausar a bayana, ban san me ya sa Hamzah ya tsaya daga waje bai karaso ciki ba.

Idona ya fada cikin na Anti Wasila, sai ta mike tsaye tana hailala tana salati, ta kalle ni ta kalli Ya Omar da yaron da ke hannuna mai tsananin kama da Omar, sai kawai ta saka kuka tana fadin, “Siyama da Omar? Ko kuwa idona ne yake min gizo? Irin wanda yake min lokaci zuwa lokaci a kan ku?”

Da gudu na karasa na rungume Anti na Wasila, ina kuka tana yi, Wasilar da ta fara dora ni a kan kyakkyawar turba, ba zan taba mantawa da gudunmuwar ta cikin rayuwa ta ba. Shekaru sun karu mata, amma tana nan a ‘yar gayun ta, mai yawan ado da kwalliya, kai ba za ka ce ta haifi zagada-zagadan yaran da ke gaban ta ba.

Hayaniyar koke-koken mu ta sa Abba da sauran yaran fitowa daga dakunan su. Da dan sa Omar ya fara tozali ya soma kokarin fahimtar su waye a gaban sa. Abbana Dr. Mamman Gembu, har da furfura tsilli-tsill a kan sa da gemun sa. Shekaru sun nausa, amma yana nan a dan bokon sa yadda na san shi mai yawan tsafta da kwalisa.

Ya Omar ya karasa ya gurfana a gaban sa a kan gwiwoyin sa, ni ma na saki aunty Wasila na nufi Abba jiki na yana rawa da karkarwa, na zube a gaban sa na rungume dukkan kafafunsa guda biyu. Na ce,

“Abba na, ga dan ka Omar na nemo maka, kamar yadda ka ce sai na dawo maka da shi zaka yafe mun, mu duka masu kuskure ne, ga mu gaban ka yau dauke da kwandon laifukan mu a kan kawunan mu, ka yi duk hukuncin da ka ga dama a gare mu, mun yi rantsuwa a wannan karon mu masu biyayya ne ga umarnin ka, mu duka ba mu da fuskar da za mu fuskance ka, amma cikin jin kai da YAKANAH naku na iyaye da Allah ya halicce ku da shi a kan mu muke rokon ka ka yi hakuri, ka yanke mana duk hukuncin da ka ga dama in dai za ka yafe mana”.

Kuka sosai muke yi daga ni har Ya Omar, shi ma yau nadamar barin Abban da ya yi ta daddaure shi ta hana shi magana, tsakanin shi da Boddo bai san wa yafi wani rashin kyautawa Abba ba. Abban bai cancanci abin da dukkan mu muka taru muka yi masa ba ko da wasa.

Amma Abba ya ki magana, kokarin janye kafafun sa yake yi daga rikon da muka yi musu ni da Ya Omar, ko uffan bai ce mana ba ya kwace kafar sa ya koma dakinsa ya rufo.

Ya Omar kamar ya yi hauka, ni kuma kamar in zauce, muke rokon Anti Wasila ta bude mana dakin mu sake bin sa. Anti Wasila da ke ta nata ‘yan share-sharen hawayen ta ce, “Duk ku yi hakuri ku ba shi lokaci. Na tabbata yanzu ba zai saurare ku ba. Ku nutsu, ku huta insha Allah komai zai tafi daidai”.

Ta dubi Kausar ta ce, “Sannu da zuwa bakuwa. Barka da zuwa gidanku mai albarka. Maryam-Jamila ki fada wa Talatu a gyara sassan Ya Omar, ke kuma ki share dakin Boddo”.

Maryam-Jamila ta saki fara’a ta ce, “Da ma su ne?”

Na kama hannayen ta ina shafe hawaye na da su, ‘yan kanne na da na raina a hannu na duk sun zama ‘yammata ‘yan karamar sakandire, Shukra-Nadiya ma ta matso tana cewa, “Aunty Siyamar mu, welcome back home”.

Na hada su ita da Maryam na rungume a jiki na, Muhammad Hayatuddeen kuwa ya makale wa Aryan, ya ja shi dakinsa suna wasa.

Cikin dan kankanin lokaci Anti Wasila ta shirya mana abinci, an kai Kausar dakin Ya Omar da ke BQ, Hamzah ya ce ya wuce hotel, shi kam wannan lokacin namu ne da iyayen mu, idan Abba ya yarda zai gan shi sai na kira shi ya taho. Gabadaya he’s upset don na gaya masa mu ma Abban ya ki sauraronmu daga ni har Ya Omar.

Anti Wasila da su Maryam Jamila ne suka shirya abincin a falo, amma Abba ya ki fitowa a ci tare da shi yadda suka saba. Cewa ya yi Wasila takai masa nasa dakin sa, za ta fara lallashi ya daga mata hannu, “Kyale yaran nan Wasila kin ji! In ba so ki ke su karasa ni ba. Tsawon rai na tawakkali ne kawai ya kawo ni yau, don haka tunda dukkan su sun isa zabar wa kansu abin da suke ganin shi ne daidai, to ki kyale su su koma kasar arna su ci gaba da rayuwar su a inda suke yin ta, me suka zo su yi min yanzu? Sun gama biyan bukatun ran su?”

Abba ya dakata ya yi tari, ya ce, “Wasila gaya miki ne ban yi ba, da jimawa likita ya gaya min zuciyata ta tabu, kuma ba komai ba ne, kewar Omar da Boddo ne da na saka wa raina, alhalin su suna can suna jin dadin rayuwar su da abokanan rayuwar da suka zaba wa kan su. Don haka yanzu da suka dawo gare ni me suke so in yi musu? In raba aure ko me? Bayan dukkanin su sun kafa zuri’a da abokan rayuwar su? Da ciwo a ce ka yi wa dan ka zabi, daya ya bada maka kasa a ido, daya ya gudu ya bar ka. Wannan wane irin zamani ne mu iyaye muke gani? Ba haka muka rayu da namu iyayen ba.

Uwar ta Asshe ban santa ba sai bayan da aka daura mana aure, haka Yaya Gidado bai san Hassu ba. Mu a zamanin mu ba ka isa ka yi aure babu sanin iyayen ka da yardar su da sanya albarkar su ba kamar yadda Omar ya yi, na gansu har da yaro mai kama da shi, ita kuma Boddo ga ciki, wato sai lokacin da suka tabbatar ba abin da zan iya a kai sannan za su zo min ko? Dolen-dole in bar su da zabin su? To ya yi, ni ba bakon zafi ba ne, yanzu kuma na daina tsaurara wa a kan komai, kawai bana so a dame ni, lallaba tsufana nake yi, su je su ci gaba da rayuwarsu ni ma in ci gaba da tawa da yaran da ba su fi karfi na ba”.

Wasila jikin ta ya yi mugun sanyi, ta ce, “Abba, zamani ne, wani irin zamani ne Allah ya kawo mu na agwagwa da ‘ya’yanta (ita ke bin su ba su ke bin ta ba)”.

Abba ya ce, “Allah wadaran zamanin kuwa, mu kam mun bi iyayen mu mun gama lafiya, me ake da wannan zamanin?”

Wasila ta ce, “Ka ba su dama ko sau daya ce ka ji abin da ke tafe da su, banza ba ta kai zomo kasuwa, na tabbata zuwa yanzu Boddo ta ga rayuwa, don Nasara ta gaya min abubuwa da yawa, mijin har sace ta ya yi daga wurinsu tsawon shekara guda”.

Abba yadan dubi Wasila, sannan ya gyada kai ya ci gaba da rubutun da yake yi. Bai ce komai ba.

Kwanan mu daya a gidan muna bin kan Abba ya ki sauraron mu. A daren washegari Young Abba da Anti Nasara suka iso, su ma sai a hotel suka sauka washegari da safe suka taho gidan namu.

Ni da Anti Nasara muka rungume juna, sai labarin bayan rabo da muka kwana yi, muka gaya mata halin da muke ciki da Abba a yanzu. Ta tausaya matuka jin har Omar din Abba ya ki saurara. Don haka Young Abba ya hada emergency family meeting a nan gidanmu don shi ma tunda ya zo jiya bai ga Abba ba, ya ce, har Hamzah ya zo gidan a yi meeting din da shi.

Allah kadai ya san halin da Hamza ke ciki, sai ko Ubangijin da ya halicce shi. Ya Omar kam, gab yake da zarewa saboda tashin hankali.

Rana ta farko da Anti Wasila ta ga mijin Boddo, wato Hamzah Mawonmase a falon gidan ta, she was like exactly the black Nigerian Boddo has been dreaming and explaining of. Hakika ganin sa ya fi jin sa. Dole ya dauki hankalin mata masu yawa masu irin fantasy din Boddo na son kyawawan bakaken maza. Kuskuren Boddo, rashin bai wa Allah zabi, idan da ba ta yi kafiya ba ma in Allah ya rubuta Hamzahn mijin ta ne zai zo ya tadda ita har inda ta ke cikin yarda da amincewar mahaifin ta.

Ko kusa ba ta yi tunanin Hamzah a wanda ba musulmi a baya ba ko wani yare da ba hausa ba, domin abin ba kama. Ya fi kama da bakaken fulani a kodayaushe, ko kuma bakaken kasashen Africa ta yamma.

A wajen meeting din ne Hamzah ya baiwa Young Abba hakuri na tafiya da yayi da ni Turkiya babu sanin su. Yace he has no option a lokacin su yi wa Allah su karbi uzurin sa. Young Abba bai yi shiru ba duk da haka, ya gaya wa Hamzah rashin jin dadinsa kan abin da ya yi masa na guduwa da Boddo, “Don kawai na ce ku yi adopting ‘ya’ya? Don ina jiye muku wahalar jinya? To tunda abin naku haka ne zan barku da Abban, zan cire hannu na in bar ku da shi”.

Gabadaya aka taru ana ba shi hakuri. Har Ati Wasila. Hamzah kuma ya karbi laifin sa ya ce, “Wallahi ya yarda a lokacin shi kansa ya samu milddepression a kan son haihuwa da Boddo, bai san hakikanin abin da ya yi ba sai daga baya. Kuma ba nufin sa ba ne ya raba su da Boddo, kawai ba ya son cewa da ake ba za su haihu tare ba.

Ya kare zancensa da cewa, “Ni na karbi kaddarar Ubangiji a ko ya ya yaran suka zo zan iya kula da su shi yasa bana bayan ayi terminating wannan cikin, amma na gaba na yarda in ya nuna hakan wato an gano sickler ne na yarda a yi terminating pregnancy din da wuri, har sai in ya nuna normal ne. Kaddarar mu ce ta zo a haka, kaddarar mu ce, amma nima ba wai ina bayan auren AS-AS bane sai in ya zo da rashin sani irin namu ba yadda za’ayi. Allah ya halatta saki amma ba ya son sa”.

Anti Wasila ta kasa gane inda maganganun da ake ta yi suka dosa, sai da Anti Nasara ta yi mata bayani, cewa Hamzah Mawonmase AS ne itama kuma Siyama AS ce. Wasila was like. “Duk a cikin illolin fushin mahaifi ne Boddo ki ka ga hakan, da kuma kaddarar rayuwar kowanne bawa da bai isa ya tsallake mata ba”.

Meeting din ya fara ne a kan yadda za a yi a shawo kan Abba, ya ba mu lokacinsa ya saurare mu. Ya kuma karbi tuban mu ko yayi mana hukuncin da yake so kowannen mu ya yi alkawarin daukan hukuncin Abba da hannu bibbiyu.

A karshe Young Abba ya ce, babu mai saka Abba ya zauna da mu ya saurare mu yanzu banda Ummati, don haka mu yi shirin wucewa Gembu dukkanin mu gobe, ba da sanin Abban ba, in yaso in muka samu kan Ummati ita sai ta kira shi a yi komai a gaban ta a kare.

Young Abba ya dan yi tagumi sannan ya dan ciza fatar bakin sa ya ce, “Idan har mun yi nasara ya yarda ya saurare mu a gaban Ummati, to dole dukkannin ku ku karbi hukuncin da ya zartar ko da kuwa na rabuwa da juna ne”.

Babu cikin wanda bai duri ruwa ba, har kuwa da Anti Wasila da ta ji Hamzah da Kausar duka sun shiga ran ta farat daya, saboda nutsuwa da kamewar su. Ga albarkar yaro da kuma cikin dake jikin Boddo. Don haka in ka gan mu cikin motar da za ta kai mu Gembu daga Abuja kamar wadanda aka aiko wa da Manzon mutuwa, kowanne ya yi zugum, zuciya na ta sake-sake.

Tafiyar wuni guda sur, kuma sai da muka kwana a wani gidan baki a garin Numan, kafin washegari tunda asubahi muka kama hanyar Gembu.

Lokacin da na fara hango tsaunukan Mambillah da na Mayo Selbe, sai na fara kabbara da kuma addu’a a cikin raina.

“Ubangiji ga ni na dawo mahaifata don gyara kuskurena, don gyara irin addu’ar da na girma ina yi a baya. Ubangiji kada Ka bar ni da dabarar kaina, ka iya min duk abin da Ka san ba zan iya ba. Ubangiji Ka san ina son bawan ka HAMZAH, amma idan rabuwa ta da shi ita ce mafi alkhairi kuma ita ce za ta sa mahaifi na ya yi farin ciki da ni, na roke ka Ka sanya min hakuri da dangana, ka bani wuyan dauka. Ka musanya min da duk abin da ya fi zama alkhairi a gare mu ni da shi baki daya.

Ubangiji yau na saka ‘togaciya’ a addu’a ta ba ni da zabi ba ni da buri sai naka Ya Ubangiji, na roke Ka, Ka sassauta zuciyar mahaifi na a kaina. Ka raba ni da mafarkai da burika marasa amfani.

Ubangiji da ni da miji na bayin Ka ne, masu neman yafiya da gafarar Ka bisa kurakurai da zunuban mu. Mun kasance bayi masu tsoron haduwa da kai a kan su, kada Ka kama mu da ayyukan mu, Ka yi mana rahma Ka ji kan mu ba don halin mu ba.”

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Sakacin Waye? 66Sakacin Waye? 68 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×