DR. MAMMAN GEMBU
Yau tun safe da ya tashi da Siyama ya tashi a ran sa, yayi mafarkin wai ga ta tana ta binsa tana kuka ya ki kula ta, ga Omar tare da ita yana ta cewa, “Abba ka yafewa Boddo na”.
Da wannan ya tashi a ran sa wanda ya sa begen ‘ya’yan nasa guda biyu da kewarsu ta addabe shi. Har Wasila da ke hada masa shayi ta lura ya yi zugum cikin tunani. ‘Yammatan Abba wato Maryam-Jamila da Shukra-Nadiya na ta ba shi labarin primary school graduation din su da aka yi jiya. . .