Skip to content
Part 70 of 73 in the Series Sakacin Waye? by Sumayyah Abdulkadir Takori

“A rayuwar duniya kowa da kaddararsa!”

Wata waka ce ta marigayi Dr. Mamman Shata da Hamzah Mustapha Mawonmase yake matukar so, a duk lokacin da damuwa da tunanin Boddo ya addabe shi ya kan murdo wannan wakar yana bi, yana yarda da dukkan kalaman da ke fita daga bakin fasihin mawakin na kasar Hausa wanda ya ci dogon zango a arewacin Najeriya.

And he is in love with the song, with the dialect, with Hausa people, with Hausa language, culture da traditions na Hausawa, da duk wani abu da ya shafi Hausawa da Fulani tun ma kafin ya san Siyama. Har ta kai ta kawo ya zabi ya karanta linguistics a jami’ar Jos, Hausa kuma ta zamo second major dinsa bayan turanci, duk da cewa, tsakanin kabilar sa ta ainahi wato (BEROM) da Hausawa kiyayya ce mai asali da tushe. Shi ya sa bai yi mamakin hukuncin Kakar Siyama (Ummati) da mahaifinta Abba Dr. Mamman Gembu, suka zartar a kan sa, ko da ma ya tsammaci hakan ya kuma shirya wa hakan. Abin da ya guda kenan tun farko ya yi wauta mara bullewa ta daukar Siyama zuwa inda ba ta da kowa don su ci gaba da rayuwar su tare, amma ta ke ganin ya zalunce ta, Abba na son Siyam, shi ma yana sonta, aka ce so so ne, amma son kai ya fi. Shi ma dan Adam ne kamar kowa mai son kansa da nema wa kan sa farin ciki. Amma ya yarda hakkin iyaye abu ne mai girma da ya isa hana ma’aurata zaman lafiya da kwanciyar hankali duk irin so da kaunar da suke wa juna.

Ga shi dai ya rabu da Siyama a gidan mahaifinta, iyayen ta sun yafe mata, sun karbi ‘yar su, shi sun kore shi, amma abin mamaki ko kadan hakan bai daga hankalin sa ba, saboda ya yi imani da Allah yanzu cewa komai ka bar maSa ka nemi mafita daga gare Shi da gaske ko ba dade ko ba jima zai ba ka mafitar a lokacin da ba ka zata ba. Hasalima ya fi samun kwanciyar hankali yanzu da maida hankali ga ibada da sallah da ba ya tare da Siyama.

Bayan ya baro Mambillah ya yi niyyar zuwa Jos, amma sai ya ga wajen wa zai je? Ba uwa ba uba balle dangi, babu Kaka Veronica, bai ajiye Da ba bai ajiye jika ba. Siyamar da ya mallaka wa duniyar sa ta yanzu, iyayen ta sun kwace a bar su. Me ya kamata ya yi yanzu? Ban da tunanin hanyoyin da zai bi ya gyara rayuwar sa ta yanzu ya martaba kansa ta hanyar kamewa ga barin shegiya giya wadda a ganin sa duk ita ta dagula masa rayuwa. Ya kuma wanke tarin zunuban sa a wurin Ubangiji ta hanyar istighfari da kullum Siyama ke koya masa?

Tunanin da yake kwance yana tashi da shi kenan tun saukar sa a Istanbul. Kwanan sa uku bai fita ko ina ba don dama cikin hutun sati biyun da ya dauka yake. Giya kuwa bai kara waiwayar ta ba, don haushin ta yake ji ba dan kadan ba, musamman in ya tuna irin tijarorin da ta saka ya rika yi wa Siyama. Wata kwayar mutum guda daya da yake da tabbacin duk duniya ba za a samu mai kaunarsa kamarta ba bayan Kaka Veronica. Ba za a samu macen da ta ba shi farin cikin da Siyama ta ba shi ba, ta fidda shi daga duhu zuwa haske, tana kokarin tura shi cikin rahmar Ubangiji yana botsarewa. Wannan kaicon da nadamar da su yake kwana yake tashi, ya yi rantsuwa zai mutu ne rike da igiyoyin auren Siyama ko da iyayenta ba za su bari ta yi masa takaba ba, tunda ba su dauke shi komai ba sai kafuri bayan ya shaida babu sarki sai Allah, Shi kadai Yake, bai da abokin tarayyah, bai haifa ba ba a haife shi ba, kuma Annabi Muhammad (S.A.W) bawanSa ne kuma manzonSa ne.

It hurts him deeply yadda Ummati ta nuna kyamatarsa karara, Abba kuma ya bi bayanta, ya yi zaton za a samu rangwame daga bangaren Ummati, amma ina! Ita ta fi rura Abba, yau da ta sauko ta karbi kaddara da Abba ba shi da ja a kan hukuncin mahaifiyarsa, da yanzu yana nan tare da ‘yarsu Siyama, Siyamarsa su yi fada su yi dadi, wanda fadan ya fi yawa, kuma ba komai fadan nasu ke kara masa ba sai sonta da kaunarta don ya san duk a kan gaskiyarta da soyayyarsa ta gaskiya ta ke yin duk irin boren da ta ke yi masa.

Ina ma zai sake samun damar da ya samu a baya ya yi repenting kurakuran sa ya gyara komai? Gyara kuma na har abada. Ba ya son tuna kalmar bature ta ‘opportunity comes only once in life’.  He wept, and wept, hoping to repent. Amma da kyar Abba da Ummati za su kuma ba shi wannan damar.

Ko ma me zai biyo baya, ko ma me Allah zai yanke he’s willing to accept it in good faith and total submissiveness to Allah. Ya tuna ayar da ya ji Sheikh Mufty ya fada cikin ire-iren wa’azin da Siyam ke kunna masa yana saurare da kunne daya, “Wa man yattaqillah yaj’allahu makhraja. Wa Yayarzuq hu min haithu laa yahtasib. Innalillaha baligu amrihi, qad ja’allallahu likulli shai’in qadra’.

Malamin ya fassara ayar da harshen Turanci a wancan lokacin, da cewa, “Duk wanda ya ji tsoron Ubangiji a al’amuran sa zai ba shi mafita, kuma ya azurta shi ta inda bai zata ba. Duk wanda ya dogara ga Allah, Allah ne ma’ishin sa. Ubangiji mai isa da al’amuransa ne. Hakika Ubangiji ya sanya lokaci ga kowane abu”.

Yana wannan tunanin ya ji ana danna masa kararrawar son shigowa. Ya yi mamakin waye ya zo masa a wannan lokacin karfe takwas na dare. A hakan ya bude kofar sai ya ga makwabcinsa Baturkiye Suhail Nadir.

Suhail ya ba shi hannu suka gaisa, shi kuma ya ba shi hanya ya shigo daga ciki.

Bayan sun gaisa Suhail ya shantake yana zuba masa hira tamkar bai lura da cewa ba ya cikin walwala ba. Kuma ba ya son a dame shi a wannan lokacin da yake ganawa da zuciyar sa cikin kan-kan da kai ga Mahaliccin sa. Cikin hirarrakin Suhail abu daya ya fahimta, wai Sarki Abdul’aziz na kasar Saudi-Arabia na bada scholarship ga wadanda suka nemi PhD a Jami’ar Oum Al-Qura, Suhail ya ce zai gwada sa’ar sa don yana son zaman kasa mai tsarki ko don ya samu damar fadada ilmin addinin sa a fannoni daban-daban da mue da su na addinin musulunci.

A take Hamza ya ji tamkar Nadir ya kawo masa mafita ga rayuwar sa, ya ji ba abin da yake so shi ma irin ya yi kaura zuwa Saudi-Arabia da sunan neman ilmi, ya halarci Jami’ar Ummul-Qura don ya fadada ilmin addinin sa ko iyayen Siyama sa daina masa kallon tubabbe, zai je ya koyi duk abin da ake son musulmi na kwarai ya koya. Makka da Madinah su zama refuge din sa, yin hijira daga inda ya yi maka kunci zuwa inda zaka samu sauki da cigaba sunnah ne.

Ya samu kansa da tambayar Nadir ko a ina ne ake application din? Nadir ya fiddo wayar sa ya nuna masa komai, ya ce, “Online ne”. Hamzah ya ce yana so su nema tare.

Nadir ya ce, “Wani hanzari ba gudu ba Mr. Hamzah a Saudi Arabia ba a shan giya, hasalima ba a shiga da su Maccah da Madinah, anya za ka iya zama? Na ga you ar an addict…”.

Kunya da bakin ciki suka lullube Hamzah, ya kara yarda cewa shan giya ba karamar kazanta ba ce a musulunci tunda har aka haramta shiga da ita garin Maccah da Madinah.

A take suka hau cike application din tare a kwamfutocinsu na kan cinya (laptops). Kasancewar Ummul-Qura na koyarwa da harshen Turanci ne ya zabi zai karanta digiri na uku (PhD in Islamic Jurisprudence). Babu daukan lokaci mai tsaho cikin yarjewar Ubangiji Hamzah da Suhail suka yi sa’ar wucewa Ummul Qura University.

                   *********

Haka rayuwar ta canza wa Hamzah Mawonmase gaba daya a kasa mai tsarki, yanzu ya yarda bai san komai a kan addini ba cikin tsananin jahilci yake rayuwa a baya da sunan ya musulunta shi yasa Siyam ta kasa jurewa zama da shi cikin ilmin ta duk da son da take masa. Bayan dawowar sa jami’ar Ommul-Qura ba da bata lokaci ba ya fara PhD dinsa, da ma kuma kun san Hamzah ba dai brain ba. Shi da Nadir suka zamo aminai na kut da kut, kullum tare suke zuwa masallaci yin duka salloli biyar cikin jam’I, yana kara koyon komai na addinin musulunci daga al’ummahr musulmi da aboki nagari wato Suhail (in theory and practice).

Duk inda suka ji gayyatar wani program, workshop, seminar na karawa juna sani ko lacca ta addini a kan fannoni daban-daban na musulunci a garin Makkah ko a Madina sune kan gaba wajen halarta. Annabi (S.A.W) ya yi gaskiya da ya ce ku yi abota da mutanen kirki, domin abokai su ne manyan instruments ko yardstick na daukan dabi’u a wajen maza, a wasu lokutan har matan ma.

Haka duk inda suka ji za a yi wani gajeren (course on vacations) ko a Da’if ne suna kokarin zuwa, na karshe-karshe da suka je a Riyadh ne, wato babban birnin Saudi-Arabia wanda aka yi na sati uku a kan “Kimiyyar Al-Qur’ani mai tsarki”. Hamzah bai tsaya a nan ba, ya zama cikin daliban Sheikh Salah Bukarti (na online) wanda a can yake koyon karatun Alqur’ani tun daga Nasi zuwa sama da qira’ar Salah Bukarti. Shi addini sa kai ne, ba ra’ayi ke tafiyar da shi ba. Saboda ko kana da ra’ayin sa in ba ka sa kan ka tsamo-tsamo a cikin sa ba hakika ko cikin musulunci ka tashi ba za ka kyautata shi yadda ya kamata ba.

Zuwa wannan lokacin Hamzah har sajen ustazai ya ajiye, a yanzu in kin san shi a VOA a cikakken ba-amurken shi ki ka ganshi a gefen titunan Meccah ko Madinah cikin farar jallabiyyah kal da farar hula ba za ki gane Mawonmase farat daya ba.

A shekarar sa ta biyu a Saudiyyah ne ya fara tuntubar asibitoci a kan aikin diyar sa, har suka daidaita da Saudi-German. Hamzah ya sayar da dukkan gonakinsa na Jos don dai ya samu kudin da za a yi wa Nasara dashen bargo, bai gaya wa kowa ba sai da ya gama dukkan shirye-shiryen sa aka sanya lokacin yin aikin sannan ne ya sanar da Ya Omar don ya gaya wa Abba.

Wannan abun da Hamzah ya yi wa ‘yar sa Nasr ana sayar da dukkan abinda ya mallaka don ya ceto rayuwar ‘yar sa ya girgiza Abba, duk da cewa ‘yar sa ce shi ya haife ta ba wani ba, ya nuna cewa ya yarda ya rasa komai, in dai zai tsira da ita.

Kuma Bahaushe ya ce, “Mai DA wawa ne”.

Wannan al’amari ya zaftare kiyayyar da Abba yake yi wa Hamzah da 50%. Lokacin da za su tafi Abba kasa zama ya yi, ya ce da shi za a je don ba shi da tabbacin ko Nasra za ta tashi, gara ya je a yi komai a kan idon sa, idan ya kama ya zama sallama tsakanin sa da jikar tasa.

Na dauka bayan tafiyar su da Nasra Saudi-German inda za a yi mata Bone-Marrow Transplant ba zan damu ba, tunda harda Abba aka tafi. Gidan ya zama daga ni sai Anti Wasila da Maryam-Jamila da Yatuddeen. Amma ko barci bana iya yi idan na tuno irin sallamata da ita. Ta ce,

“Boddo na, wai da gaske Yatuddeen ya ce bargo da jinni za’a canza mini?”

Ban iya na ba ta amsa ba saboda kukan da ya ci karfina. Ina ji tana cewa.

“Ki daina kuka Boddo na zan sayo miki chocolate in zamu dawo. Bye-bye Boddo na”.

Ba ni kadai ba, kowa da ke wajen a lokacin sai da ya tsane hawaye da hankicin sa, Abba kuwa tashi ya yi ya bar wurin.

Bayan tafiyar su sai da na yi kwanaki uku ban fito ko falo ba, ko abinci bana iya ci, Anti ce ke bi na da tea ko noodle har daki ta takuramin saida naci.

Ranar da za a yi aikin kuwa da Abba ya yo waya ya ce min in yiwa Nassy addu’a za a shiga da ita ‘theatre room’ gasu tare da ita shi da Baban ta, sai da na koma unconscious na lokaci mai tsawo, kuma zazzafan zazzabi ya rufe ni nan take. Na shige bargo na ina rawar dari kawai. Addu’ar ma na kasa.

Hakika yau na sara wa kowacce UWA da ta dandanin rashin dan da ta haifa yana karami ta kuma yi jinyar sa.

Sai washegari Ya Omar ya kira ni, amma tsoro da fargabar abin da zan ji ya hana ni dagawa, sai Anti Wasila ya kira, ya ce, “An yi aikin lafiya, yaran duka suna dakin hutu, ya ce ta kai min wayar ta ta roke ni in amsa kiran sa.

Sai da Anti ta fara gaya min an yi aikin Nassy lafiya lau, duka yaran kuma wato Aryan da Shukra donors din ta sun fito lafiya sannan na samu karfin gwiwar amsa kiran Ya Omar.

Ya Omar ya ce, “Boddo am, ki ce Allahu Akbar sau uku. Wa man yattaqillaha yaj’allahu makhraja wa yarzuquhu min haithu la yahatasib. Innalallah baligu amrihi, qad ja’allalhu likulli shai’in qadra”.

Sai da ya gama karanto ayar sannan ya ce min, “Ga can Abba da surukinsa Hamzah suna sujudushshukr tare a Harami, bayan sun gama kwanan zaunen su tare a bakin ‘theatre room’ din da aka shigar da Nasra.

Ina ji Abba na tambayar Hamzah a ina yake zaune yanzu? Hamzah ya ce, yau shekarar sa uku a nan Saudiyyah a Ummul-Qura ya hada phD din sa a kan FIQH (Jurispridence) har bayan kammalawa jami’ar tayi masa tayin aiki sabida turancin sa. Wallahi wallahi Boddo Abba suma ne kawai bai yi ba don mamaki, ina ji yanace masa,

“Amma kuwa Allah da girma yake!”.

Ko dazu tare suka ci abinci a ‘Mud’am Furouj Faqeeh’.

Ni ma kaina Siyaman da ake baiwa labari, I became mute, wordless, speechless ba Abban kadai ba. Astonishment ya mayar da ni mara magana, Hamzah ya yi abin da ban taba zato ba.

Duk wani kullaci da na yi masa na cewa ya watsar da ni ya manta da ni bai taba nema na ba cikin duka shekaru ukun nan, sai na ji yana melting yana dissolving, yana zaizayewa duka a lokaci guda. Ashe shi yana can kasa mai tsarki yana canza rayuwar sa positively. Ni ina nan kullace da shi a kan ya kin ema na. Allah kai ne abun godiya, tsarki ya tabbata a gare ka, nastagfiruka wa natubu ilaika.

Satin su Abba uku a Saudiyyah kafin su dawo, amma wani babban abun tashin hankali a gare ni shi ne sun dawo ne ba tare da Nasra ba, Aryan shi ne mai zakin bakin gaya min cewa, Baban Nasra na Saudiyyah ya rike ta, ya ce ba za ta dawo Abuja ba, makaranta zai saka ta in ta samu lafiya.

Ban san sanda na cisge kallabi na na jefar ba, na gwaggwafe a kasa zan saka kururuwa na tuna na daina jayayya da kowa da komai in dai a kan al’amarin duniya ne, musamman a kan abin da ba ni da iko a kai, kuma ihu ko kwarmaton da zan yi din ba zai sa in ga ‘ya ta Nasra a gabana ba. Illa al’ummar gidan mu su yi min kallon zatacciya. Ba kuma su za su sa Hamzah ya san ina ihu ya dawo min da little Nasra ba. Maimakon hakan, sai na shiga ambaton innalillahi wa’inna ilaihi raji’un.

(Sune wadanda idan musiba ta same su suke ambaton daga Allah muke, kuma gare shi za mu koma. Wancananka su ne muminai na hakika suna da daraja da gafara daga Ubangijin su).

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Sakacin Waye? 69Sakacin Waye? 71 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×