Skip to content
Part 73 of 73 in the Series Sakacin Waye? by Sumayyah Abdulkadir Takori

Ya dawo daga Masjid inda yayi sallar asubahi bai kuma taho gida ba sai da gari yayi haske. Ya tarar har Nanny din Nasra ta iso. Wato dattijuwar Takarin da ya dauka take kula masa da ita daga safe zuwa yamma. Ta zo karfe 8 ta koma biyar na yamma lokacin ya gama dukkan uzurorin sa na Jami’ah ya dawo gida, sai ya cigaba da kula da Nasra da kan sa har wayewar gari.

Yana daukar daliban Master’s Degree ne yanzu haka a Jamiar ta Ommul Qura a kan albashin Doctorah na kasar Saudiyyah. Jami’ar ta bashi gida guda cikin gidajen malaman ta.

Yana shigowa gidan da gudu Nasra ta taho tana masa oyoyo! Taci ado gwanin sha’awa da ribbons kala-kala a kan ta, dama kuma ba dai gashin yaran Mambillah ba. Tana girma komai na Boddo na kara nuna kan sa a jikin ta amma kalar fatar da dabi’un ta nashi ne. kai har farcen kafar su dana hannu iri daya ne.

“Umm Subay’a” wato (Nanny) din Nasra ta biyo bayan Nasra rike da kwalin Laban din data ki sha, ta biyo ta da shi a hannun ta tana korafi tana gayawa Abban nata cewa Nasra bata son cin abinci sai choculates kadai. Dr. Hamzah na dariya ya suri Nasara akan wuyan sa yana yi mata Doki sukutum, yana cewa mai aikin nasu dattijuwa Umm Subay’a,

“bar min ita da abincin nan naki Yaa Umm Subay’a, kada ta zama lukuta, Haleeb da Laban zasu wadatar da lafiyar jikin ta in ji likitan ta har zuwa ta kara warwarewa”.

Suna cikin hakan suka ji ana danna masu kararrawar son shigowa.

Nasra, ita tayi maza ta nufi kofar ta bude da dan siririn hannun ta.  Tsaye yake rike da ita lokacin da kofar ta bude yana tambaya “wane ne?”And he cannot believe the beautiful Fulani faces that stood before him, na jama’ar garin Mambillah. Iyalin Malam Dalhatu Gembu.Kallo daya Nasra ta yi wa fuskokin ta gane su. Da karfi da karaji tace “Abba, Boddo na!” Ta dane jikin Abba tana ihun murna. Hamzah sai ya kasa motsi, ya daskare a tsaye ya koma kamar mutum mutumi don wani abu ne da ya riga ya fidda rai da shi, kuma abu ne da bai taba zato nan kusa ba. Boddo Siyama a kofar gidan sa.

Sai ya ji wasu hawaye masu dumi da ya kasa fassara dalilin tsatstsafowar su sun tsirgo cikin idanun sa, idanun sa cikin na Boddon, da hannun ta ke cikin na Kakar ta Ummati. Sai na lumshe masa ido a hankali, nima hawayen suka ciko ido na. Hamzan ya matsa ya baiwa Abba hanya, Abba na murmushi ya kama hannun Hamzah a haka muka karasa cikin gidan, da kyar Hamzah ya iya cewa “Abba Jabbama, Ummati marhaban bikum”. Abba da Ummati kasa amsawa suka yi sabida tausayi da nadama da suka zo suka lullube su. Barin Ummati data tuna kalaman da ta rika yi masa amfani da su a haduwar su ta farko a Mambilah, ga wata kasumba irin ta ustazan Makkah da ta shafe rafin fuskar Hamzah ta kusan boye kamannin sa na asali, amma kuma ta kara masa kwarjini da haiba na musamman.

“Umm Subay’a wato mai kula da Nasra ya yi wa magaa nan da nan ta cika gaban su da ababen sha masu sanyi. Can na hango Hamzah da Boddo ana satar kallon juna ta kasan idanu, kowanne na mamakin sauyukan da ya gani a tare da dan uywan sa, lokacin da Abba ya yi sallama ya soma bayani.

“To alhamdulillah ba tare da doguwar Magana ba sai in ce Hamzah gamu mun zo neman afuwar ka bisa sabanin rashin fahimta da ya faru, bayan dukkan tunanin da ya dace mu yi mu da kan mu mun yanke shawarar dawo maka da iyalin ka.

Muna rokon Allah Arrahmanu ya sanya albarka da alkahairi a cikin rayuwar ku. Ya raya mana Nasra rayuwa mai albarka.

A karshe muna rokon ka da ka bar komai ya wuce kamar ba’a yi shi ba, kowannen mu ya dauki darasin da ya dace ya dauka har da kai kuwa. Mun yi Umrah lafiya mu zamu koma gida sai ka san yadda zaka yi Boddo ta samu irin visar ka. In kuma gida zaku dawo, to duk daya, muna maraba da ku koyaushe, domin kasar mu ma na bukatar irin ka a fannin ilmin addini da na boko musamman a jami’o’in mu. Zabi dai yana gare ku.

Ummati ta ce “maigidan, ni bani da bakin bada hakuri domin na gama ban hakuri na ta hanyar data dace, na yi maka tanadi mai girma sai dai in ce Allah ya kawo kazantar daki shekara mai zuwa war haka in zo in yi wa Bddo jego irin wanda ban taba yi mata ba irin na ‘yan gata.

Yanzun dai na mata wankan nono da wankan turare, na daka mata tukudi da hakin maye da hannu na, na bata madarar rakumi data shanu ta sha ta koshi wadanda aka tatso daga jikin dabbobi da zafin su, don haka na maka gyara na asalin Fulani ‘yan gata wanda bata samu a baya ba, yanzu ne zaka banbance aya da tsakuwa tsakanin diyar Mambillah da ta kasar turawa wacce ka aura. Sai in ce ga Allah ga Boddo na a hannun Hamzah!”

Hamzah bai san sanda ya fashe da dariya ba duk da ba duka hausar ta ya fahimta ba, ya dai fahimci tana nufin ta gyara masa Boddo, Abba kunya kamar yayi yaya da wannan katobara ta Ummati, ita kam ko a jikin ta ta ce da Hamzah “miko min ‘yar talalabuwar ‘yar taku in saka mata warwaron azurfa dana sa a ka yi mata maganin tsari da mugun baki, wannan kyan nata har tsoro yake bani wane Boddo tana karama.”

Aka yi-aka yi Nasra ta je gun Ummati ta saka mata abin hannun amma ta ki, ta makale jikin Boddon ta tana shagwabar data dade bata yi ba, sai Hamzahne ya karba ya saka mata. Hamzah ya rako su Abba zuwa taxi din da ta kawo su ya shigo da jakar kaya na da shopping din da Abba ya yo wa Nasra, babu abinda Abba bai sayo mata ba kama daga sutturah dana bukatar yara daga shagon ‘Majma’al Qimmah’ dake Madinah.

Muka yi musu rakiya dukkan mu muka bude musu kofar motar suka shiga, a lokacin ne na rike hannun Abba tamau cikin hawaye. Abba ya dora hannun sa a saman kaina yace “Allah yayi miki albarka Boddo, Allah ya jikan mahaifiyar ki da bakisan dadin ta ba kamar yadda nasan na Ummati. Ina arokon Allah ya raya ki tare da diyar ki, ku zamo abokan shawarar juna. Allah ya mallaka miki soyayyar mijin ki ya huwwace masa tausayin ki, ya tallafi maraicin ki.”

Wannan ita ce sallamata da Abba na, Dr. mamman Gembu.

Bayan wucewar su muka koma cikin gidan, Nasra nata zuba min labari na irin wuraren wasa da Abban ta ya ke kai ta. Hamzah ya rugume hannayen sa a kirji yayi tsayuwar san nan ta Hamzah Mawonmase a kan mu yana kallon mu with great admiration, Nasra na ta tsalle-tsalle a cinyoyi na.

Jin idanun sa da nayi all over me shiya sa ni dagowa. Sai idanuna suka fada a cikin nasa.

Da farko I couldn’t believe girman abunda na hango a cikin su, gani na yi Hamzah na rikidewa yana koma min yaro saurayi danye shataf in his thirtieth, saboda soyayyar da ke makare cikin kwayan idanun sa. Sai na ji kwallar farin ciki ta hau disa a kundukuki na.

“Nasra je ki amso min haleeb a wurin Umm Subay’a.”

Da gudu tasauko daga jiki na ta yi waje, sai ya kira Umm Subay’a ta wayar hannun sa yana cewa ta kula da Nasra har sai mun neme ta.

Cikin muryar da ke rawa da wani sabon feelings akan mijina nawa na yi karfin halin cewa.

“Yarinyar da ba lafiya ce ta ishe ta ba zaka korar mun?”

Hamzah ya zauna a masangalin kujerar dana ke zaune ya dora hannayen shi a saman kafadu na, hatta kamshin turaren sa ya canza yanzu kasancewar ya koma na non-alcoholic perfumes din larabawa (Oud Abyad), dora hannun sa da yayi a kafadu na ya sa ni jin wani irin yarrrr! Tun daga yatsar kafata har zuwa cikin kwakwalwa ta. Na ji tasowar wannan tsohon ajiyayyen feelings din nawa a kan shi, ya kuma tuna min ashe dai har yanzu da sauran halittar matantaka a jiki na kuruciya ta bata bar ni gabadaya ba kamar yadda na yi tsammani tun komawa ta gaban iyaye na.

Tashin da tsigar jiki na yayi yana tuna min ne cewa shekaru uku kwarara ba kwana uku ba muka yi ba tare da wannan kusancin da junan mu ba. Ba kuma tare da wannan ni’imar ta aure a rayuwar ba.

“Shin akwai wani mara lafiya a duniya iri na Siyama? Kin san watanni nawa shekaru nawa na dauka bana barci saboda kewar ki? Kin san cewa zuwan jiran wannan ranar da nayi tamkar jiran zuwan eternity moment ne? Kin san yaya na yi na kawo yau babu Siyama?”

Hawaye suka shiga gangaro min na ce “amma Shaheed shi ne ko kira, ko text, sai dai in ji ka kana magana da mutane amma banda ni, me na yi maka Habeeby? Ka san yadda hakan ya cutar da ni ya azabtar da zuciya ta?”

Hamzah ya rike hannu na cikin nasa ya ce “Siyam, ki yarda duk a cikin biyayyar dana ke son yi wa Abba ne, ya dauki hannun nawa ya dora a kan kirjin sa daidai saitin zuciyar sa yace “kin ga inda kike zaune kane-kane a duka wadannan shekarun, baki taba gusawa ba ko na minti guda, and now……..”. Ya russuno da kan sa daidai wuya na ya sumbaci masangalin wuya na ya ce “give me my Siyam and bury the hatchet” (bani Siyama ta tunda Abba da kan sa ya kawo min cikin yarda da amincewar sa da albarkar sa, a manta da abinda ya riga ya wuce.”

Ya runguma ni tsam-tsam a jikin sa, ilahirin jikinsa na kaduwa (shaking). Da kyar Hamzah ya iya cewa “na yi kewar mata ta rabin rai na, SIYAMAH!”

Siyam dai baki ya mutu, domin yau ta ji ta ga ta ga Hamzan ta, ta ji ta rungume a hannun da ta fi so a kan na kowa, yana sarrafa ta yadda duk yake so take kuma so, sai tazbihi ga Ubangijin da ya sanya soyayya tsakani na da Hamzah, saboda irin tsotson kaunar da Hamzah ke yi wa bakin nawa cikin wani salo na “sumba” tamkar ta fitar rai ban iya furta ko tari ba.

Can na gano su sun dauki hanyar masterbedroom din su, Siyam goye a bayan Hamzah, goyo sosai kamar ya goya Nasra, yana addu’a da fatan ya zamo mata namiji “dan goyo” kuma “mijin marainiya” kamar yadda Abba ya roki Ubangiji cikin dukkan dawafin sa daga nan har karshen rayuwar su.

Bayan Watanni Biyar

Zaune Hamzah da Siyam suke gaban teburin likita cikin jiran tsammmani, bayan an yi wa Siyam gwajin ciki na amniocenteses. Likitan ya shigo fukar sa ba yabo ba fallasa ya zauna yana fuskantar su, kafin ya saki dariya ganin yadda suka kafa masa ido yace, “Congratulations Mr&Mrs. Hamzah”. Sannan ya aje takardar da ke dauke da sakamakon gwajin a gaban Hamzah.

“Yaron da ke cikin matar ka yanzu normal ne, kamar yadda test ya nuna.”

Daga Hamzah har Siyam kasa magana suka yi saboda abu ne da suka riga suka fidda rai da faruwar sa, kuma basu taba zato ba, sun zo ne don a yi gwajin in an ga cewa sickler ne ko carrier a yi terminating din sa tun bai girma ba don hujjoji kwarara na wasu malamai sun yarda da hakan. Sai gashi likita na yi musu wannan albishir din cewa yaron su mai zuwa na gaba lafiyayye ne basa bukatar su yi terminating third pregnancy din su. 

“Allah kai ne abun godiya sarki Jalla wa azza. Sarkin da babu kamar sa”. In ji Hamzah.

Shekaru Goma Sha Biyar A Gaba

Boddon Hamzah wadda yaran ta biyar ke kira “Mamah”, in ka dauke Nusra da har gobe “Boddo na” take cewa, ta fito daga cikin taron dangin ta na Gashaka dana Mambillah inda suke get together nasu na iyaye, har da Aunties din ta masu girma wato Anti Nasara da Anti Wasila data hannun daman ta Kausar din Ya Omar ta nufi dakin Nusra inda ake wa amarya Nusra kwalliya, ta soma fada “anya Shukra ba zaku bar kwalliyar nan haka ba gashi har motar angwaye ta iso? Kin san Aryan baya son jira sam.” Aunty Shukra Nadiya dake yi wa Nusra kwalliyar amarci ta ce “Ya Boddo, kina ji da Aryan kowa ya sani, amma bar shi ya jira kin ji, in gama gyara ‘ya ta yadda nake so”. Dariya ta yi tana hango yadda tata ranar irin wannan ta kasance, da ba’a samu yi mata irin wannan kwalliyar ba, kasancewar hawaye ya bata armashin tata ranar. Don haka Nadiya ta fita gaskiya, Aryan yayi ta jira har a gama cancada masa amarya.

Ai kuwa sai gashi ya shigo gidan da kan sa, ya sha ado cikin farar excelcior matashin saurayi mai jini a jika da wadatar ilmin addini dana boko, yayi sallama ba tare da ya jira an amsa ba ya tsallake kannen sa dake zazzaune da Aunties din su Maryam-Jamila da Shukra-Nadiya, ya kamo hannun Nusrah wadda a lokacin an kammala mata kwalliyar ‘in blue wedding attire’, a gaban kowa Aryan ya hau tasbihi yana fadin “Yaa Subhanallah! Nusrah am, looking ravishing!”. Daga haka ya janye amaryar sa zuwa mota yana bada hakuri ga su Aunty Nadiya yana fadin “na kasa jira, bani da hakurin jira kun sani, sai kun taho.”

Maimakon ya wuce wajen dinner kamar yadda aka tsara gidan su da Ya Omar ya gina musu a Guzape ya wuce da amaryar sa. Yace ya gaji da bukukuwan, a biyo su da dinner din gidan su. Shekarar sa goma sha takwas yana jira amma ya kasa jiran awa biyu.”

Sai mu ce “ARYAN & NUSRAH” Allah ya kawo kazantar daki. Amen.

Tammat bi-hamdullah.

Karshen littafin SAKACIN WAYE kenan.

Kuskuren dake ciki ku taya ni rokon Allah ya yafe mini. Alkhairi da fadakarwar da ke ciki Allah ya raba mana ladan sa ni da ku baki daya.

Sumayyah Abdulkadir

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 4.5 / 5. Rating: 2

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Sakacin Waye? 72

1 thought on “Sakacin Waye? 73”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×