Skip to content
Part 1 of 2 in the Series Sakacina Ko Halin Maza? by Jamila Lawal Zango Jamcy

Sanin cewar a kwai banbanci a cikin duniyar da Allah subuhanahu wata ala ya halitta masu ɗauke da halittu mabanbanta jinsi,bayan ya halicci duniyar mutane, da kuma waɗanda ba’a ji ko gani gare su sai dai duk wanda ya yi imani,ya na da yaƙinin samuwarsu a cikin duniyar da muke cikinta,da sauran halittu na dabbobi.

Allah gwani wanda ba shi da abokin tarayya a cikin gwanintar halintunsa,ya halicci mutane ya kuma nuna babu wani banbanci a tsaƙanin su,sai wanda ya fi wani tsoron kiyaye abin da ya sharaɗa game da bautarsa, tabbas wannan haka ya ke a gurin Allah,amma kuma yayin da jinsi na bil’adama suka ɗauki sabanin haka, sun ɗora mizanin hankalin su suna auna banbanci na jinsi ta hanyar duba ga mulki, kuɗi ko kyawu na halitta.

Su na kallon waɗanda suka mallaki waɗannan ababen na more rayuwa ga mafi ƙololuwar more rayuwa, wanda duniya ta yi maraba da zuwan sa kuma su ke kurɓan ruwan mafi ƙololuwar ɗaɗi a cikin ta. Haka ta kasance ga wannan matashi mai cike da kyawu da kuɗi da kuma baiwar ilmi da Allah ya azurta shi dashi, ya na ji da kansa da kuma kalar rayuwar da ya tsinci kansa a cikin ta, bai san a kwai wani ƙunci ko wani ƙalubale da Allah ya ke jarabtar bayin sa, waɗanda suka yi imani domin ya gwada ƙarfin imanin su da shi. Tabbas duniya ta na gara masa ƙwallo yadda ya ke so, domin ya fito daga cikin farin jadawali na tsarin rayuwarsa don ya yi gam da katar da bai fito daga cikin baƙin jadawali ba! Waɗanda da duniya ta ke musu kamun kazar kuku, su shiga halin ƙaƙa na iya tare da tunanin makomar rayuwar su. Sanye ya ke cikin shadda ruwan bula gizina, sai ɗaukar ido da sheƙi take ga wani daddaɗan ƙamshi da ke tashi a jikin sa wanda ya ke sanyaya zuciyar duk wanda ya shaƙi ƙamshin.

Tuƙi ya ke cikin gwanance wa da kuma yanga, dan yadda yake jan motar ya ke kamar mai jin bacci ya na lumshe idanunsa masu kama da mai jin bacci. Gefen sa amininsa wato Ak ya ke zaune a kujerar mai zaman banza da wayarsa riƙe a hannunsa ya na dannawa. Jefi-jefi su na taɓa hira duk da hirar ta su, ba ta wuce na ‘yan daƙiƙa yayin da shuru yafi yawa a tsakanin su, kasancewar ta kowannen su ya na ji da kansa, dan sun haɗu ta ko ina ga kyau kuɗi da kuma wayewa da tsantsar ilmi. Wani irin ƙara motar ta yi ya ja birki ya tsaya cikin tashin hankali ganin wani tsoho ya shige masa gaba har ya buge shi da motar.

Ya tsaya ya na kallon gurin da takaici, ganin yadda tsohon ya ke son ɓata mishi lokaci. Da sauri ya kuma buɗe murfin ƙofar zai fita ya na faɗin, “Wannan wawan mutumin zai ɓata min lokaci, an gaya mishi bani da aikin yi ne?” Ya fice ba tare da ya kula Ak da yake mishi magana ba, da sauri Ak shima ya fito sanin halin shi sai dai kafin ya ƙara sa am ya wanka ma wannan tsohon mari har guda biyu. “Ba ka da hankali ne da wannan banzan ƙarfen na ka zaka ɓata min lokaci? Shashasha kawai!” ‘Dan tsohon ya yi taga-taga ya faɗi har ya na fasa baki, da sauri Ak ya kama hannunsa ya mike sai kawai ya fashe da kuka, don shi kaɗai yasan halin da yake ciki. “Haba Am ya zaka mari wanda ya haifeka rashin mutincin na ka ya kai haka? Dubi halin da yake ciki amma baka tausaya mishi ba.”

Harara ya watsa mishi kamar ba zai ce komai ba,har ya fara taku zuwa motar shi sai kuma ya buɗe baki ya ce, “Kai baka ganin abin da ya yi min?Jiya na fara hawa motar nan amma ya ƙuje min mota. Nasan kaf zuriyarsa babu wanda zai iya siyan ko da tayar motar ce.”

A.k ya yi shuru ya na kallonsa cikin takaicin halin sa na rashin daraja talaka da nuna tsantsar tsana da hantara, amma shi a ganin sa ya kama ta ya dinga kawaici saboda yasan waye Ak kuma waye asalinsa. “Da izinin Allah sai ka sami dai-dai da kai.” Ya faɗa ya na jin tsoro kasancewarsa yasan waye shi, ɗa ne ga Alhaji Muhammad Turaki, waye bai san wannan family masu ji da kuɗi da ilmi da wayewa ba.

Cikin sa’a sai A.m bai ji abin da ya faɗi ba don ya juya ya nufi motarsa ya na tsaki. A.k ya zaro kuɗi masu yawa ya miƙa mishi ya na ce wa.” Gashi Baba ka yi haƙuri don Allah ka je asibiti a duba ka.” Ya faɗa ganin duk ya ƙuje a hannunsa. Da sauri ya karɓe ya na godiya, ganin kuɗ’in da ya ba shi dan shi gaba ta kai shi, dama ya fito zai je ya saida kekensa gashi kuma ya sami wannan kuɗi. ‘Dan tsohon ya dinga saka mishi albarka ya na hawaye kamar zai yi mishi sujjada, juyawa ya yi ya nufin motar da A.m yake ƙoƙarin tayar wa,sai kuma ya tsaya ya na kallon titin da alamun abin hawa yake nema a ransa ya na jin kawai ya haƙura da abokantakansu don ya sama ma zuciyar sa salama, da irin cin kashin da A.m yake yi wa talaka a gaban sa.

A.m ya kashe motar ya fito ya na mishi maganar ya shigo, amma ko kallon inda yake bai yi ba sai ma juyar da kansa da ya yi,ya na kallon titi fuskar sa kamar an aiko mishi da mala’ikan mutuwa. “Well.” Ya ce tare da ɗaga kafaɗunsa ya juya ya na faɗin, “Shike nan tun da baza ka taho muje ba ni na tafi, sai mun haɗu a ofis ka taho min da fayal ɗin da mukai maganar da kai, sannan ka shirya gobe ne tafiyar mu.”

Ya ta da motar ya bar gurin A.k na kallon motarsa har ta ɓace wa ganinsa, ya ja numfashi mai zafi ya fesar ya riƙe habbar shi ya na jiran ɗan acaba, sai kuma ya fasa hawa mashin ya fara taku ahankali ya na jiran adaidaita. Tafiya kaɗan ya yi ransa a jagule ya na jin zafin yadda yake nuna tsanar talaka karara baya kawaici a gabansa, yasan cewar bazai taɓa iya canza aminin nasa ba don tsanar talaka a jinisa yake kasancewar duk family d’insu basa son talaka ya rabe su,shi kansa don Allah ya bashi tarin baiwar ilmin kasancewar Allah ya yi mishi baiwa da samin na’ura mai ƙwaƙwalwa,kuma saida suka mai da shi wani don yanzu ya na jin kansa a cikin jerin masu hannu da shuni.

Murmushi ya so ya suɓuce mishi sai kuma ya dake, ya kauda kansa tamkar bai ga motar A.m da ta yi ribas ta dawo ba,da ma yasan dole ya dawo kamar yadda suka saba duk sanda suka yi faɗa a tsakaninsu, wanda ba ya wuce sati don A.m bashi da haƙuri ko kaɗan gidan su da gurin aiki duk sun san haka, shi kuma A.k ba ya ɗaukar raini mafi yawancin lokuta mutane su na mamakin yadda abokantakarsu ta yi ƙarko a haka don kullum cikin faɗa suke kamar wasu yara Daddy shi ne ɗan sasanci, sam baya gajiya kasancewar ya na ji da shi saboda irin ci gaba da ya ke kawo mishi a cikin kampanin sa, ya sani cewar in har babu A.k to kampaninsa bazai ci ga ba.

A.k ya kauda kansa bai tanka mishi ba sai wayar sa da ya ciro da nufin ya kira direban sa ya zo ya ɗauke shi, don ya fasa shiga cikin a daidaita.”Ganin ya taho kamar zai buge shi da motar amma bai kula ba, sai ɗauke kansa da ya na kallon gefe don cike yake dashi. A.m ya leƙo ta tagar motar sa ya ce ya na murmushi mugunta,don daga ganin yadda ya yi ya san ya gaji matuƙa.”Don Allah ka zo mu tafi kasan dole na dawo, Daddy ya kira ni ya na son ganinmu.”

Banza ya yi da shi ya ci gaba da tafiya, ganin haka ya fito tare da kashe motar sai kawai ya kama shi da kokuwa zai tura shi cikin motar, kamar dai yadda suka saba duk lokacin da suka yi fad’a. Bai wani ja ba ya shige cikin motar ransa a haɗe, dariya sosai A.m yake mishi don ya na matuƙar son aminin nasa saboda riƙo da gaskiya, kuma bashi da shishshigi a lamuran sa. Tun da suka shiga cikin motar babu wanda ya yi ko tari a cikin su,da ma ɗabi’ar su ce shirin basu cika magana ba kasancewar kowa naji da kansa.

Wayar A.k ta yi ƙara alamun ana kira amma sai A.m ya kai hannunsa ya kashe wayar baki ɗaya,don yasan mai kiran taɓe bakinsa ya yi ya ci gaba da tuƙi cikin kwanciyar hankali.A k ya ja fasali tare da buɗe baki da nufin ya yi magana,amma da ya kula rigima yake ji sai kawai ya kauda kanshi bai ce ƙala ba don har yanzu ransa a ɓace yake da abin da A.m ya yi ma mutumim da ya haife shi. Ko da suka ƙaraso tangamemem get ɗin gidan mai gadi ya buɗe musu, A.m ya yi parking bai kula da gaisuwar da maigadin yake mishi ba ya shige cikin gidan,yayin da A.k yabi bayan sa kasancewar ba’a yi mishi shamaki da cikin gidan ba.

*****

Juwairiya zaune a gefen ƙanin ta Ibrahim ta zuba mishi idanu, ya yin da hawaye suke gasar turarreniya a fuskarta, ji ta ke kamar ta yi hauka tsabar damuwa ta na jin wani irin baƙin cikin halin da suka tsinci kansu. Zura hannunta ta yi a cikin kofin ruwa ta shafi fuskar Ibrahim da yake kwance rai kwakwai mutu kwakwai, sai kuma ta kama shi ganin yadda ya zaburat amkar zai shiɗe.

Mama da ke tsaye a bakin ƙofa fuskarta ɗauke da tsananin damuwa da ƙunci ta janye tagumin da ta yi tare da ajiyan zuciya mai ƙarfi. “Anty Juwairiya mutuwa zan yi ga shi Baba ya ƙi dawowa.” Ya faɗa da wata irin murya da yake ƙoƙarin haɗa kalmomin da su.”Baza ka mutu ba Ibrahim ciwo ba ya kisa.”Mama ta ce cikin tausayin sa. Juwairiya kuwa ta kasa magana sai kuka ganin gudan jinin na ta ƙanin ta tilo na cikin wani mawuyacin hali, ji take da ma ace ciwon a jikinta yake. Sun jima suna tsaye a kansa da numfashin sa yake baraxanar ɗauke wa, hankalin su a tashe sai shafa masa ruwa suke yi suna kuka gunun ban tausayi. Juwairiya ce ta miƙe ta na faɗin, “Mama bai kamata mu zuba mishi ido mu na kallon sa a cikin wannan halin ba, tunna Baba bai dawo ba zan fita na samo abin da za’a kaishi asibiti.”

Ta ce cikin kuka.

Mama ta kasa ce mata komai duk da ta na tunanin in da za ta samo kuɗin, amma har ta na shirin fita ba ce komai ba. “Juwairiya na shiga uku!Ya sume.” Ta ji muryar Mama cikin ƙaraji dai-dai lokacin da ta fice da ga gidan.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 4.5 / 5. Rating: 2

As you found it interesting...

Follow us to see more!

Sakacina Ko Halin Maza? 2 >>

2 thoughts on “Sakacina Ko Halin Maza? 1”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×