Fitilar aci bal-bal ke ci a dakin, haskenta ya haska mata Ma'aruf Ji-Kas wanda ya dago ido daga kan agogon (Rolex) da ke daure a fatar hannun hagunsa ya dube ta cikin hasken a ci bal-bal din, sai ta ga kamar idanun sun tara hawaye ne. Amma da ta kalle shi sosai ta gane ba hawaye ba ne, halitta ce. Dogo, mara kauri, yana zaune bisa kujera kafafunsa a mike. Shaddar jikinsa sai maiko ta ke da alamun ba ta (squeezing) sam-sam. Tafin kafarsa fari sol kamar ba ya taka kasa. Ta tuno yadda kullum. . .