Skip to content
Part 13 of 50 in the Series Sanadin Kenan by Sumayyah Abdulkadir Takori

Fitilar aci bal-bal ke ci a dakin, haskenta ya haska mata Ma’aruf Ji-Kas wanda ya dago ido daga kan agogon (Rolex) da ke daure a fatar hannun hagunsa ya dube ta cikin hasken a ci bal-bal din, sai ta ga kamar idanun sun tara hawaye ne. Amma da ta kalle shi sosai ta gane ba hawaye ba ne, halitta ce. Dogo, mara kauri, yana zaune bisa kujera kafafunsa a mike. Shaddar jikinsa sai maiko ta ke da alamun ba ta (squeezing) sam-sam. Tafin kafarsa fari sol kamar ba ya taka kasa. Ta tuno yadda kullum ta ke fama da goge kaushin tata kafar da dutsen kaushi. Kai Allah mai kyauta da kari, wannan sardidin miji Allah ya dauko ya ba ta har gida. Labban bakinsa jazur da su kamar yankan reza, fuskarshi (intact) cikakkiya, komai ya zauna daf a muhallinsa, wato ido, hanci, gira kowanne daidai yake a inda Allah ya halicce shi. Ba fari ba ne can, sannan ba za a kira shi baki ba. Kamar tsafta ce ta bayyanar da haskensa, amma ba shi da hasken fata sosai. Ga wani saje ya kwanta tun daga gefen fuskarsa sai sheki yake, da gani yana samun (extra) kulawa.

Ta ga in ta tsaya kallon mijin nata zai dauke ta sakarai, dole ta kama kanta, ta zauna a kujerar da ke fuskantarsa, ashe kushin din kujerar a rarake yake sabida tsufan kujerun tana zama ta burma ciki.

Tana kokarin fitowa ya ce, “Sorry”. Da murya mai nuna kulawa.

Ita dai kunyar duniya ta hana ta magana duk da ba ta ga alamun ya yi mata dariya ba. Ta bar kujerar ta koma wata duk suka yi shiru. Ya gaji da shirun ga dare yana yi, kuma cikin Jigawa za su kwana a hotel.

Ya ce, “Ba ki iya gaisuwa ba?”

A dan daburce ta dago domin ba ta zaci zai yi maganar ba kamar daga sama ta ji ta.

“Iyee, na’am?”

Ya maimaita, “Ba ki iya gaida na gaba da ke ba?”

Da sauri ta ce, “Ka yi hakuri, ina wuni?”

Ya basar, “Ya ya sunanki?”

“Laila!”

Ta amsa.

Ko ba komai sunan ya dace da ita, kyakkyawa ce da kuma alamun mai son ado ce, uwarta bafullatana ce don haka fara ce tas!

“Ni sunana Ma’aruf”. Ya fadi a gajarce.

“Na sani”. Ta ba shi amsa.

“Ya akai ki ka sani?”

Ta dube shi da kyawawan idanunta kamar ta ce waye bai sanka ba a garin nan? Sai kuma ta kama kanta, ta ce,

“Baba ne ya fada.”

Ya gyada kai. Cikin sakakkiyar murya ya soma magana sosai duk da ba ta fi layi biyu ba a ganinsa ya yi cikakken bayanin da ya dace.

“To ni Laila na zo ne don mu ga juna, mu kuma fahimci juna kamar yadda iyayenmu suka yi umarni. Na ganki na karbe ki a matsayin matar aure na ta biyu. Na taba yin aure har ina da ‘ya. Wannan shi ne”

Jimlar nan ‘kamar yadda iyayenmu suka yi umarni’ bai yi mata dadi ba. Wato ba soyayya ta kawo shi ba, umarnin iyaye ne. Wata zuciyar ta ce, ‘Ban da abinki Laila yaushe ya ganki har da zai yi zancen soyayya? Tunda ya riga ya zo a hankali za ki sa ya so ki, ki mallake shi, ki mantar da shi tunanin kowace ‘ya mace, har matacciyar da aka ce yana masifar so’. Wannan tunanin ya sa ta yin murmushi, har ya zaci shi ta yi wa murmushin.

“Sunana Laila, ta biyar wajen Baba, ta farko wajen Innarmu. Ina karatu a jami’ar Dutse ina karantar economics, yanzu ajina biyu. Na amince ni ma, Allah ya tabbatar mana da alkhairi.”

Ya gyara zama kamar ya gaji da zaman yana son mikewa ko jijiyoyin bayansa sa warware daga zaman jiran da ta sa shi. Bai yi shiru ba ya ce, “Me ya sa ki ka bar ni na yi ta jiranki? Ko kin san jira na daya daga cikin abubuwan da na tsana a rayuwa ta?”

Da hanzari ta ce, “Ka yi hakuri.”

Ya ce, “Na yi. To ga shi kina karatu a Jigawa, ni kuma Bauchi zan ajiye ki. A can gidana yake, kuma can na fi zama, ko ya ya za a yi?”

Laila ta kasa jan ajin a wannan lokacin cewa ta yi, “In za ka bar ni in yi business zan ajiye karatun.”

Ya dan dube ta na sakanni, “Business kuma? Karatun naki fa?”

Ta girgiza kai, “Barinshi zan yi. Na fi so in yi kasuwanci”.

Cikin mamaki ya ce, “Bauchi ba a karatu?”

“Ana yi, ban so ne kawai.”

Bai ja da yawa ba, ya zunkuda kafada irin ko ohon nan

“Za ki saida duk abin da ki ke son saidawa, in dai a gida ne. Ni zan tafi, Allah ya ba mu alkhairi. Sai gani na biyu.”

Kamar kada ta barshi ya tafi, ji ta yi in za su kwana suna hira ba za ta gaji ba. Mikewar nan da ya yi zai tafi kamar an soki zuciyarta. Babu yadda za ta yi tana ji tana gani ya bace a falon, ya bar mata sassanyan kamshinsa.

Da kyar ta ja jiki zuwa cikin gida, tambayar duniya Innarta ta yi ta fada mata abin da suka tattauna, ta kasa gaya mata komai. Laila ta ce a zuciyarta, wannan ita ce soyayya? Duk da ba wanda zai ba ta amsa ta yarda ta amince ita ce. Ta kuma yi mata mummunan kamu.

A bangaren Maaruf babu wani sauyi a zuciyarsa daga yadda ya zo, ya kuma tafi.  Suka yi sallama da Hajiya da Liman, motocinsu suka tashi. A cikin Jigawa suka kwana a hotel, da asuba suka kama hanyar Abuja.

Karfe goma na safe itama Hajiya direbanta ya dauko ta, sai Bauchi.

Amina na nan jiya-i-yau, sai ma baki da ya karkace. Ta samu Doctor da nosis suna yi mata gashin bakin. Hajiya ta daga hannunta sama, ta ce, “Ya Allah! Ka dubi wannan kankanuwar baiwa taKa, Ka ba ta lafiya. Lafiyarta kwanciyar hankalinmu ce da al’umma masu yawa, domin ubanta warkewarta kadai ce za ta sanya mishi nutsuwa ya ci gaba da ayyukan alherinsa ga al’umma.”

Bai kara tunawa da Laila ba yana Bauchi ya tare wajen Amina, in ka ga ya fita sallah ce da wanka da canza kaya ya fitar da shi. Don bacci kan kujera rike da hannun Amina ya riga ya saba da shi. Hajiya na gefe kan sallayarta tana lazimi tana tausaya musu su duka. Tana ganin in ya yi auren nan maraicin zai ragun musu, za su samu wadda za ta rungume su su duka biyun, ta rage musu maraicin da suke ciki. Don haka ta yi wa Liman magana a tsaida daurin auren cikin sati mai kamawa, ta kuma umarci Ma’aruf ya kara zuwa wajen Laila su kara fahimtar juna.

Sai a lokacin ya tuna da ita. Bai yi musu ba, ya tsakuri lokaci cikin muhimman lokutansa ya je ya kara ganin Laila.

Sai dai hirar ba ta yi armashi kamar wancan zuwan ba. A dalilin wasu tsare-tsare na shagulgulan biki da Laila ta lissafo masa har guda bakwai. Shi mamaki ma abin ya ba shi, tana kauye kamar Ji-Kas don ta je birni karatu shi ne ta samo wannan budadden idon haka? To ina ga ta shiga manyan birane irin Bauchi da Abuja? Shi ba abun ya ce zai janye ba, Hajiya ba za ta yarda ba. Sai ya ga bari ya ba ta duk abin da ta ke so don a zauna lafiya, amma da sharadin babu keyarsa cikin shagulgulan nata.

Laila ba ta so haka ba, amma da ya tura mata leda cike da kudaden da ta bukata sai ta amince. Suka yi sallama ya tafi zuciyarsa cike fal da tunane-tunane masu sosa zuciya. A hankali ya tambayi kansa,

“Yaushe zan samu matar da za ta so ni don Allah ba don wadannan takardun ba? Yaushe zan samu matar da zan so kamar A’isha? Yaushe zan kara jin soyayyar wata diya mace a zuciya ta bayan Aisha? Yaushe? Yaushe?? Yaushe???”

*****

An daura auren Ma’aruf da Lailah ranar lahadi, uku ga watan Fabrairu. Laila ta yi duk shagulgulanta a Dutse da kawayenta na jami’a, wunin biki kawai aka yi a Ji-kas.

Ya bada motoci don dauko amarya kamar yadda Hajiya ta umarce shi. Nan gidansa na Bauchi aka sauke su. Ya rufe bangaren Aisha domin a can duk wasu memories na rayuwar farin cikinsa ke ajiye. Sashen baki ya bai wa Laila, shi kuma da ma yana da nasa bangaren.

Dangin Laila sun yi dukkan kauyancinsu sun gama, an kwashe su an mayar Jikas, ya zama sai ita kadai cikin wannan katafaren gida. An tabbatar mata ba aikin da za ta yi, akwai ma’aikata, girki wannan sai ta ga dama, ba abin da ya fi wannan dadi ga Laila, domin da ma ita makiwaciya ce. Inda duk kuma aka samu makiwaciyar mace za a samu kazanta. To Allah ya fishshe ta.

Da daddare tana ta shirye-shiryen tarbar ango shiru ba ta ganshi ba. Ta yi kwalliya kamar-kamar-me, ta sha turaruka ba irin nata na gida ba, wadannan na cikin kayan lefenta ne da Hajiya ta sa aka hada mata. Tun tana zuwa gaban madubi tana kara gyara kwalliyar, har gyangyadi ya soma dibanta.

A lokacin ta ji alamun shigowar mutum dakin ta hanyar sauyawar kamshin da ta ke shaka a hancinta, da wani nau’in kamshin na daban da jefi-jefi ta kanji har ta gane na mutum daya ne, wato mijinta Engnr. Ma’aruf Habibu Ji-kas. Ta ware ido tana dubansa da sassanyan kallo, shi kuma da alama wanka ya sha, ya zuba farar shadda, yana balle ‘links’ din hannun rigarshi. Suka hada ido, ya yi murmushi.

“Sannu da bakunta, ya ya ki ka samu gidan da ma’aikatanshi?”

Ta yi far da idanunta.

“Komai lafiya kalau”.

Ya ce, “Madalla. Ni yanzu zan tafi asibiti ne, sai gobe zan dawo da safe sabida Hajiya ba ta dawo daga Ji-kas ba da sai ta karbe ni.”

Cikin mamaki Laila ta ce, “Me ake a asibitin? Waye ba lafiya?”

A hankali ya ce mata, “My Little daughter Amina”.

Bai ja bayanin da nisa ba, ita ma ba ta tambaya da nisan ba, duk suka yi shiru. A zuciyarta tana fadin,

“Ranar ‘first night’ dina ita ce ranar jinyar ‘ya?” Mafari kenan da kishin yarinya Amina ya shiga zuciyar amarya Laila. A tashi zuciyar yana sauraro ne ya ji ta ce ‘mu je tare in raka ka’. Ko kuwa ‘me ya sameta?’ Da ya ga babu alamun daya cikin hakan daga gare ta sai ya sa kai ya fita.

“Night”

Ya furta a hankali. Yana mai janyo mata kofar.

Tun daga wannan rana Laila ta ji ta tsani wannan ‘ya ta Ma’arouf don ta lura an kar-maciji ne ba a sare kansa ba, babu uwarta amma za ta zame mata kishiya.

Duk da cewa bayan dawowar Hajiya daga Ji-kas da komawarta asibiti ya ba ta lokutansa yadda ya kamata, an barji amarci Laila ba ta gode ba. Wannan ‘ya ta Ma’arouf ta tsaya mata a makogaro kwarai da gaske, ganin yadda yake ba ta muhimmanci fiye da ita. Kai zata iya cewa fiyeda komai nasa. Ba ta taba zuwa ta duba ta ba, ba ta taba cewa a gaishe ta ba, shi ma Ma’arouf din ya kullaci wannan a zuciyarsa, bai dai nuna mata ba ne.

Baba da Alhaji mansur kan zo duba jikanyarsu lokaci zuwa lokaci. Zabe na karatowa, kamfen na kara tsananta gare su. Ya zamana ba shi da lokacin kansa, sau tari mantawa yake da Laila a cikin gidansa, sai ta kira shi a tafi-da-gidanka, amma hakan bai sa ya daina kula da ‘yarsa a asibiti ba, amma yana mancewa da Laila a gida.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 4.8 / 5. Rating: 6

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Sanadin Kenan 12Sanadin Kenan 14 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×