Skip to content
Part 27 of 50 in the Series Sanadin Kenan by Sumayyah Abdulkadir Takori

A ofishinsa yake, bayan tafiyar Dr. Amina da kwana uku. Mutanen da ke son ganinsa sun fi dari. Ayyukan da ke gabansa wadanda suke bukatar ya sanya hannu (signing) sun fi guda hamsin. Amma me? Ya kasa yin ko daya, ya kasa (attending) ko mutum daya. Idan ya tuna in ya koma gida ba zai tarar da Dr. Amina da Ameena ba sai ya ji wata irin kewa da damuwa sun taru sun lullube shi. Ya kasa aiwatar da komai wadanda ya saba yi a rayuwarsa. Hatta kiran waya damuwa yake jefa shi don jira yake ko Amina za ta turo masa sako, ko ta kira shi ta ba shi amsa kan bukatarsa na zamowarsu abokan rayuwar juna na har abada, amma har aka cinye kwanaki ukun babu ‘text’ ko wayar Dr. Amina. A karshe ya gane mafitar daya ce, ya bar komai ya yi yakin mallaka wa zuciyarsa abin da ta ke so da kauna don ya zauna lafiya cikin nutsuwa da kwanciyar hankali wata da watanni yana dannewa. Amma yanzu an zo wani ‘limit’ da ya fahimci cewa, ci gaba da dannewar nan ba abin da zai haifar a gare shi, sai (Psychological depression), mafitar kawai ita ce auren AMINA. Wadancan falsafofin na auren mace fiye da daya a yau ya sauke su, da ma bai taba rantsuwa a kai ba. Ya kan fada ne dai kawai. Ya fahimci in ya tsaya ta jin amsa daga bakin Amina zai shekara bai ji ba, soyayyar da ke cin zuciyarsa ta zauta shi. Ya yarda ko Amina ba ta sonsa to ba ta kinsa.

Ya amince zai aure ta ko da ba ta sonsa in dai har zai mallake ta cikin gidansa zai samu soyayyar a hankali, kai ko tana kinsa din ya amince ya aure ta, hakan in dai za ta dawo cikin rayuwarsu shi da Amina, ta bar ‘downstairs’ ta koma ‘upstairs’ wannan shi ne babban burin zuciyarsa a yanzu, ya yanke shawarar sauke rawanin Gwamna ya daura na yakin neman soyayyar Amina da aurenta.

Ya dauki wayarsa ya kira mataimakinsa Prof. Bugaje, ya ce duk ayyukan nan da ke gabansa ya yi masa, ya ci gaba da ‘handling’ komai, zai yi hutu na kwanaki uku. Farfesan ya amsa da girmamawa komai ya koma hannunsa.

*****

Ilya ya shigo gidan da yammacin ranar da Amina ta yi kwanaki uku, Goggo ta shiga makota barka. Ya ji dadin samun Amina ita kadai. Tana suyar awara ne da ta tashi da marmarinta tun azahar ta ke aikinta. Ta gama soyawa tana kwashe wa Ilya ya tsaya a kofar kicin din.

“Anty Amina, ina nawa? Raina ya biya wallahi”

Ta ce, “Dauki guda daya, shugaban kicin din gidan Gwamna da kwadayi, ban taba ji ba.”

Ya kyalkyale da dariya ya mika mata farar leda.

“Ungo ga guzurin gidan Gwamnatin na yo miki ke ma, don na san kwana biyu kina kewarsu.”

Ta galla masa harara, “Wa ya ce da kai ina cin abincinsu? Wanda na saba ci shi nake dafawa da kaina.”

Ta dai karbi ledar ta leka, shawarma fal, soyayyun kaji da samosa, springrools da wani dunkulallen cake. Ita da ta ke cewa ba ta ci, sai ga ta tana cika baki tana taunewa tana hadiyewa, kunnenta har motsi yake. Ilya ya dinga yi mata dariya, ya yi kyau ya yi kiba, ya yi tsaf farinsa na Fulani ya fito. Amina har mamaki ta ke yadda Ilya ya murje cikin ‘yan watanni ya waye sosai, kamar ba shi ba.

Ya ja kujera ‘yar tsugunne ya zauna, “Ke muhimmiyar magana ta kawo ni, gidan Goggo ya kammala fa, har an yi fenti. yanzu kudaden abubuwan da za a zuba za ki tura ta account dina, ga takardar abubuwan cikin gidan su kujeru, air-condition, gado, labulaye, cooker gass, carpet, kayan kicin da sauransu. Ga list din da kudin komai a rubuce a kasansa”

Amina ta karba tana dubawa, ta yaba da komai, Ilya dan baiwa yana ba ta mamaki, ya san kaya na zamani masu tsada, amma da quality da nagarta, ban sha’awa da burgewa. Ta zabi kalolin da ta ke so wanda Goggo sune kalolin da ranta ke so, ruwan madara da ‘brown’, ta ce, “An jima zan sako in na gama ciye-ciyen nan, yunwa nake ji, motar fa?”

“Mota tuni ta iso tana rumfar adana motoci na gidan Goggo, na fi so sai ta je can ta same ta. Amma ya za mu yi mu daga Goggo da komai nata daga gidan nan ba tare da ta sani ba? Sai dai mu dauke ta mu kai ta har dakin barcinta?”

Amina ta yi dan tunani, “Ta ce min za ta Shira jibi bikin ‘yar Kawu Bilya, kuma tun safe har dare don haka ka yi kokari daga yau zuwa gobe a saka komai a muhallinsa. Washegarin dawowarta da safe zan ce mata ta raka ni asibiti duba matar Kwamishina Turaki ta haihu na san ba za ta ki ba, Astagfirullah na shirya karya.”

Ilya ya yi dariya, “A kan abin alkhairi ki ka yi karyar ai, Allah zai yafe miki. Gama ci maza ki turo min.”

Ta ce, “Saura kai Ilya. Gidan nan na ba ka shi halak malak. A rushe shi ko a yi furnishing’ dinsa da kyau ya zama na zamani ka nemi mace haka ka yi aure Ilya. Ni zn dauki nauyin ginin, lefe da komai. Ni dai burina ka yi aure Goggo ta ji dadi, tunda nawa babu rana.”

Ilya ya tsura mata ido, kwalla suka cika idonsa.

“Dr. Amina hidimar ba ta yi yawa ba? Na fa tsaya da kafafuna yanzu ina tari tunda na fara aikin nan.”

“Ba ruwana da aikinka Ilya. Burina in faranta wa wadanda suka tsaya min a rayuwa ta a lokacin da na rasa mahaifi. To Ilya kai ne mutum na biyu bayan Goggo da ku ka tsaya wa ilmina. Ba ni da abin da zan biya ka sai dai in kamanta ihsani. Baba Talatu zan turo maka milyan daya ka ba ta ta yi duk abin da ta ga dama da su, ta tallafi ilmin marayunta. Za ka raka ni Shira kuma in na kara hutawa in ba su abin da ya rage min a account bana bukatar komai a rayuwa ta, I’m o.k, mota kawai zan saya saboda zuwa ciki.”

Shi dai Ilya ya kasa magana daga karshe ya yi ta sanya mata albarka kamar shi ya haife ta.

*****

Duk shawarwarin da suka yi ita da Ilya haka suka aiwatar da su. Goggo ta budi ido ta ganta a wani dankareren ‘bungalow’ mai hawa biyu. Ga dalleliyar mota a rufe cikin tamfol an ce ta kai ta unguwa ce. Duk tarkacenta Amina ta bai wa Inna Zulai ta zuba mata sabo. An karo mata mai aiki sun zama biyu sunanta Rabi, suna ci gaba da yin sana’ar ta Goggo, ita kam nata umarni ne da taimakawa, ga samari maza uku masu barrow da suke aiki tare da Ilya tuntuni sun tsaya madadinsa.

Goggo ba ta da bakin gardama Amina ta gama komai, ta cika burinta na kyautata rayuwar Goggonta a shekarun girmanta kamar yadda ta shanye shekarun kuruciyarta cikin aikin karfi da wahala wajen gina rayuwarta da ‘future’ dinta. Ta yi kuka sosai don farin cikin haihuwar ‘ya irin Amina daya fiye a goma. Ta sanya mata albarka har kamar harshenta zai bushe. Ta ce da Amina, “Burina daya ne yanzu a rayuwa, Allah ya nuna min mijinki kamin ya dau raina. Saboda kyautatayinki ga iyaye Amina, jikina yana ba ni Allah ba zai barki haka ba, zai ba ki miji na gari wanda kowa sai ya daga ido ya kalla, wanda zai rike ki da amana ko bayan raina”.

“Wai Goggo me ya sa ki ke kira ma kanki mutuwa ne? Tsufa ki ka yi? Life began at fourty? Insha Allahu sai kin dauki jikokina ba ma ‘ya’yana kadai ba Goggo. Ki daina cewa bayan ranki, zuciya ta tana girgiza.”

Goggo ta ce, “Na bari Amina, Allah ya ci gaba da raya mu tare, rayuwa mai tsayi da albarka. Ya ji kan mahaifinki, Ya yi masa rahama, Ya ba shi aljannah albarkar faranta min da ki ke yi”

Amina na dariya ta ce, “Amin Goggona.”

Goggo ta yi dan jim tana tunani, kafin ta tsare Amina da ido.

“Ina ki ke samun wadannan makudan kudi haka? Wannan ya fi karfin albashinki ko ninki goma ne, musamman ginin gidan nan.”

A wannan lokacin ne Amina ta yi wa Goggo bayanin komai, har wayar da suka yi da Dr. Turaki, ta ci gaba da cewa, “Dr. Turaki ya taba gaya min cewa, da ma ya yi alkawari duk likitan da Ameena ta warke a hannunsa ta sanadinsa, zai ba shi tukwici wanda shi kansa bai sani ba, kuma ya ce a hakan ma ya rage ne kamar yadda shi kwamishina ya ba shi shawara kasancewa ta mace, kuma bukatuna da kudi kadan ne. Na nemi shi Turakin mu raba ya ce wallahi sam, kuma in daina damuwa, a cewarsa a wurin Ji-kas wannan kamar an fidda allura ne daga cikin kogi, sama da haka ma yana bai wa wanda Allah ya ci da shi ko ba su yi masa aikin komai ba”.

Goggo ta yi murmushi tana kallon Amina tana mamakin wautarta watarana, kiri-kiri ga alamomi masu yawa da ke nuna Turaki yana sunsunarwa abokinsa takalmi, mma ba ta gane komai ba. Komai ya gaya mata sai ta hau kai ta yarda. Wannan kulawar da yake ba ta, Ubangidansa yake yi wa. Shi din ne dai ba ta da tabbas din hakan daga gare shi tunda ba ta taba ganinsa ba, sai dai ta tsinci abubuwan da ke gasgata mata tunaninta daga kalaman da Amina ke yi a kanshi, kwashe rbin tantabaru a wane dalili/ In tantabaru yake so ya je kasuya ya saya mana, sai na gado? Jikinta ya ba ta akwai abin da yake son yi wa Amina da tantabarun nan don ta amfana, amma shi me zai yi da su?

Ta nisa a hankali ta dubi Amina, “Na yrda da ke Amina”

Amina ta ji dadin furucin Goggo, don ba ta so ta yi tunanin akwai wani abu binne a zuciyoyinsu ita da Ji-kas din. Watakila ma ya manta da ita, ya bar maganar, ganin har kwanakinta goma a gida babu wayarsa, text dinsa ko aikensa. Damuwa da tunanin kada hakan ta kasance na kassarata, amma hakan ba ya hana ta jarumtar daukar sanda ta fatattaki damuwar da tunanin daga gabanta ba ta shiga harkokinta.

Sati biyu kenan da gama aikin Amina a gidan gwamnati, ba Ma’arouf ba wayarsa, babu ko dan aikensa. Ya rage saura sati biyu ta koma bakin aikinta a asibitin koyarwa na Abubakar Tafawa Balewa.

Duk da fatattakar tunanin da damuwar da rashin jin nasa ya jaza mata wani lokacin zuciyarta na ingiza ta da ta kira shi a waya ta ji ko lafiya? So ba karya ba ne… Kuma ba abu ne da ke faruwa a duk sanda ya so ya gudanar da tunani ya sarrafa gangar jiki… To hakan ce ta faru da Amina da Engnr. Ma’arouf Ji-kas. Juriya da fin karfin zuciya su suka hana Amina kiran Ma’arouf Ji-kas, amma ba zuciyarta ba.

Ina Ma’arouf Ji-kas din?

Yana can cikin takunkumin abokinsa kwamishinasa consultant Dr. Usman Turaki, wanda ya haramta masa tuntubar Amina ko zuwa inda ta ke ko yi mata aike har tsayin sati biyu.

Ya je masa da bukatarsa ne na ya shige masa gaba su dumfari neman auren dalibarsa. Ya gane cewa ba zai iya rayuwa cikin sukuni ba tare da ya aure ta ba, Ameena ta dawo hannunta.

Turaki ya yi dariya a boye, ya yi farin ciki a fili da boye, amma bai bari ya gane ba.

‘LOKACI’ ba abin da ba ya canzawa in ji Dr. Usman Turaki. Yau ga lokaci ya canza Ma’arouf Ji-kas, wanda shi da ma ya tabbata watarana za a yi haka. Amina ba macen da za a zauna da ita na lokaci kalilan a bari ta wuce har abada ba ce. Ba tare da an janyo ta ta dawo ba. Ba don kyawunta kadai ba, sai don dabi’u da halayya, wadanda in ya auna sai ya ga duk irin na Ma’arouf Ji-kas ne, kuma ita kadai ce ta dace da mutum na gari mai kyakkyawar zuciya irin Ma’arouf Habibu Ji-kas. A dai cikin matan da ya sani a fadin duniya. Kasancewarsa likita fitacce, wanda ya yi alaka da mata kala-kala a wajen karatu ne, a wajen aiki ne, a wajen (counselling) da sauransu.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 4

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Sanadin Kenan 26Sanadin Kenan 28 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×