Skip to content
Part 26 of 50 in the Series Sanadin Kenan by Sumayyah Abdulkadir Takori

Murmushi ya yi, domin iya gaskiyarta ta yi furucinta.

“Ku kuma likitoci haka ku ke zama gaban Goggonninku ba kwa ko tunanin yin aure? Dube ki don Allah (close to 26), ko kunyar ambatar Goggo za ta rike ku, ba kya yi bayan ke ma kin isa zama Goggon wasu irin su Ameenata. Amina Mas’ud Shira, in kin amince ki maye min gurbin Babar Ameena. Ina nufin, ina sonki, ina niyyar aurenki ba don Ameena ba, I just love you, so do I since… Amma fa idan har ban yi miki tsufa ba. Ina son dukkan halayenki wadanda su suka ja ni ga kaunar ki  zamo cikin iyalina. Wannan sakona ne gare ki da Goggo, na ba ki kwana uku ki yi tunani da shawara. Kwana uku bai yi kadan ba? Dr. Amina ki ba ni amsa.”

Amina wadda ta mutu a zaune, tun daga farkon furucinsa, ‘In kin maye min gurbin Babar Ameena…’ ta daskare ta kasa motsawa, sai dai abin da ya ba ta mamaki shi ne, jin can wani lungu na zuciyarta ya yi sanyi daga azabtar da yake na rabuwa da Ameena da Baban Ameena, “… Amma fa in har ban yi miki tsufa ba…’

Ta tuno jimlarsa ta gaba. A wannan karon sai ta yi murmushi. At 41, kwarai zai yi wa ‘yammata da yawa tsufa, to ita mai 26 ta ce me? Kada dai sake-saken zuciyar nan yana nufin tuni zuciyarta ta aminta da soyayya da kaunar Baban Ameena? Mutumin da duniya ke so ba abin mamaki ba ne in ita ma ta so shi. Sai dai fa nata wadannan ‘feelings’ din daban suke da na sauran al’umma, irin su Yayanta Ilya, na tana are extra-ordinary. Ba ta taba jin irinsu a kan kowa a duniya ba. Kamar da ma suna ajiye a wani sako na zuciyarta ne, jira suke a sanya kara a zunguro su. Kamar tun da ma can an halicce su a cikin kirjinta ne.

Ta yi nisa a duniyar sake-saken nan, ta sunkuyar da kai ta kasa dagowa. Ba ta san sanda ya mike ya nufi kofa ba. Sai da ya murda marikin kofar ya dan ba da kara, Amina ta dawo daga duniyar tunaninta. A tsakiyar kunnenta ta tsinkayi sautinsa yana fadin.

“In kin gama kintsawa Akilu na jiranki. Ameena za mu wuce Ji-kas da ita, ki gaida Ilyas”. Ya fice.

Ta mike cikin sanyin jiki ta ci gaba da harhada kayan amfaninta. Ameena ta yi kuka ta gaji, ta bingire ta yi bacci. Wannan damar ta samu ta silale da akwatinta biyu. Duk kayan sanyawar da ta tarar a gidan ta yi amfani da su a nan ta barsu, ba ta dauki ko daya ba.

A cikin mota suna tafe suna gaisawa da direba Akilu, ta ji shigowar sako a wayarta. Ta dauko ta duba, sakon shigowar kudi (Alert) ne daga Kwamishina Usman Turaki. Adadin kudin sun ba ta tsoro, sun tada hankalinta. Da hanzari ta danna wa malamin nata kira.

Dr. Turaki ya san za a yi haka, kuma tuni ya shirya karbar kiranta, don haka tana kira ya yi murmushi ya dauka.

“Dr. Amina ya aka yi?”

Amina ta feso ajiyar zuciya.

“Doctor wannan kudin sun fi karfina, me na sayar muku? Me na yi muku na wahala haka? Doctor na fi son iya cikon albashina, Goggo za ta yi zargi, wanda kullum cikinsa nake a gurinta.”

Dr. Turaki ya yi magaan cikin muryar kwantar da hankali.

“Amina, me na gaya miki sanda za ki fara aikin nan? In ban manta ba na ce da ke, ‘Allah ya sa ta hannunki za ta samu lafiyar, ina addu’ar tukwicin hakan ya zamo naki ne’. Kin yi kokari a kan Ameena, ta samu lafiya a hannunki, idan Ma’arouf ya mallaka miki rabin abin da ya mallaka ba zai ji komai ba. Sai bai yi hakan ba, ya yi daidai hankali da tunani don kada ya razana ki. Ina so ki sani, wane ne gwamna kuma Engnr. Ma’arouf Ji-kas, wannan tukwicin da ya ba ki kwatantawa ne ba kankat ba a kan son da yake yi wa ‘yarsa Ameena. Ki sanya a ranki, ilminki ne ya ba ki, SANADIN KENAN!. Ki yi wa mahaifiyarki bayani kada ta damu, ilmin da ta tsaya miki ki ka yi ne ya ba ki, babu matsayin da ilmi ba ya bai wa mutum a rayuwa. Sannan a wajen His Excellency wannan kamar an fitar da allura daga kogi ne so relax please, say thanks to almight Allah, not Ji-kas.”

Amina ta yi murmushi ta sauke wayar. Tunda ya kashe tasa alamar bai son “anymore word from her) karin wata kalma daga gare ta. Ta zama attajira mai zaman kanta sanadin ilminta, ta samu zuciyar mutum irin Ma’arouf Habibu Ji-Kas SANADIN ILMINta.  Dadin dadawa ta samu (exposure) na rayuwa kala daban-daban a gidan gwamnati, wanda za su taimaka mata wajen tafiyar da zamantakewarta har karshen rayuwarta.

Har Akilu ya yi fakin a kofar gidansu tana wadannan tunanninkan. Sai da ta ji motar ta daina motsi ta farga.

“Sai watarana Akilu, daga yau an gama.”

Murmushi ya yi, ya ce, “Ranki ya dade, Allah ya kyautata rayuwarki da ki ka kawo karshen matsalar shugaban. Mun gode, Allah ya kara wa Ameena lafiya”.

“Amin Baba Akilu, sai watarana.” Ta fadi tana ‘waving’ dinsa ta shige gida, sakamakon wasu hawayen sabo da suka shimfido mata, zuciyar ta na gaya mata ta rabu dasu fa kenan ta bar gidan gwamnati har abada! Alfarmar shugaban nasu ba mai yiwuwa ba ce, ba shine irin mijin data tsarawa rayuwarta ba, ina ita ina kishi da Anty Laila? Aka ce yaro tsaya matsayin ka kada zancen ‘yan duniya ya rude ka!  Kwarya ta bi kwarya in tabi akushi sai ta fashe. Jikas mijin mata da yawa ne ba shine Mr. Right dinta ba, jikinta na bata cewa the best is yet to come….. amma atamfar tunanin alkawarin data yiwa Goggo kafin ta barta ta fara aikin Ma’arouf Habibu Jikas sai hankalinta yayi mugun tashi.  Sai ba da kayanta ya yi aka shigo mata da su. Goggonta kadai ta samu a gida, suka yi murnarsu har suka gaji. Wannan karon ma ba ta gaya wa Goggo adadin kudin da ke cikin asusunta ba. Ta dai gaya mata ya biya ta albashinta cikakke, da kudin tantabarunta. Ta ce kyauta ta ba shi, ya ce in ba ta karba ba, zai maido mata kayanta.

Goggo ta ce, “A’a ba a yi haka ba, ki karba.”

Ta yi murmushi, “Na karba Goggo.”

Sun yi sallar isha a daren ranar, bayan Amina ta idar da shafa’i da wutiri ta ji wayarta na kara. Ta dauka ta duba mai kiran ‘HAJIYAN JI-KAS’ Kamar yadda ta adana sunan shi ke yawo a fuskar wayar. Ta juya ta kalli Goggo, sai ta ga lazimi ta ke, da cikakkiyar nutsuwa, da ladabi mai yawa ta amsa kamar yadda ta saba amsa wayar Hajiyan.

“Assalamu alaikum Aminatu”

“Amin wa’alaikis salam Hajiya, Ya ya Ameena?”

Hajiya ta ce, “Kya bari mu gaisa ai Maman Ameena, kwana uku baya ya kamata in bugo wayar tun sanda na ji Ameena ta mike a kan kafafunta. To garin in kira ki saboda farin ciki na jefa wayar tawa a ruwa, sai yanzu da ya zo ya hada min wata (tana nufin Ma’arouf).

Ubangiji shi ya nufa, amma da kokarinki da sadaukarwarki. Mun gode, madalla Amina. Ba ni mahaifiyarki in tana kusa mu gaisa.”

Amina ta mika wa Goggo, “Hajiyan Ji-kas ce.”

Ba tun yau ba Goggo Hauwa ta san Hajiyan Ji-kas, Amina ta sha hada su su gaisa idan ta zo weekend Hajiya ta kira ta. Don haka da sanayya suka gaisa Hajiya ta yi mata godiya a kan taimakon da Dr. Amina ta ba wa jikarta.

Goggo ta ce, “Babu godiya a tsakani, ai aikinta ne. Ko ba ta yi wa Ameena karama ba za ta yi wa sauran al’umma ko ba ko sisi balle Amina da ake biyanta.”

Ita dai Hajiya Saude godiya ta ke tana karawa har suka yi sallama.

Kwana daya, biyu, Amina ba ta da kuzari ta rasa kwarin gwiwar isar da sakon Ma’arouf Ji-kas ga Goggo. Ta bar wa zuciyarta wannan al’amari mai girma da ya tunkaro ta. Ta kasa aiwatar da abubuwan da ta saba yi yadda ya kamata saboda tunanin amsar da za ta bai wa His Excellency da kwarin gwiwar sanar da Goggo. Ita dai zuciyarta ta riga ta gama nutso da ninkaya a cikin maliyar So. So irin wanda ba za ta iya fassarawa ba.

Wanda ba lokaci daya ya shiga zuciyarta ba, ya dade yana kassara ta, yana huda kasusuwa da bargonta a hankali a hankali (like a biological VIRUS). Ba ta ba shi muhimmanci ba ne tun lokacin da ya soma samun muhallin don sanin cewa abu en da ba zai taba yiwuwa ba zuciyarta yaudararta ta ke yi. Don ba ta taba ganin wata alama da ke nuna hakan daga Ma’arouf Ji-kas ba. Mutumin da ko cikakken kallo ba ta ishe shi ba.

Sannan kuma ta kan tuna matarsa ‘yar kwalisa Anty Laila. Ina ita ina iya shiga kishi da wannan kasaitacciyar mace? Yaushe ma ta kai wannan matsayin? Beside, tana jin kamar lokacin yin aure ya wuce mata babu wanda zai kara cewa yana sonta daga shekaru ashirin da shida. Tunanin komawa karo ilmi ne a ranta da zarar ta bar gidan Gwamnati, don haka ta dauko bulo da katon dutse ta danne gurbin da ke darsa soyayyar Ma’arouf a zuciyarta (A baya kenan).

Amma daga shekaranjiya da ya furta neman soyayyarta da aurenta gaba daya sai ta ji kamar an sauke wannan bulo da dutsen da ta adana tsofaffin ajiyarta suka fito zahiri suka lullube zuciyarta.

To amma da wani harshe za ta gaya wa Goggo? Ya ya Goggon za ta dauki al’amarin? Kada ta zarge ta da cewa tun can baya soyayya ta ke yi ba aikinta ba, duk da ta san Goggo ta yarda da ita dari-bisa-dari. Hasashen zuciyarta ne wannan kawai. Gaskiyar magana shi ne, kunyar Goggo ta ke ji. Bari ta yi shiru abinta kawai. Goben a ina zai ganta har ya bukaci jin amsa daga bakinta? Ta san yawan ayyukan da ke kansa ba za su bari ya kara tunawa da wata Dr. Amina ba. Don haka ta like bakinta ta shiga sabgoginta da kula da tantabarunta/ Lokaci-lokaci Ameena Ma’arouf na fado mata a rai, amma in ta tuna tana hannun Hajiyan Ji-kas sai ta ji damuwarta a kan kewar yarinyar ya ragu. Tana da yakinin tana samun kauna da kulawa yadda ya kamata fiye da na Babanta.

Ta lura shi kansa ba ya alakanta rayuwar diyarsa da matarsa Laila, ko me ye dalili? Oho!

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 3

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Sanadin Kenan 25Sanadin Kenan 27 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×