Duk kuma sai ta ji ba dadi, ta shiga damuwa. Amma ita iyakar gaskiyar abin da ke ranta ta fada, ba ta zo don cin daular gidan gwamnati ba. Ta zo neman guminta ne, don haka a sanyaye ta tura jakarta ta fito zuwa inda direban ke jiranta. Ta gaishe shi don ya manyanta.
Ya amsa da karramawa, ya karbi jakarta ya sanya a mota ta shiga suka tafi.
Goggo na alwala a gindin famfo, Amina ta yi sallama. Goggo ta dakata ta amsa tana kallon mai shigowa. Aminanta ce hatta muryarta ta canza. Wani sanyi ya ratsa zuciyarta, da. . .