Skip to content
Part 22 of 50 in the Series Sanadin Kenan by Sumayyah Abdulkadir Takori

Duk kuma sai ta ji ba dadi, ta shiga damuwa. Amma ita iyakar gaskiyar abin da ke ranta ta fada, ba ta zo don cin daular gidan gwamnati ba. Ta zo neman guminta ne, don haka a sanyaye ta tura jakarta ta fito zuwa inda direban ke jiranta. Ta gaishe shi don ya manyanta.

Ya amsa da karramawa, ya karbi jakarta ya sanya a mota ta shiga suka tafi.

Goggo na alwala a gindin famfo, Amina ta yi sallama. Goggo ta dakata ta amsa tana kallon mai shigowa. Aminanta ce hatta muryarta ta canza. Wani sanyi ya ratsa zuciyarta, da gudu Amina ta yar da jakar hannunta ta sheka ta rungume Goggo.

“Na yi kewarki Goggo, na ji dadin samunki lafiya.”

Goggo ta yi murmushi, “Cika ni to in karasa alwalata. Ke kam ban san yaushe za ki girma ba.”

Ta cika ta tana dariya, ta nufi dakin tantabarunta.

Tana ciki tana duba lafiyar kowannensu, Ilya ya yi sallama ya shigo. Ya ce, “Aha! Wannan sassanyan kamshin na san daga inda ya fito. Barka da zuwa Dr. Amina”. Ya fadi tare da dunkule hannu alamar jinjina.

Amina ta ce, “Umh, Ilyan Goggo na Baban Ameena. How I wish zan iya dumi da shi in ba shi labarinka ko watarana ya kira ka ku gaisa.”

Ilya ya gintse fuska, “Kina nufin ba kya ganinsa? Na dauka tuni an wuce nan kin gabatar da ni?”

Amina ta girgiza kai, “Oh-oh! Mutumin nan ina ganinsa dare da rana, ‘as if’ ganin nasa ya fi komai arha. Amma wallahi Ilya bana iya doguwar hira da shi, kamar wani babban Zaki ko Giwa yake zama a idanuna. In ba a kan abin da ya zama dole ba bana iya bude baki a gabansa. Gara yau mun yi zancen mintuna biyar amma ya zama dole ne, saboda mahaifiyarsa da nake amfani da ita wajen jakadanci a tsakaninmu ta tafi. Hirar kuma ba ta dadi ba ce, kai karshe ma baram-baram muka rabu a kan account number.”

Ta kwashe yadda suka yi ta gaya masa.

“Ba ki kyauta ba Amina”. Goggo ta fada, “Tunda ya ce ki ba shi sai ki ba shi kawai, ba abokin musunki ba ne. Watakila shi bai saba da a yi masa musu ba ma. Ba a mayar da hannun kyauta baya, kuma ya ce ba ke zai yi wa ba, a nan ya nuna girmamawa ne ga mahaifiyarki ba wai na damu da abin da zai ba nin ba ne, amma kin san ko me zai bada din girmansa ne. ba abin da zai tsikari abin da yake da shi ba ne, hanya ce ta kyautata wa wanda ya kyautata maka ka ji dadin taimakon da yake yi maka.”

Ilya saboda kuluwa harararta yake.

“Kyale ta Goggo, shashasha ‘yar bukulu. Ni na yi nan Goggo Talatu ba ta jin dadi shi ya sa ba ta zo ba, ina da abubuwan yi da yawa.”

Ya shuri takalminsa ya fice kamar ya kirbi Amina ko ya huce. Shi ba abin da za a bayar din ne ya dame shi ba, a’ah ita wace ce da za ta yi wa masoyinsa musu, har ta bata masa rai? Ina ruwan Ilya mai soyayyar babu gaira babu dalili alhalin ba a san da kai ba.

Haka Amina ta shiga hidindimunta a gidansu kamar yadda ta saba, jefi-jefi Ameena karama na fado mata a rai.

Ta debi kyawawan Tantabaru aure biyu ta saka a karamin keji ta ajiye on cika alkawarin da ta yi. In dare ya yi zama ta ke a gefen gadonta ta shiga bincike cikin manya-manyan littattafan (Physiotherapy) don kara wa kanta sani a kan lalurar ‘Paralysis’. Ba ta da buri a yanzu irin na samun lafiyar Ameena Ma’arouf, tana tausaya mata amma ta fi tausaya wa ubanta, wanda ba shi da kwanciyar hankali sam saboda ita. Don ma dai an ce zuciyar shuwagabanni mai fadi da zurfi ce da suke iya daukar ‘large’ abubuwa ba tare da kowanne ya gogi dan uwansa ba.

Goggo ta ba ta wasu addu’o’i ta ce, a cikin zam-zam za ta dinga tofawa tana shafe mata gabbai da su in tana yi mata gashin kashi. 

*****

Haka Dr. Amina ta ci gaba da aiki a gidan gwamnati har tsayin watanni hudu. Ba ta taba karbar albashinta ba, saboda bai kara yi mata zancen account number ba.

Ranar wata lahadi abincin rana yake bai wa Ameena, bayan ya dawo daga zagayen da yake yi da ita cikin ‘Wheel chair’ a falo, soyayyen ‘Chips’ mai tsananin laushi, duk da laushin nasa sai ya murza mata shi da hannunsa don ta ji saukin ci, yadda ya ga Dr. Amina na yi mata.

Tun ranar juma’a yake jin kansa cikin wata irin kewa da sanyin jiki, wadanda ya rasa daga ina suka zo. Ya san dai ba tafiyar Laila Ji-kas ba ne ya haifar da hakan ba, don ta saba tafiye-tafiyenta na shigo da kaya tun kafin ya zama gwamna bai taba jin komai ba. Yau din ya bude mata wuta ne a kan dole ta je mahaifarta ta kwana biyu, shi ba zai dauki wofintar da iyaye ba saboda rashin hankali da daular duniya, idan kuma ba za ta je ta kwana ba, to ta tattara yanata-yanata ta san inda dare ya yi mata. Dole kan ba yadda za ta yi ta debi kayan sanyawarta biyu, aka cika boot din hummer jeep’ da kayan abinci da sitturu bandir-bandir ta kame a bayan mota da ‘yan sandarta mace a gaban mota, aka nufi Ji-kas da ita.

Wannan ya faru ne ranar asabar ne kwana daya da dawowarta daga Dubai da ta kara komawa check-up. Don haka ‘week end’ din daga shi sai Ameena suka yi shi, ya dauke ta suka koma nashi dakin, a can suka kwana. Ko wanka ya kasa yi mata tun kafin tafiyar Amina ta wannan satin, ba shi da wannan kuzarin. Yana jinsa (incomplete) tamkar wani bari na jikinsa ya mutu shi ma. Ya kuma laluba a zuciya da gangar jikinsa ya kasa gane abin da ya haifar da hakan.

Al’amarin ya ci gaba ‘to such an extent that’ ya taho dakin da Ameena da Dr. Amina suke, yana dube-dube domin ya ji a jikinsa kamar a can din ne ya rasa abin da ya maida shi ‘incomplete’. Ya tsaya ya zuba duka hannayensa biyu a aljihun wandon ‘jeans’ da ke jikinsa yana dube-dube. Ga injinan aikinta nan ba ta tafi da su ba. A can kan madubi kayan shafarta ne da turare guda daya da wani ‘deo-spray’ shi ma guda daya. Ya karasa gaban madubin ya daga turaren ya sunsuna, Sassanyan kamshinta na kullum shi ne a cikin turaren. An rubuta ‘Devidoff (cool water)’. Kayan shafar duka sai da ya bi su ya sunsuna, ta yi gyaran gadon tsaf kamin ta fita. Ya karasa ya zauna a gefen gadon ya yi tagumi, ya dauki filonta ya rungume a cinyoyinsa, ya runtse idonsa.

Yanzu komai ya bayyana gare shi, babu sauran bincike. Dr. Amina Mas’ud yake kewa, bayan tarin nazarinta da ya yi watanni hudu yana yi, ya lura daban ta ke da sauran mata. Abin da bai taba faruwa da shi a kan mace ba bayan Aisha. Ba kuma zai ji shi daidai (cikakke) ba, sai ta dawo cikin gidansa.

Komawa ya yi dakinsa ya dauko Ameena ya dawo da ita dakin. Ameenar ta tambaye shi, “Daddy, Mama ta dawo ne?”

“A’ah Ameena, sai gobe za ta dawo. Mu koma can mu kwana, dakina akwai sanyi”

Ta yi shiru ba ta kara cewa komai ba, don da ma maganar jefi-jefi ta ke yinta.

Suka kwanta a lallausan gadon, ya karanta addu’o’i ya shafe ta da su, sannan ya yi azkar din dare da yake yi kamin ya kwanta. Ya ja lallausar ‘duvet’ din gadon ya rufe su kasancewar lokacin sanyi ne.

Washegari lahadi bayan sun karya shi da Ameena ya dauki wayarsa ya kunna, ya kira Kwamishinan lafiyansa Dr. Usman Turaki.

Turaki ya daga yana fadin, “Ya aka yi ka kunna waya yau lahadi, ya maulaya? Na gaya maka ka bar komai a hannunmu, samun wadataccen hutu yana da kyau a gare ka.”

“Yaushe zan huta tunda ba a halicci dan Adam don ya huta ba? Daga wannan sai wancan. Babban farin cikina Ameena’s condition is improving, bakinta ma ya bude tana magana. Da gaske ka ba ni likita kwararriya, wadda bayan likitanci tana da hikima da basira, on her own unique way. Yanzu dai ba ni lambarta shi ne abin da ya sa na kira ka”

Dadi y rufe Kwamishina Turaki, Allah ya sa Amina ta zamo karshen matsalolin Habibu-Jikas. In abin da ya yi zargi ya zama tabbatacce, bai san irin farin cikin da zai yi ba.

“Zan turo lambar yanzu (through text). Amma ya ya uwargida ta karbi zaman Amina a gidanta?”

“Ban gane ba? Kana nufin ni da gidana akwai mai ba ni ‘do and don’ts ne?’

“Ba haka nake nufi ba, ka san halin mata da kishi, za ta karbi abin the other way round.”

“To ban samu zama da ita ba har yanzu. Saboda ta yi tafiya ranar da Aminan ta zo. Ranar da ta dawo kuma Aminan ta je gida, da ta dawo na gabatar mata da Amina ba ta ce komai ba, harkokinta ta ci gaba da yi, amma bana jin ko gaisawa sun yi, ba ta zuwa inda ta ke. Ta sake komawa ta dawo,  a ranar ne kuma na kada ta Ji-kas ta gaida iyayenta, don ita ba ta san ya kamata ba sam sai an yi mata jan ido. Amina nake so zan tura Akilu ya dauko ta shi ne ya sa na ke son lambatra don in gaya mata ga shi nan zai taho. Ba zan iya bari sai yamma ba kamar yadda muke yi. Abubuwa da yawa ina kasa yi wa Ameena.”

Turaki ya jinjina kai zuciyarsa kal, a ransa ya ce, ‘A juri zuwa rafi dai… wanda bai iya kallon mata ba yake kuma zaune da wadda ya tabbatar ba sonsa ta ke ba, kudinsa ta ke so. Ina nan zaune za ka kira ni.’

Suna gama magana ya tura masa lambar. Ya tsura wa lambobin ido kamar mai shawara da zuciyarsa kan ya kira ko kada ya kira? Abu ne da bai taba yi wa wata mace a rayuwarsa ba bayan Aisha. Bai taba kiran Laila ba, ita ta ke kiransa.

Me ya sa ya damu da Dr. Amina har haka? Kwarai yake son jin sassanyar muryarta mai cike da tsiwa a wasu lokutan hakan na faruwa da shi, duk sanda ta je gida. Ko dai ya sa Turaki ya kira ta ya fada mata? Kama kanka Ma’arouf yarinyar nan wata iri ce. Ita ce mutum ta farko da ta taba yi maka musu a rayuwarka. ‘Be careful’ da girmanka a idanunka’

Don haka maimakon kira sai ya rubuta mata sako mai layi biyu kacal.

‘Ga Akilu nan ya taho daukarki, please don’t ask me why?’ Ji-Kas.

Amina na zuba wa tantabarunta abinci da ruwa a safiyar lahadi da waya a kunnenta tana magana da wata abokiyar aikinta Dr. Nazifa da ke ‘special hospital Bacas’ tana gamawa sakon ya shigo wayarta.

Ta ji karar shigowar tasa, don haka ta ajiye kwanon dawar da ke hannunta ta bude. Tun kafin ta karanta ta ji gabanta ya yanke ya fadi ganin sunan da ta yi ‘saving’ watanni biyar a baya ya bayyana; JI-KAS!

Ba shakka ta firgita, tunda har ya yi mata sako da kansa wani muhimmin abu ne ganin bai taba yi ba a tsawon zamansu na watanni hudu. Allah ya sa ba wani abu ne ya samu Ameena ba. Da sauri ta karanta.

Ta yi dan jimm! Tana tunani. Daga baya ta fito ta gaya wa Goggo da ke kwabin ‘meatpie’ madafi (kicin).

Goggo ta ce, “Ai sai ki yi sauri ki shirya Allah ya sa yarinyar lafiya ta ke.”

Tuni ta yi wankanta da ma, tana tattara ‘yan komatsanta cikin ‘handbag’ da ta zo da ita, ba ta dauko babbar jakarta in za ta zo, suka ji dirin mota a kofar gida. Ilya ba ya nan balle su tafi tare, suka yi sallama ita da Goggo da Talatu ta fito. Akilu ya karbi kejin tantabarun ya bude mata kofar motar ta shiga, ya ajiye kejin ya ja tana rokonsa kada ya kara fitowa ya bude mata kofa, domin a haife ya haife ta.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 3

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Sanadin Kenan 21Sanadin Kenan 23 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×