Bayan gama wayarsu da Turaki, ta kira Ilya. ta yi ringing har ta gaji bai dauka ba. Ta gaya wa Goggo wai Baban Ameena ya ce yana gaida Ilya. Mamaki zai zautata, wa ya yi masa zancen Ilya? A ina ya sanshi? Goggo ta yi shiru tana kallon Amina, zancen Ji-kas ya yi yawa a bakin Amina. Daga wannan sai wancan. Ta danne tunaninta, ta ce, "To wadannan mutanen mene ne abin mamaki in sun binciko abu?"
Amina ta ce, "Har account number dina."
A nan Goggo ta dan yi shiru, amma ba ta nuna wa Amina komai a. . .