Skip to content
Part 24 of 50 in the Series Sanadin Kenan by Sumayyah Abdulkadir Takori

Bayan gama wayarsu da Turaki, ta kira Ilya. ta yi ringing har ta gaji bai dauka ba. Ta gaya wa Goggo wai Baban Ameena ya ce yana gaida Ilya. Mamaki zai zautata, wa ya yi masa zancen Ilya? A ina ya sanshi? Goggo ta yi shiru tana kallon Amina, zancen Ji-kas ya yi yawa a bakin Amina. Daga wannan sai wancan. Ta danne tunaninta, ta ce, “To wadannan mutanen mene ne abin mamaki in sun binciko abu?”

Amina ta ce, “Har account number dina.”

A nan Goggo ta dan yi shiru, amma ba ta nuna wa Amina komai a fuskarta ba.

Amina ta yi shiru, maganar albashi da kudin tantabaru (kamar yadda Turaki ya ce), ta barsu a ranta har zuwa wa’adin aikinta ta isar da muradinta. In ta ce za ta mayar Dr. Turaki zai ga kamar raini ya shiga tsakaninsu, haka wanda ya turo kudin ba za ta ji dadi ya ce ya dawo mata da tantabarunta ba.

Tana tunane-tunanenta har aka sanar da ita Akilu ya zo daukarta. Tare da shi wata irin babbar mota ce mara kujeru suka kwashi tantabarun. Ita kuma suka yi sallama da goggo suka tafi.

Tana ta sauri ta isa ga Amina suka yi karo da mai fitowa, saura kadan Amina ta fadi. Ta dafa kofa ta dago don ganin waye haka da tafiya kai a sama? Aunty Laila ce kamar yadda ake kiranta a gidan.

Amina ba ta yi mamaki ba, ta ba ta hanya ta wuce bayan ta rafka mata tsaki. Hakan ta sha faruwa in dai suka hadu. Don ba ta shiga dakin da suke. Amina ta tuno da haduwarsu ta farko da Aunty Laila.

Ranar wata litinin ce, ta dawo weekend da kwana daya, a ranar ne kuma Laila ta dawo daga tafiyar da ta yi. A lokacin ko gaisuwa ba ta shiga tsakaninta da ubangidanta kasancewarsa shi ma marar sakin fuska kamar matarsa.

Ta ga kofar dakin daya daga shigififin falon ‘downstair’ dinsu a bude, kuma an kunna karatun alkur’ani yana tashi daga radiyo. Ta tambayi mai aikin da ke bayanta, “Hajiyan Ji-kas ta zo ne?”

Ya ce, “A’ah likitar Ameena ce da Ameena a ciki.”

“Likita?” Ta tambaya cikin mamaki.

Mai aikin ya ce, “Eh, mai kirkin gaske”.

Kawai sai ta danna kai dakin babu sallama duk Amina na jinsu.

Kallo daya ta yi wa Amina ta ji ba wanda ta tsana duk duniya irinta, saboda wasu irin ilhamomi da kuruciya da wadatar ilimi da ke tare da yarinyar.

Amina ta katse kallon kurillar da ta ke mata da cewa, “barka da dawowa, ina wuni?”

Laila ta buga tsaki ta juya. Ko Ameena karama ba ta kalla ba. Ban da ta san halinsa da tsarin rayuwarsa babu mata a ciki ko cikin al’amuransa da burirrikansa, da ba za ta bar wannan likitar ta zauna mata a gida ba. Ko ta halin kaka sai ta kore ta. Wani bangare na zuciyarta ya ce, “kin isa? Ke a wa? Ya yi hukunci a kan rayuwar diyarsa da ki ka nuna ba za ki iya ba ki ce ba haka ba? Ai sauki da adalci ya yi miki”.

Tun daga wannan ranar in sun hadu za ta san yadda ta yi ta bangaje ta ta harare ta, ta yi mata tsaki. Abin har dariya yake bai wa Amina, don haka duk sanda suka hadu tun daga nesa za ta kauce mata, wanda ma ba su fiya haduwar ba. Duk abin da ta ke nema tana da shi a dakinsu. Fitowarta sai in za ta zaga da Ameena a wheel-chair ta sha iska. Ba ta kuma taba yin gigin hawa ‘upstairs’ ba inda suke da mijinta.

Ta nisa daga tunanin da ta ke yi ta wuce ciki ta tadda Amina, ya kwantar da ita ya tafi tana ta barci.

Kwana biyu ba su kara ganinshi ba, ya je seminar jihar Lagos. Ranar da ya dawo laraba tana yi wa Ameena ‘chemotherapy’ aka yi mata kararrawar kira, zuw falo na hudu kamin a tadda inda suke. Ta yi hanzarin kammala abin da ta ke yi, ta sanya Ameena cikin wheel-chair ta gangaro da ita suka fito tare zuwa falon da kiran ya fito.

Amina ta daskare a tsaye ganin abin da ke faruwa. An shake katafaren ‘dinning table’ din da na’u’in abinci kala daban-daban. Ga wasu ‘greating cards’ manya-manya an manna a kowacce kusurwa ta falon. Mutum biyu ne zaune a ‘dinning’ din suna cin abinci, a jikin kowanne ‘greating card’ an rubuta ‘Welcome to Government House ILYAS.’

Duk suka dago suka dube ta da murmushi, Ilya da Gwamna Ma’arouf Habibu Ji-kas. ta hada ido da Ilya idonsa cike da hawaye ga murmushi yana yi, da gani hawayen farin ciki ne. Ya sha farar shadda kal ‘yar ciki da babbar riga da hula, kamar ba Ilya ba.

Ta kama baki da hannu daya tana kallonsu. Baban Ameena murmushi yake yi, Ilya kuka da dariya, ya ce, “Dr. Amina.”

Amina ta ajiye mamakinta a gefe, ta ce, “Ilyan Goggo?”

Ya ce, “Na’am, SANADIN ILMINKI Amina, Sanadin ilminki yau ga ni ga JI-KAS! ba zan iya kwatanta miki farin cikina ba. Sanadinki na hadu da wanda na fi kauna a rayuwa ta…” Sai kuka.

Amina ta karaso inda suke tana turo keken Ameena a hankali, ta zauna a wata lallausar kujera a gefen Ilya, Ameena na cikin kujerarta a gabanta.

Ta ce, “To Ilya ai ni ban fada masa ba, ban taba yi masa zancenka ba…”

“Kada ki cika kwakkwafi…” In ji Baban Amina, “Kina zaton zan amince in damka amanar ‘yata guda daya ga mutumin da ba ni da cikakken sani a kansa da asalinsa? Wajenki ya zo ku gaisa, an gaya masa kina ta nemansa kafin ki taho last week”.

Ya mike yana goge hawayen da ’tissue’ ya wuce su, bayan ya kama hannun Ameena ya saki ya wuce.

Amina jikinta har rawa yake ta kara matsawa kusa da ‘dinning’ din.

“Ilya ya aka yi? Last week ya ce in gaishe ka, a ina ku ka hadu? Kai ka ba shi account number dina?”

Ilya ya goge idonsa yana dariya, “Wallahi Amina ni ne. Wannan kwamishinan malaminku ya zo har gida bidar account din da kansa, Goggo ta ce in ba shi. Ya tambaye ni, ni ne Ilya? Na ce ni ne, sai kawai ya ce in biyo shi. Da farko Goggo ta dan ji tsoro kada a ce laifi na yi, na ce mata ta kwantar da hankalinta shi ne wanda ya zabe ki yi aikin ai. Haka ya dauko ni a mota, bai ajiye ni a ko’ina ba sai ofishin Gwama, sai ga ni ga JI-QAS ido da ido.

Ya ba ni hannu, ya ba ni ruwa na sha. Kwamishina ya gaya masa ni yayanki ne ba na ciki daya ba, kuma kin gaya masa yadda nake matukar kaunarsa tun kafin ki fara aikin nan, da yadda na ja ku ke da Goggo ku ka je ku ka jefa masa kuri’a. Ya ji dadi sosai, ya gode mini, ya kuma gayyace ni yau in zo mu ci abincin rana tare. Wadannan kayan na jikina shi ya aika mini ya ce nashi ne, in sanya in zan zo….”

Amina ta ce, “Ikon Allah”

Ya ce, “Ke ce SANADI ai. ya kuma dauke ni aiki a gidan nan ni ma, ni ne shigaban babban kicin.”

Da fari ya tambaye ni na yi karatu ne? Na ce a’a sai na yaki da jahilci. Ban taba dana sanin rashin tsayawa in yi karatu mai zurfi ba Amina sai yau. Don cewa ya yi, da ya ba ni mai bashi shawara kan harkokin matasa.”

Amina ta yi dariya, “Har na hango Ilyan Goggo a office”.

Suka sa dariya, ya ce, “Wannan din ma da kyar zan karba, in na bar Goggo ya ya za ta yi da tata sana’ar tunda ni ne karfinta?”

Amina ta ce, “Ka nada wani cikin yaranka masu tayaka wanda ya gane kan container, amma kai namiji ne iyali za ka tara, dole ka tsaya da kafafunka, Goggo ma za ta fi son haka fiye da a ce saboda tata sana’ar kai ka kasa tsayawa ka gina kanka.”

Ya mike yana sabe hannun babbar riga, “Ke kin faya tsari. Bari dai sai na yi shawara da Goggon. Ni na tafi.”

Ka gaida gida, Goggo da Inna Zulai, Talatuna da tantabaruna”.

“Za su ji! Wannan ce ‘yar taki?” Ya fada yana dafa kan Ameena.

“Ita ce Ameena.”

“Allah sarki! Yarinya kamar Babanta ya yi kaki. Allah ya ba ki lafiya Ameena”.

Ameena karama ta ce, “Amin”

Suka yi sallama ya tafi, ta tura Ameena suka koma.

*****

Haka Amina ta ci gaba da aiki a gidan Ji-Kas har ga shi yau ta debi watanni takwas tana kula da Ameena da iyakar iyawarta da iya zurfin ilmin da Allah ya hore mata. Kullum kuma yarinya Ameena kara samun lafiya da kuzari ta ke. Hannayenta hagu da dama duk suna motsi, kafar ce guda daya har yau Allah bai ba ta damar takawa ba, Amina ta soma yi mata amfani da karafuna biyu hagu da dama, tana taimaka mata tana koyon takawa da su.

A hankali sabo mai tsanani ya ci gaba da shiga tsakanin Gwamna Ji-kas da Amina, hali shi ne babban abin da ke sanya soyayya. A kullum Ma’arouf Ji-kas cikin (observing) halayen Amina yake, na yau daban, na gobe daban masu yi masa kama da na AISHA. A sannu soyayya mai girma ta soma ginuwa a zuciyarsa ba tare da sanin shi kansa ba. Abin da ya nuna masa son Aminan ya dade da kama shi, shi ne halin kewar da yake samun kansa a ciki a duk lokacin da ta je gida, ga damuwa da al’amuranta. Ga son ganinta akai-akai, ga son jin muryarta.

Goggo da Ilya wanda yanzu ya zama babban (officer) na (catering) a gidan gwamnati sun dade da gane His Excellency son Amina yake yi, amma ita wawiyar har gobe ta sanya Baban Ameena a matsayin wani mutum mai son ci gabanta, mai kula da al’amuranta, mai darajja iyayenta. Don haka ita ma a gare ta Ma’arouf Habibu Ji-kas mutum ne mai GIRMA da kima a gare ta. A gefe ga kaunar da Hajiya ke mata kamar ta hadiye ta, kusan kullum sai sun yi waya. Hajiya na da wannan dadadden burin a zuciyarta na Allah ya hada zuciyoyin Ma’arouf da Amina, amma idan ta tuna tsarin da a kullum yake fadin ya yi wa rayuwarsa, sai jikinta ya yi sanyi. Duk da haka tana addu’a idan Allah ya tashi sauya zuciyar Ma’arouf daga kan tsarinsa na auren mata daya kacal, Ya sanya Amina ce. Ita ba za ta tilasta masa ya kara aure ba, ko ta tallata masa Amina ya zo ya ce a’ah ta zubar mata da martaba a banza, a idanunsa.

A daya gefen zamansa da Laila na kara tabarbarewa. Kullum ba ta gida, in kuma tana nan za ka tadda falonta cike da kawaye da women leaders. Idonta ya bude sosai ta yadda har ba ta da lokacinsa. Ko tafiya ce ta kama shi ya nemi rakiyarta ba ya samu yanzu, za ta ce tana da biki, ko gayyatar taro ya je abinsa.

Tafiya ta yi tafiya aka gangara watanni goma, Ma’arouf Ji-kas ya soma ganewa, wato bayan ilmin likitancin tada mataccen kashi da Allah ya bai wa Amina, tana da sani a fannonin rayuwa daban-daban. A hankali zuciyarsa ta soma darsa masa soyayyar Amina mai girman gaske.

A karshen wata na goma ne Amina ta duba asusunta. Kudin ciki sun ba ta tsoro, sai ta ga lokacin da ya dace ta cika burinta a kan Goggonta ya yi.

A wani yammaci ta kira Ilya kafin ya wuce gida, bayan ya tashi daga aiki. Suka zuna a wani karamin falo, ta ce, “Ilya ka taimaka mani, na samu abin da zai ishe ni cika burina. So nake Goggo ta ji dadi a wannan siradin na rayuwarta. Ta daina wannan wahalalliyar sana’ar, shekarunta sun ja. Ta daina shiga motar haya, ta je ta sauke farali. A rushe gidanmu a yi mata na zamani. ga abin da nake da shi, gaba daya na damka wannan hidimar a hannunka. Ina kuma rokonka kada ka gaya mata sai ka kammala komai. Aikin hajji kuwa sai an sa musu ranar tashi za ka gaya mata”.

Ilya ya dubi Amina, sai ya ga tana share hawaye.

“To kukan na mene ne kuma? Allah ya yi miki albarka Amina, Allah ya ba ki miji na gari da zuri’a mai albarka masu jin kan mahaifa. Hakika ni ma na yi wannan tunanin, lokaci ya yi da Goggo za ta huta haka a rayuwarta tunda dukkanmu ni da ke yanzu mun tsaya da kafafunmu. Ta daina aikin wahalar nan.”

Amina ta yi sharbe, “Ba komai ya sa ni kuka ba Ilya, illa tuna Baba da na yi. How I wish shi ma yana raye? Ya shigo cikin inuwar ilmin da suka dora ni a kai? Allah ya yi masa rahama.”

“Daina kukan haka, ya isa. Ki ba ni kwana bakwai komai zai kammala a gabanta insha Allah. Amma maganar gini ki ba ni wata daya, ba nata za a rushe ba, saboda za a yi. In aka ce sai an rushe dole sai ta fito daga gidan, kuma sai ta tambayi ba’asi. Sabon fili za a saya a gaba kadan. Aikin hajj kuwa an kusa gama biyan na wannan shekarar, don haka zan hanzarta. Mota kuwa Kwatano za ni na auno mai kyau, Allah ya yi miki albarka”

Amina ta ce, “Sai abu na biyu. So nake Goggo ta daina wannan sana’ar wahalar daga lokacin da za ta tare a sabon gidanta, zan dinga raba albashina biyu duk wata in ba ta rabi”

Ilya ya dan girgiza kai, “Da kyar za ta yarda da wannan. Zan dai dauki ma’aikata a dinga biyansu su ci gaba da komai nata ya zamo umarni”.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 2

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Sanadin Kenan 23Sanadin Kenan 25 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×