Skip to content
Part 37 of 50 in the Series Sanadin Kenan by Sumayyah Abdulkadir Takori

Goggonta kadai ta samu a gida, suka yi murnarsu har suka gaji. Wannan karon ma ba ta gaya wa Goggo adadin kudin da ke cikin asusunta ba. Ta san Goggo tsorata zata yi ko ta darsawa ranta zargi, ta dai gaya mata ya biya ta albashinta cikakke, da kudin tantabarunta. Ta ce musu kyauta ta ba shi, ya ce in ba ta karba ba, zai maido mata kayanta.

Goggo ta ce,

“A’a ba a yi haka ba, ki karba.”

Ta yi murmushi,

“Na karba Goggo”

Sun yi sallar isha a daren ranar, bayan Amina ta idar da shafa’i da wutiri ta ji wayarta na kara. Ta dauka ta duba mai kiran ‘HAJIYAN JI-KAS’ Kamar yadda ta adana sunan, shi ke yawo a fuskar wayar. Ta juya ta kalli Goggo, sai ta ga lazimi ta ke, da cikakkiyar nutsuwa, da ladabi mai yawa ta amsa kamar yadda ta saba amsa wayar Hajiyan.

“Assalamu alaikum Aminatu”

“Amin wa’alaikumus salam Hajiya, Ya ya Ameena?”

Hajiya ta ce, “Kya bari mu gaisa ai Mai Ameena, kwana uku baya ya kamata in bugo wayar tun sanda na ji Ameena ta mike a kan kafafunta. To garin in kira ki saboda farin ciki na jefa wayar tawa a ruwa, sai yanzu da ya zo ya hada min wata (tana nufin Ma’arouf).

Ubangiji shi ya nufa, amma da kokarinki da sadaukarwarki. Mun gode, madalla Amina. Ba ni mahaifiyarki in tana kusa mu gaisa.”

Amina ta mika wa Goggo, “Hajiyan Ji-kas ce.”

Ba tun yau ba Goggo Hauwa ta san Hajiyan Ji-kas, Amina ta sha hada su su gaisa idan ta zo (weekend) Hajiyan ta kira ta. Don haka da sanayya suka gaisa Hajiya ta yi mata godiya a kan taimakon da Dr. Amina ta bawa jikarta.

Goggo ta ce, “Babu godiya a tsakani, ai aikinta ne. Ko ba ta yi wa Ameena karama ba za ta yi wa sauran al’umma ko ba ko sisi balle Amina da ake biyanta.”

Ita dai Hajiya Saude godiya ta ke tana karawa har suka yi sallama. A ganinta basu da abinda zasu biya Amina duk tarin dukiyar su.

*****

Kwana daya, biyu, Amina ba ta da kuzari, ta rasa kwarin gwiwar isar da sakon Ma’arouf ga Goggo. Ta barwa zuciyarta wannan al’amari mai girma da ya tunkaro ta. Ta kasa aiwatar da abubuwan da ta saba yi yadda ya kamata saboda tunanin amsar da za ta bai wa His Excellency da kwarin gwiwar sanar da Goggo. Tuni dai zuciyarta ta riga ta gama nutso da ninkaya cikin maliyar So. So irin wanda ba za ta iya fassarawa ba.

Tun tana ignoring fassarar abubuwan da take ji din da gangan akan Ma’arouf, da  kalubalenta kala-kala marassa madafa, ba shine Mr. Right ba da sauransu, wannan da wancan, har ta yarda ta fassarasu da Son Ma’arouf ne.

Wanda ba lokaci daya ya shiga zuciyarta ba, ya dade yana kassara ta, yana huda kasusuwa da bargonta a hankali a hankali (like a biological VIRUS). Bata bashi muhimmanci ba ne tun lokacin da ya soma samun muhallin, don sanin cewa abu ne da ba zai taba yiwuwa ba, zuciyarta yaudararta ta ke yi. Don ba ta taba ganin wata alama da ke nuna hakan daga Ma’arouf Ji-kas ba. Mutumin da ko cikakken kallo ba ta ishe shi ba a baya.

A hankali suka soma shakuwa, shakuwa mai yawa akan siyasarsa, duk da hakan babu wata alama makamanciyar wannan data gitta a tsakaninsu.

Sannan kuma ta kan tuna matarsa ‘yar kwalisa Anty Laila. Ina ita ina iya shiga kishi da wannan kasaitacciyar mace? Wadda bata ajiye kanta anan kusa ba? Yaushe ma ta kai wannan matsayin banda giggiwa irin na zuciya? Beside, tana jin kamar lokacin yin aure ya wuce mata babu wanda zai kara cewa yana sonta daga shekaru ashirin da shida. Tunanin komawa karo ilmi ne a ranta da zarar ta bar gidan Gwamnati, don haka ta dauko gingimemen bulo da katon dutse ta danne gurbin da ke darsa soyayyar Ma’arouf a zuciyarta (A baya kenan).

Amma daga kwana uku baya da ya furta neman soyayyarta da ra’ayin sa na son aurenta gaba daya sai ta ji kamar an sauke wannan bulo da dutsen da ta adana tsofaffin ajiyarta suka fito suka yi yabanya suka lullube zuciyarta.

To amma da wane harshe za ta gaya wa Goggo? Ya ya Goggon za ta dauki al’amarin? Kada ta zarge ta da cewa tun can baya soyayya ta ke yi ba aikinta ba, duk da ta san Goggo ta yarda da ita dari-bisa-dari. Hasashen zuciyarta ne wannan kawai. Gaskiyar magana shi ne, kunyar Goggo ta ke ji. Bari ta yi shiru abinta kawai. A ina zai ganta har ya bukaci jin amsa daga bakinta? Ta san yawan ayyukan da ke kansa ba za su bari ya kara tunawa da wata Dr. Amina ba.

Don haka ta like bakinta da (super glue) ta shiga sabgoginta da kula da tantabarunta. Lokaci-lokaci Ameena Ma’arouf na fado mata a rai, sai tace cikin ranta, ko an kaita makarantar kwanan? Amma in ta tuna tana hannun Hajiyan Ji-kas sai ta ji damuwarta a kan kewar yarinyar ya ragu. Tana da yakinin tana samun kauna da kulawa yadda ya kamata fiye da na Babanta.

Ta lura shi kansa ba ya alakanta rayuwar diyarsa da matarsa Laila, ko me ye dalili? Oho!

*****

A ofishinsa yake, bayan tafiyar Dr. Amina da kwana uku. Mutanen da ke son ganinsa sun fi dari. Ayyukan da ke gabansa wadanda suke bukatar ya sanya hannu (signing) sun fi guda hamsin. Amma me? Ya kasa yin ko daya, ya kasa (attending) ko mutum daya. Idan ya tuna in ya koma gida ba zai tarar da Dr. Amina da Ameena ba sai ya ji wani irin  kadaici da damuwa sun taru sun lullube shi. Kamar shikadai ya rage a duniyar Subhana. Ya kasa aiwatar da komai wadanda ya saba yi a rayuwarsa. Hatta kiran waya damuwa yake jefa shi don jira yake ko Amina za ta turo masa sako, ko ta kira shi ta ba shi amsa kan bukatarsa na zamowarsu abokan rayuwar juna na har abada, amma har aka cinye kwanaki ukun babu ‘text’ ko wayar Dr. Amina.

A karshe ya gane mafitar daya ce, ya bar komai ya ajiye komai dake gabansa ya yi yakin mallakawa zuciyarsa abin da ta ke so da kauna wannan gem mai daraja wato AMINAH don ya zauna lafiya cikin nutsuwa da kwanciyar hankali, wata da watanni yana dannewa, yana boye halin da zuciyarsa ke ciki.

Amma yanzun an zo wani limit (geji) da ya fahimci cewa, ci gaba da dannewar nan ba abin da zai haifar a gare shi sai (psychological depression), mafitar kawai ita ce mallakar AMINA.

Wadancan falsafofin na gudun auren mace fiye da daya, a yau ya sauke su a gefe, da ma bai taba rantsuwa a kai ba. Ya kan fada ne dai kawai a matsayin ra’ayin sa. Ya fahimci in ya tsaya ta jin amsa daga bakin Amina zai shekara bai ji ba, soyayyar da ke cin zuciyarsa ta zauta shi. Ya yarda ko Amina ba ta sonsa to ba ta kinsa.

Ya amince zai aure ta ko da ba ta sonsa in dai har zai mallake ta cikin gidansa zai samu soyayyar a hankali, kai ko tana kinsa din ya amince ya aure ta a hakan, in dai za ta dawo cikin rayuwarsu shi da Amina, ta bar downstairs ta koma upstairs wannan shi ne babban burin zuciyarsa a yanzu, ya yanke shawarar sauke rawanin Gwamna ya nada na yakin neman soyayyar Amina da aurenta.

Ya dauki wayarsa ya kira mataimakinsa Prof. Yusuf Bugaje, ya ce duk ayyukan nan da ke gabansa ya yi masa, ya ci gaba da handling komai, zai yi hutu na kwanaki uku. Farfesan ya amsa da girmamawa komai ya koma hannunsa.

*****

Ilya ya shigo gidan da yammacin ranar da Amina ta yi kwanaki uku da dawowa.  Goggo ta shiga makota barka. Ya ji dadin samun Amina ita kadai. Tana suyar awara ne da ta tashi da marmarinta tun azahar ta ke aikinta. Ta gama soyawa tana kwashe wa Ilya ya tsaya a kofar kicin din.

“Anty Amina, ina nawa? Raina ya biya wallahi”

Ta ce, “Dauki guda daya, shugaban kicin din gidan Gwamna da kwadayi, ban taba ji ba”

Ya kyalkyale da dariya ya mika mata farar leda.

“Ungo ga guzurin gidan Gwamnatin na yo miki ke ma, don na san kwana biyu kina kewarsu”

Ta galla masa harara, “Wa ya ce da kai ina cin abincinsu? Wanda na saba ci shi nake dafawa da kaina”

Ta dai karbi ledar ta leka, (shawarma fal, soyayyun kaji da samosa, spring roll da wani dunkulallen cake). Ita da ta ke cewa ba ta ci, sai ga ta tana cika baki tana taunewa tana hadiyewa, kunnenta har motsi yake. Ilya ya dinga yi mata dariya, ya yi kyau ya yi kiba, ya yi tsaf farinsa na Fulani ya fito. Amina har mamaki ta ke yadda Ilya ya murje cikin ‘yan watanni ya waye sosai, kamar ba shi ba.

Ya ja kujera ‘yar tsugunne ya zauna, “Ke muhimmiyar magana ta kawo ni, gidan Goggo ya kammala fa, har an yi fenti. yanzu kudaden abubuwan da za a zuba za ki tura ta account dina, ga takardar abubuwan cikin gidan su kujeru, air-conditions,  kayan gado, labulaye, cooker gass, carpet, kayan kicin da sauransu. Ga list din da kudin komai a rubuce a kasansa”

Amina ta karba tana dubawa, ta yaba da komai, Ilya dan baiwa yana ba ta mamaki, ya san kaya na zamani masu tsada, amma da quality da nagarta, ban sha’awa da burgewa. Ta zabi kalolin da ta ke so wanda Goggo sune kalolin da ranta ke so, ruwan madara da brown, ta ce, “An jima zan sako (transfer) in na gama ciye-ciyen nan, yunwa nake ji yanzu, motar fa?”

“Mota tuni ta iso tana rumfar adana motoci na gidan, kamfanin lange&grant sukayi ginin. Na fi so sai ta je can ta same ta. Amma ya za mu yi mu daga Goggo da komai nata daga gidan nan ba tare da ta sani ba? Sai dai mu dauke ta mu kai ta har dakin barcinta?”

Amina ta yi dan tunani, “Ta ce min za ta Shira jibi bikin ‘yar Kawu Bilya, kuma tun safe har dare don haka ka yi kokari daga yau zuwa gobe a saka komai a muhallinsa. Washegarin dawowarta da safe zan ce mata ta raka ni asibiti duba matar Kwamishina Turaki ta haihu na san ba za ta ki ba, Astagfirullah na shirya karya”

Ilya ya yi dariya, “A kan abin alkhairi ki ka yi karyar ai, Allah zai yafe miki. Gama ci maza ki turo min.”

Ta ce, “Saura kai Ilya. Gidan nan na ba ka shi halak malak. A rushe shi ko a yi furnishing dinsa da kyau ya zama na zamani ka nemi mace haka ka yi aure Ilya. Ni zan dauki nauyin ginin, lefe da komai. Ni dai burina ka yi aure Goggo ta ji dadi, tunda nawa babu rana.”

Ilya ya tsura mata ido, kwalla suka cika idonsa.

“Dr. Amina hidimar ba ta yi yawa ba? Na fa tsaya da kafafuna yanzu ina tari tunda na fara aikin nan.”

“Ba ruwana da aikinka Ilya. Burina in faranta wa wadanda suka tsaya min a rayuwa ta a lokacin da na rasa mahaifi. To Ilya kai ne mutum na biyu bayan Goggo da ku ka tsaya wa ilmina. Ba ni da abin da zan biya ka sai dai in kamanta ihsani. Baba Talatu zan turo maka kudi ka ba ta ta yi duk abin da ta ga dama da su, ta tallafi ilmin marayunta. Haka Inna Zulai. Za ka raka ni Shira kuma in na kara hutawa in ba su abin da ya rage min a account bana bukatar komai a rayuwa ta, I’m o.k, mota kawai zan saya saboda zuwa aiki.”

Shi dai Ilya ya kasa magana daga karshe ya yi ta sanya mata albarka kamar shi ya haife ta.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Sanadin Kenan 36Sanadin Kenan 37 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×