Skip to content
Part 4 of 50 in the Series Sanadin Kenan by Sumayyah Abdulkadir Takori

Don haka shi ya shige wa Mas’ud gaba ya auri Hauwa, ya sayar da gonarsa ya saya musu gida a nan inda suke zaune har yau. A lokacin duniya na kwance sayen gida ba tashin hankali ba ne. gidansu yana nan a unguwar Gwallaga, wanda suke raye har yau a ciki. Sana’o’i iri-iri Hauwa ta yi don ta taimaki kanta da mijinta. Sun dade Allah bai ba su haihuwa ba, sai da suka shekara goma da aure, sannan Allah ya ba su Amina.

Lokacin da Masa’udu ya yi karfi a kan sana’arsa sai ya dauko kaninsa Sule daga Shira ya nuna masa sana’ar Gwanjo, ya sai masa ‘dealer’, ya fasa yana sayarwa da dai-daya, cikin sa’a sana’ar ta karbe shi, har dai da ya yi wani ubangida da ke ba su (dealer) su fasa su sayar su kawo mishi uwar kudi su rike riba. Ya ba shi daki a nan zauren gidansa suke zaune tare, kasancewar iyayensu su biyu rak suka haifa, Kawu Bilya da Kawu Tasi’u duk uba suka hada, shi ya sa sau da yawa idan Hauwa na nuna damuwarta a kan rashin haihuwa ya kan ce, ni kam ba na damuwa, watakila rashin haihuwa a cikin jinina yake, don duk zuriyar su mahaifiyata daga mai Da daya sai mai biyu.

Da Sule ya yi karfi a sana’ar gwanjo ya yi gidan kansa, ya auri ‘yar ubangidansa Atika, sannan ne ya bar gidan Yayansa Mas’udu Baban Amina, domin zuwa lokacin ya fi Yayan nasa samun nasibi don Alhajinsu na ji da shi, har dai da ya auri Atika, shi ma ya sakar masa harkar sosai, har Turai yake zuwa ya shigo musu da kaya.

Amina, ta taso yarinya mai hazaka da son karatu, ga naci a kan abin da aka koya mata, har sai ta ga ya zauna a cikin kanta. Ga son iyaye da son kyautata musu. Tun tana shekara shida ba ta barin Goggonta da ayyukan gida, ko dai a bar mata tayi, ko ta sa hannu su yi tare. Albarka kullum shanta ta ke daga bakin uwa da ubanta tun tana kankanuwa, shi ya sa ta taso yarinya mai matukar nutsuwa da wadatar hankali. Amina ba ta da aboki sai littattafanta da alqur’ani. A zuwa makaranta Amina ba ta san latti ba, daga islamiyya har boko, kullum ita ke daukar tsintsiya ta share ajinsu na islamiyya dana boko saboda tana riga kowa zuwa.

Amina na da shekaru goma sha biyu mahaifinta Mas’udu ya gamu da lalurar shanyewar barin jiki, sun tashi lafiya sun wuni lafiya, da yamma ya dawo daga kasuwa suka taba hira a tsakar gida da iyalinsa. Ana gab da kiran sallar magriba ya mike.

“Yar albarka zuba min ruwa a buta ki gani in yi maza ko na samu jam’i”.

Amina ta ce, “Baba, ai tun dazu na zuba maka.”

Ya kai hannu ya daga butar, “Haka kuwa, Uwata Allah ya kara albarka”.

Murmushi Amina ta yi.

Yana shiga ita da Goggo suka mike don gabatar da tasu alwalar, sai ji suka yi timmm! Ya yanke jiki ya fadi cikin bandakin. Da gudu suka danna kai a bandakin daga uwar har ‘yar, ba tare da tunanin halin da za su riske shi a ciki ba.

Hauwa na kokarin taimaka masa ya mike, ta kasa don idanunsa sun kakkafe, bakinsa ya gicciye. Amina sai kuka, Goggo ta ce.

“Maza kirawo Ilya”

Ta kwasa da gudu domin kiran Ilya a dakin soro.

Ilya ne ya samo taxi suka taitayi Malam Mas’udu, suka sanya shi suka nufi Specialist Hospital Bacas.

Duk wasu shige da ficen shi ya yi har likitoci suka karbe shi. Abin da suka gaya wa iyalinsa bayan sun dudduba shi, ya yi matukar daga musu hankali. Cewa Mas’udu ya gamu da lalurar shanyewar barin jiki, (sudden stroke) don haka sun ba su gado, za a ci gaba da ba shi kulawa da taimakon gaggawa.

Aka danka wa Ilya (bill) na allurai da magunguna da ake bukata, ya je gidan Kawu Sule ya kai masa, ba da son ransa ba ya kawo kudin ya bayar amma bai je asibitin ba yace da Ilya ya gaya musu tafiya ta kama shi Allah ya kara sauki. Ilya ya kawo ya biya komai harda na aljihunsa ya kara aka ci gaba da ba shi kulawa.

Satinsu uku a asibitin ya ji sauki, aka ba su sallama. Yana iya motsa hannunsa da kafarsa, amma ba ya iya yin komai da su. A gida jinyarsa ta koma hannun Goggo, domin Sule ko dubiya bai zo ba bai kuma kara tallafa musu da komai ba tun bayan wancan taimakon da yayi na sayen abinda ake bukata a asibiti lokacin da abin ya faru.

Sai ya zamana Amina tun tana shekaru goma sha biyu ita ke dafa abin da za su ci a gidan, ta tsaftace ko’ina ta kula da sana’ar Goggo ta kalanzir da sayar da itace da ta ke yi a lokacin. Har ya zamanto tana makara a zuwa makaranta, sannan ba ta da nutsuwa kwata-kwata, tana tunanin halin da za ta koma ta riski Babanta a ciki, malamanta kansu sun fahimci hazika Amina Mas’ud ta canza. Da ko an tashi makaranta Amina ba ta gaggawar tafiya gida sai ta kammala rubuce-rubucenta, in aikin gida ne (homework) sai ta kammala shi a lokacin sannan ta tafi gida. Amma yanzu ana kada kararrawa Amina ce farkon fita daga aji cikin sassarfa, wani lokacin ma da gudu ta ke fita.

Ranar wata lahadi a islamiyyarsu inda suke yin Tahfiz daga karfe takwas na safe zuwa azahar wani malaminsu Ustaz Abdulsalam wanda Allah ya daurawa kaunar Amina (ba kauna ta soyayya ba), bayan ta bada haddarta ya daga kai ya dube ta tana harhada takardunta don komawa gida ba tare da an yi addu’ar tashi ba.

Ya ce, “Amina Mas’ud, zauna ki jira ni in gama da ‘yan uwanki, akwai maganar da za mu yi.”

Ba da son ranta ba Amina ta koma bencinta ta zauna tana ta sake-sake cikin ranta, “Ban daura abincin rana ba, na san yanzu daga Goggo har Baba sun dawo daga asibiti ba su samu na dafa komai ba…” Sai hawaye sharr-sharr.

Ustaz na lura da Amina, kawai sai ya ji zuciyarsa ta karye, ya fahimci tsayar da ita din da ya yi ne ya sa ta kuka. Shi kuma so yake ya ji me ta ke yi wa sauri haka da har ya shafi hazakarta a kan karatu? Tana daga cikin daliban da ya sanya sunansu za su halarci gasar karatun alqur’ani mai tsarki ta duniya (International competition of Holy Qur’an) wadda za a yi a kasar Misra wannan shekarar.

Bai nuna ya ga tana kuka ba, har ya gama da dalibansa uku da suka rage masa. Ya isa har gaban bencinta ya ce,

“Aminatu Mas’ud!”

Ta dago jajayen idanunta ta dube shi, a zuciyarsa ya ce, “Subhanallahi Ahsanul Khaliqeen”. A fili kuma ya ce, “Me ke damunki ne a ‘yan watannin nan?”

Ta share hawaye da bayan hannunta, “Babana ne ba shi da lafiya”

Cikin tausayawa Ustaz ya ce, “Allah sarki, me ke damunsa?”

“An ce wai ya samu (stroke). Amma yana samun sauki”

“Allah ya kara wa Baba lafiya, ki dinga karanta fatiha kafa bakwai a ruwa, ki karanta suratu Yaseen ita ma kafa bakwai, ki ba shi ya sha, a kuma shafe masa jikinsa, insha Allahu zai kara samun sauki”

Amina ta ce, “Zan yi insha Allahu”

Ya dube ta na ‘yan sakanni, sannan ya ce.

“Ni da har na ba da sunanki matsayin wadda za ta wakilci jihar Bauchi a ‘International competition a kasar Masar, ban san halin da ki ke ciki ba ke nan”.

Amina cikin girgiza kai, “Ba zan iya zuwa ba Ustaz, don Allah ka cire sunana, ban sani ba ko nan gaba, idan na ga Babana na takawa da kafafunsa”

Ustaz ya jinjina kai, ko nawa ne ‘ya’yan da suka damu da iyayensu haka irin AMINA? Yana rokon Allah ya ba shi ‘ya’ya mata masu albarka irin Aminatu, domin an ce akasarin ‘ya’ya mata masu jin kan iyaye ne.

“Zo ki tafi Aminatu, kada ki manta da addu’ar da na gaya miki, Allah ya kara masa lafiya, ya albarkaci rayuwarki”

Ta kuwa suri jakarta ta fito, da ta tabbatar ta yi wa Ustaz nisa, sai ta kwasa da gudu. Ustaz ya girgiza kai domin yana kallonta.

To haka a boko ma, kullum cikin makara ta ke, a yi ta yi mata bulala da horon da ake yi wa ‘yan makara, amma ba ta damuwa. Don ba ta fita sai ta tabbatar ta gama komai na ayyukan gidan, tun asuba in ta tashi ba ta komawa za ta share gidansu tsaf! Da ganyayyakin bishiyar umbrella ke batawa; ta share dakunan Goggo da na Baba, ta yi wanke-wanke, ta dora sanwa, ta dama musu koko, ko kunu, ta yi musu dumame na abin da aka ci daren jiya. Sannan ta yi wanka ta yi shirin makaranta a iya shekarunta goma sha biyu.

Haka Goggo za ta yi ta saka mata albarka don ko ta ce ta bar mata in ta gama hidimar babanta za ta yi, Amina ba bari za ta yi ba. A zuciyarta cewa ta ke, ‘Don wa nake karatun? Ai don in tallafi rayuwarku ne watarana, to kuma Baba ba shi da lafiya, in na rasa shi ko ke Goggo me ye amfanin karatun nawa?’

A shekarar Amina ta shiga karamar sakandire, da kyar da sudin goshi, domin duk abin da suke samu a sana’ar Goggo a maganin Babansu da abin da za su sanya a bakin salati yake karewa, an tattaro Tantabarun babanta na kasuwa an jibge musu a gida, ita ke kula da su.

Wani zubin sai ta zauna tana mamakin Kawu Sule, tunda ya yi kudi ko gaida Yayan nasa da jiki ya daina, matarsa Atika ita ma halinsu daya, daga su sai ‘ya’yansu uku suke rayuwarsu, ya manta da nakasasshen dan uwansa, wanda shi da ya samu nasa rufkin asirin sai ya dauko shi ya kawo maraya, ya yi masa silar tsayawa da kafafunsa. Ko takardar magani aka ba su a asibiti in magungunan masu tsada ne ta kai masa, ya soma lissafo mata matsalolin da suke ciki ke nan shi da nasa iyalin, dole suka hakura suka daina kai masa.

Tana aji biyu na sakandire, mai yanke buri da soyayya ta yanke tsakaninta da mahaifinta. An ce idan ajali ya yi kira babu makawa sai an tafi, wannan haka ne, amma mutuwar Malam Mas’ud rashin kulawa da rashin magani, ko gashin kashi da ake masa gagara ya yi, ta abin da za su ci kawai suke. Goggo sai dai ta tayar da shi ta ba shi abinci, ta kwantar. In ya yi lalura ta tsaftace shi, hannun ma da kafa da suka soma warkewa bayan barinsu gadon asibiti daina motsin suka yi saboda rashin magani da (contineous treatment). Allah ya jiqan Malam Mas’ud.

Misalta halin da Amina ta shiga na rashin mahaifinta ba zai fadu ba, kwananta bakwai tana zazzabi mai tsanani, Goggo ta dage da yi mata addu’a ba dare ba rana, kada rashin ya yi mata yawa, ba ta da kowa a Nigeria sai su, domin tuni iyayenta suka koma kasarsu Sirrleone. Da taimakon Allah Amina ta samu, amma fa da kullaci a ranta na kanin Babanta Alhaji Sulaiman, da kawun mahaifinta Malam Bilya, wanda ko gaisuwa bai zo musu ba, a cewarsa ba ruwansa da bakin haure, Mas’udu lokaci ya yi ko daga can inda yake ya yi masa addu’a Allah zai karba.

Kafin rasuwar mahaifinta ne Allah ya hada Goggo da maraya Ilya, sun yi zaman mutunci da iyayensa kafin Allah ya dau ran mahaifinsa, har yanzu kuma mahaifiyarsa Zulai suna mutunci da Goggon, shi ya ba ta shawarar ta kara wata sana’ar bayan itace da kananzir tunda yanzu lokacin zafi ne kuma tana da freezer katuwa, shi zai rinka kai mata makarantu. Ta shiga wani shiri na koyon sana’o’i da gwamnatin Bauchi ta shirya karkarshin ma’aikatar ci gaban mata, tsawon wata guda aka ba su jari mai tsoka, da shi ta sayi freezer din, ta kuma ja jarin zobo da kunun ayarta masu shegen dadi da tsafta. Duk unguwar ma a wajenta ake saye bayan makarantu da ake kai wa da sauran wuraren hadaka na mutane, Ilya ya samu taimakon wasu yaran guda biyu inda suke raba kafa. A gefe kuma sana’ar itace da kananzir ita ma tana nan. Dakin soro wanda Sule ya zauna a nan Ilyan Goggo (kamar yadda Amina ke kiransa), nan Goggo ta bar masa yake kwana domin ta yarda da hankali da amanarsa.

Wani lokacin Amina in suna tadi da Goggonta ta kan ce, “Goggo da fa a ce ni likita ce, kuma na karanci lalurar Babana, da fa yanzu bai mutu a gida cikin ciwo ba, zan dinga samun albashi in sai masa magani, in kuma dinga duba shi da kaina”.

Goggo kan ce, “Kul Amina! Kada ki yi sabo, kullu nafsin za’ikatul maut, in sa’i ya yi dole sai an tafi, likita bai isa komai ba”

Amina kan ce, “Haka ne Goggo, amma insha Allah zan yi karatu mai zurfi Goggo, zan karanci lalurar da Babana ya yi domin jinyarta sai mai hakuri, imani, juriya da sadaukarwa. Idan na tuna yadda kullum Baba ke sa miki albarka, da roka miki aljannah, sai bakin cikina ya ragu domin hakika kin rabauta. Goggo za ki taimaka min in yi karatun? Ba za ki ce aure za ki yi min ba?”

Goggo ta yi murmushi, “Karatu ai ba ya hana aure Amina, sai dai ki ce sai in mijin bai zo ba, in kuma ya zo to za mu yi sharadi ko da gaban alkali ne, zai barki ki ci gaba”.

Amina kan zumburo baki, “Ba sai na kula su ba balle su zo din?”

A zuciyarta ta ke fadin hakan, don a dabi’arta ba ta ja-in-ja da Goggon nata. In ta fadi abu wanda bai yi mata ba shiru ta ke yi, hatta Goggon ta gane hakan.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 4.3 / 5. Rating: 6

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Sanadin Kenan 3Sanadin Kenan 5 >>

13 thoughts on “Sanadin Kenan 4”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×