Skip to content
Part 41 of 50 in the Series Sanadin Kenan by Sumayyah Abdulkadir Takori

Yana sane ya kashe wayoyinsa tsawon kwana uku don ya san dole za a neme shi kan batun Laila. Ba ya zuwa ko’ina a kwanaki ukun nan, wakilai yake turawa. Daga (office) sai gida manne da Aminarsa. Hajiya da ta gaji da nemansa sai ta kira layin Amina, ta ce ta hada ta da shi.

Ba yadda zai yi don yana zaune a wajen. Ya karbi wayar ya soma gaida Hajiya cikin ladabi, ba ta bari sun gama gaisawar ba ta jefo masa tambayar da take dauke da  ita.

“Me ya hada ka da Laila? Ta zo wajena ban barta ta karasa wajen iyayenta ba. Nayi-nayi ta gaya min me ya faru ta ki. Sai kuka ta ke tana fadin in nema mata afuwa a wajenku”.

Da ba Hajiya ba ce kashe wayarsa zai yi, amma wannan ita ce mace mai daraja ta farko a gare shi. Ya gaya mata duk abin da ya faru, a yau kuma ya bude baki ya sanar da ita irin zaman da yake yi da ita tun aurensu. Ya ce, saboda rashin kaunarta da tausayinta ga Ameena ya dauko Dr. Amina ya kawo gidan. Don haka ita ce SANADIN aurensa da Amina ko ta ina aka je aka dawo.

Da ta bi yadda yake so su rayu shi da ita da tilon ‘yar sa Amina shi da ba mai ra’ayin kara aure ba ne. To ta kwashi wasu dabi’u da halaye na kawayen banza ta daura wa kanta. Shi kam, ya gama aurenta zai aiko mata da takardarta don ko ta ce za ta canza ba zai iya adalci tsakaninta da Amina ba, kuma Annabi (S.A.W) ya ce a zauna da daya, in ba za a iya adalci ba. A karshe ya ce,

“Hajiya ki barta ta tafi gidansu, yanzu ne ta san ke mutum ce da za ta amfane ta? Ta taba zuwa har inda ki ke haka siddan ta gaishe ki tunda na aure ta? A matsayin ki na wadda ta haifa mata miji?   Ta taba jin kan abin da na haifa a lokacin da take bukatar Uwa mai tausaya mata? Ta taba nuna min kauna ta hakika ban da ta in na ba ta kudi? Laila ba matar zama ba ce Hajiya, don Allah kada ki takura ni in maido ta ta fita daga raina gaba daya. Ki barta ta je gida don Allah na sake ta saki daya…”

“Hasbunallahu wa ni’imal wakeel… Ma’arouf ni za ka bai wa aiken saki? Ka yi min adalci kenan? In don ta ni ne duk abin da ta yi min na yafe mata, na yi mata uzuri tunda ta yi nadama kuma ta kara jaddada min ba za ta sake duk abin da ba ka so ba, za kuma ta zauna da Amina lafiya. To na yafe mata duniya da lahira, ko tsoron surutu ba ka yi a ce don ka yi aure ka saki uwargidanka? Ce ne ka maida ita maza-maza tun wani bai ji ba bayan ni”.

“Sai ta ji na sake ta Hajiya wallahi sai ta ji, ba ni ita a wayar”.

Tunda ya rantse jikin Hajiya ya kara yin la’asar, ita kanta ta san halin Laila ba mutuniyar kirki bace, ita ma dattaku ne kawai a matsayinta na uwa gyara ne nata ba bin bayan daya ba. Tunda kuma ya rantse ba za ta so shi da kaffara ba. Lailan ta kuma sabule mata da a yau ta ji bata kaunar jikarta tilo a duniya Amina diyar A’isha. A sanyaye ta mika wa Laila wayar wadda ke zaune gabanta dirshan tana tikar kuka, tana kuma jin duk abin da suke tattaunawa tana mai yarda da kuskurenta.

“Ma’arouf don Allah ka yi hakuri na tuba, na bi Allah na bi ku…”

“Na sake ki saki daya. Kije gida kawai. Allah ya hada kowannenmu da Alherinsa”.

“Wayyo Allah Ma’arouf ka yimin rai, ina son ka, ina kake so insa raina…..???”

Sai a lokacin ta lura ya dade da kashe wayar hannunsa.”

Hajiya ta rasa kuzari, ta kasa yin komai akai, a karshe da Laila ta yi kuka ta gaji ta umarce ta data yi hakuri taje gidan nasu kawai kafin tayi tunanin yadda zata shawo kansa.

*****

An sallami Amina ta koma gida amma ba’a kwance bandejin kanta ba, Amina zata iya rantsuwa cewa ciwon nan a jikin ta yake amma Ma’arouf ne yake jin zafin sa.

Har dakinta nurse ke zuwa tayi mata dressing din ciwon kullum.

Sai kasancewarsu su kadai cikin makeken gidan su ya zama wata hanya ta kara dankon soyayya da fahintar juna, aminci da kauna mai karfi a tsakaninsu. Amina ya zamanto bata da damuwa, koyaushe idan Ma’arouf ya shiga office zama take ta kira Goggonta da yan uwanta na gida dana kauye su sha hira ko ta tura mota a dauko su su wuni tare, duk wanda ke da nasaba da Amina komai kankantar ta to kuwa yana shan inuwar data ke ciki, wannan a fili yake, hannunta a bude yake kullum cikin bayarwa take da yiwa al’ummar data shafe ta hanyar cin abinci. Hatta Yayanta Hafiz kuma tsohon masoyinsa Amina tasa Ma’arouf ya dauke shi daga kamfanin mtn da yake aiki ya maida shi bankin GT. In ma tanada damuwa to na rashin practising aikinta ne. Ta taba yiwa Ma’arouf zancen tanaso ta koma aiki don bata iya zama waje daya ba ta komai ba.

Ya ce, “Ina matar Jikas da zuwa aiki? Ko zan amince sai ranar da ‘tenure’ dina ta kare muka bar wannan gidan muka koma gidana na Fati Mu’azu”.

Dole Amina ta hakura, ta maida hankali ga bautar aurenta, domin neman dacewa wajen Ubangiji, don a duniya kam ta gama dacewa. Alfarmar auren miji na gari irin Ma’arouf Habibu Ji-kas ba karamin dace ba ne. Ta kowanne fanni da diya mace ke buri.

Duk da an ce kowanne dan Adam tara yake bai cika goma ba, a wurinta ita nata mijin ya cika har ya wuce ya isa goma sha tara!!!

*****

Laila ta isa gidansu yamma lis almajiri dauke da katuwar akwatunta, mahaifinta ta fara arba dashi a kofar gida ya shimfida tabarma yana kishingide yana sauraron radio, tun daga nesa ya hango ta tana tafe amma ya sawa ransa ba ita bace mai kama da ita ce, ina Laila ina tafiyar kasa da dirkeken akwati haka kamar mai barin gari?

Bayan watanni biyu Hajiya ta dawo da Laila. Ta zama saliha irin yadda mijin ke so, kai ka ce Amina ce uwargida yadda Laila ta kwantar da kai ta ke binta suke zaman lafiya. Sai dai ita kanta ta san da gaske Aminar ta yi mata fintinkau a zuciyar Ma’arouf ko ta canza hali ko kada ta canza ba zai amfana wa Aminar komai ba, gara ma ta karbi canjin rayuwar da hannu bibbiyu.

Shekaru biyu da auren Ma’arouf da Amina ta haifo santalelen danta mai kama da ubansa a komai. Hajiya ta ce da shi a lokacin da yake rungume da yaron kamar zai tsaga kirjinsa ya sanya shi.

“Kai dai jininka karfi gare shi, duk ‘ya’yanka kai suke debowa”.

Amina ta nemi mijin nata alfarma a sanya mata sunan Babanta, bai ki yi mata alfarmar ba, don ba ya jin ko ransa Amina ke so zai kasa mallaka mata da yana da iko. Ranar suna yaro ya ci suna Mas’ud Ji-kas.’

Duk dangin Amina na uwa da uba babu wanda ba ya jin sanyi karkashin inuwar Amina. Wannan kuwa duk sanadin ilimi ne (iyaye mata mu inganta ilmin ‘ya’yanmu mata, musamman a kan ilmin kimiyya da kiwon lafiya). Kusan duk sati Amina sai ta je wajen Goggonta ko a dauko ta.

Shekaru biyu cif da haihuwar Mas’ud Ji-kas Amina ta sake haihuwa. Wannan karon diya mace, wannnan karon ma ta sake neman alfarmar Ma’arouf a sanya wa yarinyar suna Aisha. Ga mamakinta sai ya ce, “A’ah sunanta Saudatu (Hajiyan Ji-kas) Ki kara himma zuwa shekara ta gaba ki haifo wata, watakila in sanya Aisha din”.

Laila dai haihuwa shiru tun tana damuwa har ta hakura. Abin yana bai wa Amina tausayi in ta ga yanda ta ke nan-nan da yaranta Mas’ud da Saudatu. Don haka da ta sake haihuwa, wannan karon da namiji ne, sai ta tattara kayan Saudatu ta sa Saudatun a gaba sai dakin Laila.

“Na ba ki rikon Saudatu har abada Anty Laila, ko da nan gaba Allah ya ba ki naki ba zan kwace ba. Allah ya dube ki da idanun rahmarSa ke ma”.

Laila don murna sai da ta yi hawaye, ta dauki Saudatu ta rungume, da ma yarinyar ta saba da ita fiye da kowa a gidan. Amina ta sha mamaki da ranar suna aka ce d ita ILYAS Ma’arouf ya sanya wa jaririn (daga baya Amina ta sha ba shi labarin irin tarin kaunar da Ilya ke masa in suna hira).

Lokacin da (tenure) din Ma’arouf ta cika, ya sake tsayawa kamar yadda al’ummar jihar Bauchi suka bukata. Ya sake hawa kujerar Gwamna a karo na biyu. Shekarunsu takwas ke nan a Government House, sai a wannan shekarar suka sauka. Jama’arsa sun so ya kara tsayawa Sanata, ya ki. A cewarsa, siyasa tana hana shi kulawa da iyalinsa yadda ya kamata. Don haka ya gama ta da izinin Allah. Wanda aka zalunta ko aka bata wa karkashin mulkinsa yana rokonsa ya yafe masa!

Wannan kalamin ya yi su ne a wata hira da BBC ta yi da shi. Ya sanya jama’ar Bauchi da yawa kuka.

Ilya ya yi murna sosai da samun takwara, haka ya ciko akwatuna da kayan Baby. Sun tattara sun koma gidansu na Fati Mu’azu Links. Amina ta ci gaba da aikinta, shi kuma ya ci gaba da (construction contract) dinsa. Laila ta koma makaranta.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Sanadin Kenan 40Sanadin Kenan 42 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×