A hankali drivern ke tuƙa su Ummiy, sakamakon Ummiy bata son ana gudu a kan hanya, baby da ke zaune a gidan baya a gefen Ummiy, dubanta ta ta kai kan Ummiy tana murmushi ta ce, "Ummiy gobe ai ba da wuri za mu tafi ba tun da flight za mu bi ko?"
Ummiy ta ce, "Idan kika tsaya baccinkin nan za ki tashi a ce miki na jima da isa Yobe, dan haka idan za ki gama komai da wuri ki gama."
Baby shiru kawai tayi tare da kwanciya a jikin Ummiy har suka isa, driver na parking. . .