TAƁA KA LASHE
Masu azanci suna yawan ambaton jimlar alhaki kwuikwuyo ne mai shi yake bi, sai dai a doron ƙasa akwai wasu nau'in jama'ar da ba su gama amincewa da wannan azancin ba, sun yarda cewa alhaki kwuikwuyo ne amma ba su yarda cewa wata rana yakan dawowa wanda ya aika shi har ya tumurmusa shi tare da yi masa mummunan rauni ba. A hangensu koda alhaki zai zama kwuikwuyo idan ka riga ka aika shi ya tafi kenan kamar fitar numfashi da ba zai taɓa dawowa ba. Fauziya da Aisha suna ɗaya. . .