Skip to content
Part 1 of 10 in the Series Sharri Kare Ne by Rukayya Ibrahim Lawal

TAƁA KA LASHE

Masu azanci suna yawan ambaton jimlar alhaki kwuikwuyo ne mai shi yake bi, sai dai a doron ƙasa akwai wasu nau’in jama’ar da ba su gama amincewa da wannan azancin ba, sun yarda cewa alhaki kwuikwuyo ne amma ba su yarda cewa wata rana yakan dawowa wanda ya aika shi har ya tumurmusa shi tare da yi masa mummunan rauni ba. A hangensu koda alhaki zai zama kwuikwuyo idan ka riga ka aika shi ya tafi kenan kamar fitar numfashi da ba zai taɓa dawowa ba. Fauziya da Aisha suna ɗaya daga cikin irin waɗannan nau’in halittun da suka canza ma’anar wancan azancin, shi ya saka suke sheƙe ayarsu ta hanyar yin gurɓataccen rubutu kuma su aika shi wa ɗimbin al’umma cikin farin ciki da ribar da suke samu, ba tare da tunanin wata rana ƙaiƙayi zai koma kan masheƙiya ba, haka ba su hakaito yiwuwar rikiɗewar farincikinsu zuwa akasin hakan ba a silar alƙami.

Wannan shi ne kuskure mafi girma da suka tafka a rayuwarsu, kuskuren da ya jefa ruhinsu a cikin matsananciyar damuwar da ta kusanta su da ƙabarinsu.

*****

Bari na yi amfani da zaurance wurin ƙirga lambobin babi-babi.

YAƊA

Duk Wanda Ya Sayi Rariya….

Hankali a tashe na sauko daga abin hawan ina ƙarawa motar duga-dugaina sauri ba tare da yin la’akari da cewa hanzarin da nake yi zai yi silar jefa wani daga cikin ɗaukacin jama’ar da ke kai komo a harabar asibitin a damuwa ba, kodayake idan ana ta kai ba a ta hula, wutar tashin hankalin da ke cin zuciyata ta cike kowanne gurbi na ma’adanar sirrina ta yadda babu wani sauran gurbi da ya yi saura da tunani ko tausayin wani zai samu matsugunni a wurin.

Jefa ƙafa kawai nake ban yi aune ba na ji na ci karo da mutum, ɗagowar da zan yi haka a razane na ga wata matashiya da ba za ta wuce sa’a ta ba ta tafi taga-taga kamar za ta kifa da dukkan alama ita ce wacce na bige ba tare da lura ba, sai dai yanayin da nake ciki bai ba ni damar tsayawa taimaka mata ba duk da na san cewa laifin nawa ne.

“Yi haƙuri don Allah.” Abin da na faɗa kenan a gaggauce ina shura takalmina na ƙara gaba duk da cewa na ga lokacin da matashiyar ta faɗi ƙasa rikicaa! Ga dukkan alamu kuma ta ji rauni duba da yadda take kici-kicin tashi ta kasa, sai dai ‘yan magana sun ce ana bikin duniya akan yi na ƙiyama.

Ina jiyo hayaniyar wasu daga cikin jama’ar da suka yunƙuro domin ceton matashiyar da kalamai masu zafi da wasun su suke yi a kaina sai dai ni ba ta ta su nake ba don haka na shige cikin asibitin a gaggauce ina waige-waigen neman abokiyar cin mushena da ta gayyato ni zuwa inda nake fargabar ci gaba da kasancewa a raye bayan halartarsa.

Sai dai me? Har na shafe tsayin mintuna goma ba ita ba dalilinta, ‘To me ya tsayar da ita? Kada dai a ce ta labartawa ɗaya daga cikin ahalinta labarina domin sarai na san halinta ganga ce ba a sirri da ita.’ 

Nan fa farashin tashin hankalina ya daɗa hauhawa domin kuwa tabbas na san cewa idan wani ya samu labarin halin da nake ciki na kaɗe har ganyena. Ina nan ina karatun wasiƙar jaki kamar an ce ɗaga kanki na hango ta tafe cikin hanzari, tun kafin ta ƙaraso gaf da ni ta ce

“Afwan Noorhan mu je ciki.”

Ban tamkata ba ta shige gaba ina take sawayenta yayin da ƙirjina yake lugude.

‘Me ke shirin faruwa da ni ne? Anyah abin da muke shirin aikata wa yanzu ba zai bar mana baya da ƙura ba?’

Na yi zancen a zuciyata ban san cewa zancen zuci ya fito sarari ba har sai da na tsinkayo muryar Nuriyyah tana faɗar 

“Abin da kika shiryawa faruwarsa ne zai faru da ke. Sa’annan kuma da ma kina tsoron ƙurar da za ta wanzu a baya shi ne kika yi shara ba tare da kin yayyafa ruwa ba?”

Ba tare da na tsaya daga ci gaba da bin ta da nake yi ba na ce

“Nuriyyah me kike nufi, ban fahimci inda kalamanki suka dosa ba?”

“Kin fini sanin inda suka saka gaba kuwa domin dai duk wanda ya siyi rariya ai ya san za ta zubda ruwa, wannan sokancin da kika yi idan kika yi wasa shi ne zai zama nadamarki ta ƙarshe a rayuwa.”

Ban sake cewa da ita kanzil ba har muka je bakin ƙofar da za ta sada mu da ofishin Dr Saif, na ja na yi turus kamar wacce aka dasa a wurin, har Nuriyyah ta saka kai cikin ƙofar ta lura da ban biyo bayanta ba sai kawai ta juyo don jin abin da ya dakatar da ni.

“A’ah! Noorhan me ya dakatar da ke daga kusantar burinki?”

“Tsoro nake ji…” Na faɗa da raunanniyar murya.

“Tsoron me?” Nuriyyah da take kallona baki a hangame kamar garkar wawa ta tambaya.

Na sunkuyar da kaina ƙasa

 “Tsoron abin da ka je ya dawo bayan na aikata gingimemen laifin da yafi wanda na aikata a baya zunubi. Koda dai na ji masu azancin zance na cewa amfanin zunubi romo amma ni a yanzu na ji ba na mararin sake kurɓar romon da ke ciki. A bayyane yake cewa kisan kai yafi zina zama tafkeken laifi a addinance.”

Bayan na gama zazzago dogon sharhina kawai sai Nuriyyah ta ja wani malalacin tsaki Mtsw! A ɗan zafafe ta ce 

“Shi ke nan ai sai mu koma gida duk ranar da abin ɓoye ya bayyana kada ki sake ki neme ni, kodayake ma na san kin tanadi amsar da zaki ba wa iyayenki a lokacin da tusa ta kurewa budari.” 

Tana kai nan a zancenta ta juyo za ta bar cikin farfajiyar na riƙe hannunta gam cike da damuwa da fargaba na ce 

“Yi haƙuri Nuriyyah mu shiga ciki kawai.”

Ta sauke wani zazzafan huci sannan ta juya muka shiga, kallon ɗaya zaka yi mini ka san a matuƙar razane nake.

Sa’a ta ɗaya koda ta tambayi dr Saif sai aka ce a ranar wani uzuri ya riƙe shi ba zai samu zuwa ba. Wani irin sanyin ya ratsa zuciyata har ban san lokacin da na sauke ajiyar zuciya ina faɗar Alhamdulillah ba, wannan abin ne ya matukar ɓatawa Nuriyyah rai ta fito a fusace tana faɗar “Komai kika yi mini dai-dai ne, laifina ne da na fifita damuwarki a kan tawa.”

Tana gama faɗa ta yi fuu ta wuce abin ta, alamar ta gama ƙuluwa. Na yi ta ƙwala mata kira amma ba alamar za ta saurare ni. Sai da ta ɓacewa ganina sannan na haƙura da wahalar da maƙwogwarona na fara takawa a sanyaye ina nufar hanyar fita daga asibitin.

Na ɗan yi nisa a tafiyata kamar saukar aradu na jiyo wata murya a bayana tana faɗar “Tun wuri ki yi fatali da shawar ƙawa Noorhan, kafin gagarumar nadama ta kawo miki ziyarar bazata.”

Jin an ambaci sunana ya saka na yi saurin waigawa sai dai kowa da yake wajen harkar gabansa yake, ban ga wani mutum ɗaya da alamu suka nuna shi ya yi zancen ba. Saurin bugun zuciyata ne ya ƙaru na ƙara saurin tafiyata, kafin na fita babbar ƙofar asibitin na ji wannan muryar ta sake ce da ni

“Kada ki sake ki koma faɗawa tafkin saɓon Allah Noorhan, kada ki yi kisan kai. Kar ki sake ki biyo hanyar da nake kai domin ƙarangiya ce a shimfiɗe kan hanyar.”

Nan ma a hanzarce na waigo amma ba alamar mai maganar don haka a ɗari na ƙarasa ficewa daga asibitin ina sauke ajiyar nufashi tamkar wacce ta shiga gasar tsere.

‘To waye wannan da yake yi mini gargaɗi? A’ina ya san labarina? Macece ko Namiji? Me ya haɗa hanyata da tashi?’ Waɗannan tambayoyin ne suka kawowa zuciyata ziyarar bazata, duk da cewa na ji muryar amma yanayin firgicin da nake ciki bai ba ni damar tantancewa ba.

Ina ƙarasa wa gida na faɗa banɗaki domin kuwa tun a hanya ‘ya’yan hanjina ke hautsinawa. Ina tsaka da gabatar da uzurina na jiyo sallamar wani ƙaramin yaro a cikin gidan.

“Assalamu alaikum” sai ga muryar umma tana amsa sallamar tare da faɗar “Lafiya dai yaro?”

“Lafiya Ƙalau wani ne ya ba ni wannan ya ce a ba wa Noorhan.” 

“To yaro kawo na ajiye mata an gode jeka abinka.”

Daga nan kuma na ji shiru alamar yaron ya fice, Umma kuma ta je sabgogin gabanta.

“Ke ƙaramar ‘yar iska ki ji ni da kyau kada ki sake kira na ko nema na, idan kuma kika sake ko da kuskure kika neme ni wallahi zaki sha mamakina, kin san dai abin da zan iya.”

Waɗannan kalaman na Amir ne suka fara dawowa a fasarrafar jina tamkar a lokacin yake furta su. Nan fa hankalina ya yi tashin gwauron zabi, saboda rashin sanin sahihin saƙon da aka aiko mini da mai aikowar. ‘Kada dai ya zamana saƙon Amir ne.’

Ban san lokacin da na furta kalmar na shiga uku ba. Har zan miƙe cikina ya sake ruɗewa na gama firgicewa tamkar kazar da ta ga ana wasa wuƙar yanka ta. Bisa ga tilas na tsaya domin biyan buƙatata a karo na biyu sai dai wannan karon a gaggauce na ƙarasa na fito.

*****

Ɗakin Umman na fara leƙawa a hanzarce amma ba ta ciki sai ƙawarta, tsabar firgicin da nake ciki bai ba ni damar tunowa da tarbiyyar da a ka yi mini da gayar da manya ba. A maimakon hakan sai cewa na yi “Don Allah Mama ina Umma?” Cikin ɓarin baki na yi zancen.

“Ta je ɗakinki ajiye miki saƙo lafiya dai?” Ta mayar mini

“Ƙalau.” Na amsa mata a gaggauce ina barin ƙofar ɗakin, gudun kada ta ɓallo mini ruwan da ba zan iya tarbe su ba. Majigin ƙwaƙwalwata yana hasko mini gingimemen tashin hankalin da zai afku a gidan bayan ta yi ido huɗu da saƙon da nake kyautata zaton na Amir ne.

Koda na ƙarasa ina hango gefen ta tana ƙoƙarin warware takardar hannunta. Tamkar wacce aka ingiza haka na faɗa ɗakin ba shiri na warce takardar daga hannunta.

Ta yi hanzarin juyowa tana kallona da mamaki, na sunkuyar da kaina ƙasa saboda sanin laifin da na aikata ina faɗar “Yi haƙuri Umma, wannan kamar saƙona da aka aiko mini yanzu ko?”

“I shi ne, ya aka yi kika san an kawo yaushe kika shigo gidan?” Ta jero mini tambayoyin a tare.

“Dawowata kenan, da ma uzuri ya koro ni sai na shiga banɗaki, ina daga ciki na jiyo mai kawo saƙon.” Na amsa mata tare da zama kan yagaggiyar ledar ɗakin.

“Da ma zan duba mai kawo saƙon ne kafin ki zo.”

“Shi kenan Umma tafi abinki yanzu zan duba.” 

Ba tare da ta sake tamka mini ba ta juya zuwa ɗakinta inda ta bar baƙuwarta tana jira. Fitarta ke da wuya na miƙe na sako kodaɗɗen labulen ƙofar domin ya yi wa ɗakin sutura, sa’annan na warware takardar da ke hannuna gabana na tsananta faɗuwa.

Tun a sakin layi na farko na cikin wasiƙar jinina ya fara tsinkewa na sake shiga firgici da tashin hankali fiye da farko. Sai nake ji a raina kamar ban karanta jimlolin da kyau ba don haka na sake bitar su a zuciyata kamar haka:

Barka da hutawa kyakkyawa, saƙonki ya riske ni kuma ya burge ni, shi ya sa na ga dacewar maido miki da martani. Kin ce idan ban aure ki ba za ki je har gidanmu ki tona mini asiri ko? Hakan ya burge ni, kina yunƙurin yin amfani da cikin jikin ki don yaƙata ba? To ki sani ina miki kashedi tun wuri ki zubar da makaman yaƙinki domin ba su da ƙarkon da za su daƙusar da nawa.

 Yana da kyau ki san makaman da na tanada domin tarwatsa rundunar yaƙinki. Makamanan nawa su ne kamar haka; hotunan baɗalar da kika aikata tare da ni da bidiyoyi. Na san a ranki za ki yi dariyar wautata kuma za ki ce ka nunawa duniya na sani baƙin fentin ba ni kadtai za ka shafawa ba har da kanka…

Kin san wani abin burgewa? Fasahar zamani ta sarrafa hotuna zuwa nau’in da mutum yake so a bar burgewa ce, ki yi tunani shin a yadda nake da wayewar nan ba zan iya amfani da fasahar don kaifafa makaman yaƙina ba? Ki ƙara tunani zan iya yin amfani da waɗannan makaman nawa masu ƙarfi na ɓata zancen aurenmu, zan ba wa iyayenki da nawa a matsayin hujja kina ga ba za su amince da ni ba?

Sai dalilin da ya saka na rubuto miki wasiƙar, ina so na sanar da ke cikin jikinki mallakinki ne ke ce uwa da ubansa domin idan baki manta ba ke kika yi silar samuwarsa saboda da kanki kika nemi na kusance ki. Har ga Allah na yi niyyar aurenki amma kin ɓata rawarki da tsalle. A ƙarshe dai kin cika burinki kin ɗanɗana abin da jaruman novels ɗin da kike karantawa kan ji, kuma ga kyakkyawan sakamako kin samu ina taya ki murna, ina mai miki albishir da cewa gobe-goben nan zan bar ƙasar nan. Ba zan shawarce ki ki janye yunƙurin yaƙinki ba sai dai ina sanar da ke yiwuwar juyewar reshe da mujiya.

Karantawa nake gumi na keto mini tamkar wacce ta haɗiyi kunama tuni na zube akan ledar ƙasan ɗakin sai sharce gumi nake ina faɗar

“Innalillahi wa inna illaihir’raji’un.”

Sai kuma na ci gaba da karantawa kamar wacce aka yi wa dole.

 Ki sani Allah ya isarki ba za ta yi tasiri a kaina ba, hasalima ni ne zan ja miki ita ta tasirantu a kanki domin kin dulmuyar da ni a cikin kogin saɓon Allah. Ina fatar saƙona ya riske ki cikin yanayin farinciki domin ya ƙara saka ki nishaɗi, ki huta lafiya zan yi kewar gangar jikinki.

                                                  Naki Amir.

Ina zuwa ƙarshen takardar ƙwaƙwalwata ta tsaya cak, tuni lantarkin da ke sarrafata don yin aiki ya ɗauke, zaune nake kawai kamar bishiyar da aka dasa ta ta yi rassa. Na ma rasa me zan yi a lokacin don ceto kaina daga cikin wannan tashin hankalin da yake tunkaro ni.

Sai bayan shuɗewar mintuna biyar sa’annan wutar lantarkin da ke aiki a cikin ƙwaƙwalwar tawa ta dawo, a lokacin ne na samu damar fara yin nazari kan abin da ya kamata na yi.

‘Kira Nuriyyah mana.’ zuciyata ta shawarce ni, ba musu na aminta da shawarar kasancewar duk lokacin da na shiga matsala Nuriyyah ce ke ba ni mafita.

Jakar da ke saƙale a kafaɗa ta na janyo na lalibo wayar tafi da gidanka da nake amfani da ita na shiga neman layinta afa-jajan. Sai dai har ta ƙaraci ɓurarinta ba alamar za ta ɗauka, sai da na jera mata kira sau biyar amma shiru tamkar maye ya ci shirwa.

Dole ƙanwar na ƙi ta sanya na haƙura da nemanta domin dai a yadda na san halinta idan zan kwana ina aikin kiranta zai tashi a banza ne wai gudun harbabbe. Akwai alamar har lokacin tana sukuwa a dokin fushin da ta hau bada jimawa ba, ban san tsawon lokacin da za ta ɗauka kafin ta kunce sirdin dokin ta sauka ba. Ga shi ina neman mafita da gaggawa don haka na jingine wannan tunanin na shige bincike kowane saƙo da lungu na ma’adanar tunanina don samo wata mafitar. Ina tsaka da wannan binciken ne na fara yunƙurin amai da gudu na ƙarasa bakin rariya na fara sheƙa amai a galabaice.

“Subhanallahi! Meke damunki ne Noory?” Muryar Ummana ta daki dodon kunnena.

Ban ce kanzil ba sai da na kammala na wanke fuskata na miƙe da ƙyar na juyo na fuskance su. 

Mama Aisha ta ce da ni “Sannu Noorhan, Allah Ya ƙara afuwa.”

Umma kuwa a maimakon ta yi mini sannu tambayarta ta maimaita.

Cikin sanyi na sunkuyar da kaina ina faɗar “Ba komai Umma da ma yau ina jin jikin ba daɗi, don kawai kada ki hanani fita ne ban nuna ba. Da alama zazzaɓi ne yake samame na.”

“Ayyah sannu! Ki je ɗakina ki ɗauki magani akan madubi ki sha sai ki kwanta.” Ta faɗa tana bi na da wani irin kallo da nake kyautata zaton na zargi ne, don kada na ba ta damar hakaito komai a kan yanayina ya saka da hanzari na wuce zuwa ɗakinta don ɗaukar maganin.

Kafin na fito daga uwar ɗakan na jiyo muryar Aisha ƙawar Mama tana faɗar

“Mutuniyata ashe haka kasuwancin nan namu yake da riba? Ina kwance akan gado fa sai na haɗa dubu biyar a wuni, ranar da kasuwar ke ci ma har fin haka.”

Da har zan fito zuciyata ta kwaɗaita mini son jin amsar da mahaifiyata za ta bayar don haka na jinkirta.

“Naki wasa ne, idan na faɗa miki abin da nake samu dalilin kasuwancin nan sai kin ji kishi ya ɗarsu a ranki. Shi ya sa ba na saurarar duk wani cece-kuce da gurgun wa’azi da wasu ‘yan tsurku ke yi mini. Duk ta bayan kunnena yake wuce wa.” Umma ta mayarwa ƙawarta don kawai na ji sana’ar da suke samun riba haka na sake maƙewa.

Mama A’isha ta ce “Ranar wata yar iska ta biyo ne furabet (private) ta ke ce da ni wai na ji tsoron Allah ni ma mace ce kuma ina da ‘ya’ya mata ko da ba ni da zan haifa, yadda nake jefa su a cikin masifa haka watarana abin da zai faru da ‘ya’yana ba zan so shi ba.”

“Ke ki ji munafuka sai ka ce ba su suke ƙara mana ƙarfin gwuiwar ci gaba da kasuwancin ba. Ai idan ɓera da sata daddawa ma da wari don haka yanzu na fara ru…”

Tana kai wa nan a zancenta ta dasa aya ba don zancen ya ƙare ba sai don ihun da na saka dalilin ganin mage a kusa da ni. A rayuwa inda abin da aka jarabce ni da tsoro to mage ce. 

Wannan dalilin ya sa ban ƙarasa jin gulmar ba suka yo ciki suna faɗar lafiya?

“Mag… Mage.” Na faɗa a tsorace. Mama A’isha ta bushe da dariya “ke dai an yi matsoraciya wallahi mene abin tsoro a cikin mage.”

Umma da ta ga ina kyarma ta kora mager kafin ni ma ta kora ni da faɗar

“Ɗaukar maganin ne ya sa kika maƙale a ciki haka? Maza ki tafi idan kin ɗauka.”

Sum-sum na ja kafafuna na fice daga ɗakin ‘Ba haka aka so ba ƙanin miji ya fi miji kyau.’ na faɗa a raina.

Ummu Inteesar

Sharri Kare Ne 2 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.